• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, June 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 16, 2025
in Babban Labari
0
TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Daga hagu, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ne tare da tsohon Gwamna Alhaji Aminu Bello Masai, a yayin taron

18
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
A dama, Mai Martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar ne, tare da Sakataren Masarautar Katsina, Ibrahim Ida, a yayin taron

__________

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a ranar Lahadi da ta gabata, (14 ga Satumba, 2025) ya jagoranci babban taron shawarwari da ya haɗa manyan mutane na jihar domin tattaunawa kan harkokin tsaro, mulki da cigaba.

Taron ya samu halartar dattawa, sarakuna, shugabannin addini, tsofaffin hafsoshin tsaro, da fitattun ’ya’yan Katsina daga gida da waje – dukkaninsu sun haɗu wajen duba nasarori, nazarin ƙalubale, tare da tsara dabarun tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

A jawabinsa na bufewa, Mataimakin Gwamna Faruk Lawal Joɓe ya bayyana cewa a ƙarƙashin manufar Gwamnatin Radda ta “Gina Makomarka,” gwamnatin jihar ta samar da ayyukan yi kimanin guda 35,903, a fannoni daban-daban, ciki har da ɗaukar malaman makaranta, naɗin dagatai, da kuma ɗaukar dakarun tsaro na al’umma, ’yan banga, mafarauta da shugabannin addini da suke taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya.

A sahun gaba na jigajigan da suka kasance a taron, sun haɗa da tsohon Gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari; dattijo kuma jigo na siyasa Sanata Abu Ibrahim; hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Ɗahiru Barau Mangal; Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk; Sanata Ibrahim Ida, Wazirin Katsina; da kuma Sanata Hadi Sirika.

Haka kuma akwai Ministan Gidaje da Cigaban Birane, Arc. Ahmed Ɗangiwa, da kuma Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Tsare-tsare, Hajiya Hadiza Bala Usman.

Sauran muhimman mutanen da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Lawal Daura, tsohon Daraktan DSS; Alhaji Aminu Maida, EVC na NCC; Jakada Ahmed Rufai, Sardaunan Katsina kuma tsohon Daraktan NIA; dattijo Sanata Abubakar Mamman Ɗanmusa; Injiniya Abubakar Yar’adua, tsohon Manajan Darakta na NNPC; Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta, Galadiman Katsina kuma Hakimin Malumfashi; Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina; Sanata Abdulaziz Yar’adua; Sanata Muntari Dandutse; da Sanata Nasiru Zangon Daura. Ɓangaren shari’a ya samu wakilci daga Mai Shari’a Musa Danladi, Babban Jojin Jihar Katsina.

Ɓangaren sojoji kuwa ya samu halartar manyan jami’an da suka yi ritaya: Kanal Abdulmumini Aminu, Brig. Janar Ahmed Daku, Kanal U.F. Ahmed, Brig. Janar Maharazu Tsiga (tsohon DG na NYSC), Air Commodore Yusuf Anas, AVM Sadiq Kaita, Major Janar Junaid Bindawa, da Brig. Janar Usman Sani Kukasheka, tsohon Jami’in Watsa Labarai na Sojojin Najeriya, da sauransu.

Sauran manyan baƙi sun haɗa da SGS Barr. Abdullahi Garba Faskari; Hon. Abdulƙadir Mamman Nasir, Shugaban Ma’aikata; Abdullahi Aliyu Turaji, Babban Sakataren Fada na Gwamna; tsoffin Mataimakan Gwamna — Alhaji Tukur Jikamshi, Q.S. Mannir Yakubu, da Alhaji Sirajo Damari; Barr. Ahmed El-Marzuk; Injiniya Nura Khalil; Alhaji Kabir Mashi, tsohon Shugaban FIRS; Alhaji Tukur Bello Ingawa, tsohon Shugaban FCSC; Farfesa Saddique Mohammed na Jami’ar ABU Zaria; Farfesa Sadiq Isah Radda na BUK; Farfesa Mansur Malumfashi na ATBU; Farfesa Suleiman Ahmed Isah na UDUS; Dr. Bashir Ruwan Godiya daga Gamayyar Ƙungiyoyin Kare ‘Yancin Ɗan Adam (CSOs) tare da shugabannin manyan makarantu a jihar.

Haka kuma akwai Injiniya Bala Banye, Kwamishina a Gwamnatin Tarayya, a NPC; Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri, Shugaban Kasa/CEO na NEPAD; Hajiya Mariya Abdullahi; Hajiya Indo Mohammed; Farfesa Badamasi Lawal Charanchi, Shugaban NSIPA; Magatakarda Kabir Yahaya; da Injiniya Bello Lawal Yanɗaki, Shugaban Ƙungiyar ALGON na ƙasa.

Dukkan ‘yan Majalisar Wakilai na Jihar Katsina a Majalisar Tarayya, manyan jami’ai na Majalisar Dokokin Jihar Katsina, wasu daga cikin mambobin Majalisar Zartarwa, shugabannin addinai, wakilan klƙungiyar kwadago da na kasuwanci, da ƙungiyoyin fararen hula da na al’umma, tare da ‘yan kasuwa, duk sun halarta wajen taron.

Babu shakka, muddin dai gwamnati ta yi amfani da muhimmin shawarwarin da aka gabatar a yayin wannan taro, to kuwa zai zama alheri ga al’ummar Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.
__________

Previous Post

Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

Next Post

BAKIN JAƁA (4)

Related Posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar
Babban Labari

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato
Babban Labari

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Next Post
BAKIN JAƁA (4)

BAKIN JAƁA (4)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

February 24, 2024
Lallai Ne A Sallami Shugaban Hukumar Zaɓe – Majalisar Musulunci

Lallai Ne A Sallami Shugaban Hukumar Zaɓe – Majalisar Musulunci

November 13, 2025
Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

August 23, 2024
TSOKACINMU NA YAU (22)

TSOKACINMU NA YAU (22)

March 22, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
  • Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
  • BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.