Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
___________
Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomin Jihar Katsina ta kafa wasu sabbin sassa guda biyu masu muhimmanci. Waɗannan kuwa su ne, Sashen Kula Da Sayayyar Kayayyaki da kuma Sashen Bunƙasa Rayuwar Mata.
An kafa sassan ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci nagari, inganta gaskiya da riƙon amana da kuma inganta ayyukan da ake gudanarwa ga al’umma a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar, kamar yadda shugabannin hukumar suka bayyana.
An ƙaddamar da wannan sabon tsari ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Alhaji Usman Mamman Maska, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen hukumomi da ake ci gaba da aiwatarwa, waɗanda aka tsara domin inganta ingancin aiki, daƙile almundahana da kuma tabbatar da tsarin shugabanci mai bai wa kowa dama a matakin ƙananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, wadda Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Malam Abdul’aziz Lawal Danyari ya sanya wa hannu, hukumar ta ce kafa waɗannan sassa biyu ya yi daidai da babban shirin sauye-sauyen da Gwamnatin Jihar Katsina ke aiwatarwa, wanda ke da nufin gina ƙananan hukumomi masu ƙarfi, masu saurin amsa buƙatun jama’a da kuma mayar da hankali kan jin daɗin al’umma.
Sanarwar ta ruwaito Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, yana bayyana wannan mataki a matsayin wani sabon ci gaba a ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da ingancin gudanar da harkokin ƙananan hukumomi.

“Ƙarfafan hukumomi su ne ginshiƙin samun ci gaba mai ɗorewa. Za mu ci gaba da tallafa wa sauye-sauyen da ke inganta shugabanci nagari da kuma inganta ayyukan da ake samarwa ga al’umma a matakin ƙasa,” in ji Gwamna Radda, kamar yadda aka ruwaito.
A cewar Hukumar, sabon Sashen Sayayya zai kasance mai kula da tsara harkokin sayayya, tabbatar da bin dokoki da ƙa’idojin sayayya da suka dace, ƙarfafa adana bayanai da takardu yadda ya kamata da kuma tabbatar da cewa ana samun cikakkiyar ƙima ta kuɗin da gwamnati ke kashewa wajen kwangiloli a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Ana sa ran sashen zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa ana bin ƙa’idojin da suka dace a harkokin sayayya a ƙananan hukumomi, tare da ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana tafiyar da dukiyar jama’a cikin taka-tsan-tsan da gaskiya.
Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa suna haifar da fa’ida mai amfani ga jama’a, inda ya ce:
“Sashen Sayayya zai tabbatar da bin ƙa’idojin da suka dace, ya ƙarfafa tsarin ladabtar da harkokin kuɗi, tare da tabbatar da cewa ana tafiyar da dukiyar jama’a cikin taka-tsan-tsan. Duk kwabon da aka kashe dole ne ya samar da wata fa’ida ga al’ummar Jihar Katsina.”
Saboda haka, ana sa ran kafa wannan sashe zai samar da ingantaccen tsari na gudanar da harkokin sayayya a matakin ƙananan hukumomi, tare da ba da fifiko ga riƙon amana, adana takardu yadda ya kamata, bin dokoki da ƙa’idoji da kuma amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace.
Hukumar ta kuma bayyana cewa Sashen Bunƙasa Rayuwar Mata zai kasance mai kula da tsara da kuma daidaita shirye-shirye da ayyukan da suka shafi ƙarfafa mata, bunƙasa sana’o’i da kasuwanci, koyar da sana’o’i da kuma inganta ƙwarewa da ilimin mata.
A cewar sanarwar, sashen zai kuma taimaka wajen samar da damar da mata za su samu ta hanyar shirye-shiryen gwamnati da na ƙungiyoyin haɗin gwiwar ci gaba, tare da ƙarfafa mata su taka rawa kai tsaye a harkokin shugabancin ƙananan hukumomi da ci gaban al’umma.
