• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, June 13, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 21, 2025
in Gizago
0
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

A hagu, Kwankwaso ne tare da Shugaba Tinubu a lokacin da ya ziyarce shi a Fadar Shugaban Ƙasa, a kwanakin baya

14
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
A hagu, Kwankwaso ne tare da Shugaba Tinubu a lokacin da ya ziyarce shi a Fadar Shugaban Ƙasa

 

Nan da ɗan lokaci ƙanƙane, ana sa ran Madugun Kwankwasiyya kuma jigo a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai canja sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

Da ma can a baya, Kwankwaso ya taɓa zama a jam’iyyar APC inda ya bar Jam’iyyar PDP. Sai dai a wannan karon, akwai wasu ƙalubale da ka iya fuskantarsa, a wannan canjin sheƙar.

Wannan ke nuna yadda siyasar Najeriya ke ci gaba da fuskantar juyin-juya hali, musamman yadda manyan ‘yan siyasa ke barin jam’iyya guda zuwa wata a ƙoƙarinsu na samun mafita ko domin kare burinsu na mulki ko tsira daga danniyar siyasa.

Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Tsaro, ya taɓa zama cikin Jam’iyyar APC a baya, kuma yana daga cikin waɗanda suka taimaka wajen kafa ta a shekarar 2013 daga jam’iyyun CPC, ACN da PDP. Duk da haka, rikicin gida da rashin jituwa da wasu jiga-jigan jam’iyyar, musamman a Kano da Fadar Shugaban Ƙasa, ya sanya ya fice daga APC zuwa PDP, daga bisani kuma ya kafa NNPP tare da kwashe ɗimbin magoya baya, musamman a Arewacin Najeriya.

A yanzu dai rahotanni na nuna yiwuwar dawowar Kwankwaso cikin APC – lamarin da ke barazana kai tsaye ga rayuwar jam’iyyarsa ta NNPP. Idan Kwankwaso ya koma APC, babu shakka za a iya cewa NNPP za ta ruguje – domin Kwankwaso shi ne ginshiƙi, madugu kuma ruhin jam’iyyar. Ba wani babban jigo da zai iya jan akalarta idan ba shi ba. Wannan zai saka dubban magoya bayansa cikin ɗimuwa da rashin tabbas, domin ɗaki ba ya tashi kuma ragaya ta zauna.

Sai dai kuma, komawarsa APC ba lallai ba ne ta zama mafita. Tarihi ya nuna cewa APC ba jam’iyyar da ke cika ɗaukar masu komawa cikinta da hannu biyu ba, musamman idan ba a yarda da su ba ko kuma ana kallon su a matsayin barazana ga waɗanda ke riƙe da madafun iko. Idan Kwankwaso ya koma APC, akwai yiwuwar a can gaba ya fuskanci matsala, idan amfaninsa ya ƙare, kamar dai yadda ta faru da mutane irin su Malam Nasiru El-rufa’i da Ganduje.

Haka kuma, ko a jiharsa ta Kano, za a iya samun matsala idan ya koma APC. Akwai ɓangaren tsohon Gwamna Ganduje. Akwai manyan masu sha’awar takarar gwamna a 2027, kamar Mataimakin Shugaban Majalisar Zartarwa, Sanata Barau I. Jibrin da Gawuna da sauransu. Haka kuma, shi Gwamna mai ci yanzu a NNPP, Abba Kabir Yusuf, yaya zai yi? Zai bi Kwankwaso zuwa APC ne ko a’a kuma yaya takararsa za ta kasance a 2027?

Shugaba Tinubu, wanda yanzu ke kan mulki, ba zai so wani ɗan siyasa irin Kwankwaso ya dawo ya nemi ɗaukaka ko ya janyo hankalin jama’a fiye da shi ba. Wannan na nufin, komawar Kwankwaso APC na iya zama “gaba kura baya sayaki” – babu tabbas, babu kwanciyar hankali. Kawai zai zama gugar yasa ne, idan an kammala yasar rijiyar 2027, sai a yada ita.

A ɗaya bangaren kuma, idan Kwankwaso ya nace a NNPP, ya ƙi komawa APC kuma ya ƙi shiga cikin Jam’iyyar haɗaka ta ADC ba, akwai barazanar cewa NNPP za ta rasa tasiri a zaɓen 2027. Wannan kuwa saboda jam’iyyar ADC – wacce ke ƙoƙarin kafa wata babbar gwamnatin haɗaka, tana ƙunshe da manyan ‘yan siyasa masu ƙima da tasiri kamar, Atiku Abubakar, Peter Obi, da Malam Nasir El-Rufa’i. Haɗin ƙarfinsu na iya cin karensu babu babbaka, musamman ma idan suka yi nasarar tsayar da ɗan takara mai ƙima da amsuwa ga ‘yan Najeriya.

Don haka, Kwankwaso na cikin mawuyacin hali – idan ya koma APC zai iya fuskantar dannewa da wulaƙanci; idan kuma ya tsaya a NNPP, yana iya rasa gagarumar dama ta siyasa saboda ƙarancin goyon baya da haɗin gwiwa daga sauran manyan ‘yan adawa.

A kowane hali, komawar Kwankwaso zuwa APC na ɗauke da manyan ƙalubale da illoli, da kuma wasu ‘yan fa’idodi masu wuyar samu. Abin da ya rage shi ne dabararsa da ƙwarewarsa su fisshe shi, wajen tantance inda zai fi samun kariya, ɗaukaka da tasiri a siyasar Najeriya. Amma ko ya koma ko bai koma ba, siyasar 2027 za ta buƙaci haɗin gwiwa, hangen nesa, da sabon salo – kuma ga shi lokaci yana ta ƙurewa.
__________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

Next Post

ZUWA GA ‘YAN UWA MUSULMI ‘YAN SHI’A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?

Related Posts

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
Gizago

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Next Post
ZUWA GA ‘YAN UWA MUSULMI ‘YAN SHI’A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?

ZUWA GA 'YAN UWA MUSULMI 'YAN SHI'A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Hararar Baba Ganduje

Hararar Baba Ganduje

June 29, 2023
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
Yau Maulidin Katsina First

Yau Maulidin Katsina First

July 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe
  • FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco
  • Yau Za A Fafata Tsakanin Canada Da Bosnia-Herzegovina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

June 13, 2026
FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

June 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.