Ana sa ran wannan mataki zai samar da ingantaccen tsari na hukumomi wajen tunkarar batutuwan da suka shafi bunƙasa tattalin arziƙin mata da kuma ƙara yawan shigarsu cikin shirye-shiryen ci gaba a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin saka hannun jari wajen bunƙasa mata, yana mai cewa ƙarfafa mata zai haifar da fa’ida mai yawa ga iyalai, al’ummomi da kuma ci gaban jihar baki ɗaya.
“Ƙarfafa mata yana da matuƙar muhimmanci wajen gina iyalai masu ƙarfi, al’ummomi masu juriya da kuma ingantacciyar al’umma mai wadata. Gwamnatinmu za ta ci gaba da samar da damammaki da za su bai wa mata damar cin ma cikakkiyar nasarar da suke da ikon cimmawa,” in ji shi.
Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa hukumomin ƙananan hukumomi ta hanyar manufofi da sauye-sauyen da za su samar da fa’idodi masu auna tasiri ga jama’a.
“Mun ci gaba da ƙudirinmu na gina hukumomi masu inganci, gaskiya da riƙon amana, waɗanda za su mayar da hankali wajen amsa buƙatu da muradun al’ummarmu a dukkan ƙananan hukumomi 34,” in ji Gwamna Radda.
Hukumar ta bayyana cewa kafa Sassan Sayayya da Bunƙasa Rayuwar Mata, ba wani mataki ne da aka ɗauka shi kaɗai ba, illa dai wani ɓangare ne na jerin sauye-sauye masu faɗi da ake aiwatarwa domin ƙarfafa ƙwarewar hukumomin ƙananan hukumomi a jihar.
Ta tunatar da cewa daga cikin sauye-sauyen da aka aiwatar a baya akwai kafa Sassan Kasafin Kuɗi (Budget Units), Jami’an Kula da Dokar Ɗa’a da Ɗabi’a da kuma Jami’an Kula da Sauyin Yanayi a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
A cewar hukumar, an tsara waɗannan matakai ne domin inganta haɗin gwiwar hukumomi, ƙarfafa riƙon amana da kuma tabbatar da cewa hukumomin ƙananan hukumomi suna da isassun tsare-tsare da ƙwarewar da za su ba su damar fuskantar sabbin ƙalubalen da suka shafi shugabanci, harkokin kuɗi, muhalli da ci gaban al’umma.
A wani ɓangare na aiwatar da sabon tsarin, hukumar ta sanar da cewa shugabannin sabbin Sassan Sayayya za su gudanar da wani horo na musamman a Kwalejin Gudanarwa ta Bala Abdullahi da ke Funtua.
An tsara fara gudanar da horon ne a ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2026, da nufin bai wa jami’an ilimi, ƙwarewa da dabarun da suka dace domin samun nasarar aiwatar da sabon tsarin sayayya.
Ana sa ran horon zai ƙara wa jami’an fahimta game da hanyoyin gudanar da harkokin sayayya, buƙatun dokoki da ƙa’idoji, tsarin adana takardu, da sauran muhimman abubuwan da suka shafi gudanar da harkokin sayayya na gwamnati.
Sabbin sauye-sauyen da hukumar ta ƙaddamar ana sa ran za su ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsarin ƙananan hukumomin Jihar Katsina, tare da samar da ƙarin tsare-tsare da za su ba da damar samun ci gaba mai ɗauke da kowa, musamman ta hanyar ƙarfafa shigar mata cikin harkokin tattalin arziƙi da ci gaban al’umma.
Ta hanyar kafa waɗannan sassa biyu a tsarin ƙananan hukumomi, Gwamnatin Jihar Katsina na ƙoƙarin zurfafa sauye-sauyen da take aiwatarwa, ta hanyar tabbatar da cewa hukumomin ƙananan hukumomi suna gudanar da ayyukansu cikin inganci, riƙon amana da kuma saurin amsa buƙatun jama’a.













