An Kammala Jana’izar Shugaba Buhari Cikin Jimami Da Alhini
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Tun daga ranar Litinin da ta gabata, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci a taron manyan jami’an gwamnati da shugabannin ƙasashen Afirka zuwa garin Daura da ke Jihar Katsina, domin halartar jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Landan.
An gudanar da sallar jana’izar bisa tsarin Musulunci a filin saukar jirgin sama na PMB Helicopter Ground da ke Daura, ƙarƙashin jagorancin Babban Limamin Daura, Sheikh Alhaji Salisu Rabi’u.

Adadin mutanen da suka shiga sahun sallar jana’izar ba su ƙidayuwa, domin kuwa sun zo ne daga sassa daban-daban na duniya, lamarin da ya nuna irin girman soyayya da martabar da ake nuna wa marigayin.
Shugaba Tinubu ya samu rakiyar wasu fitattun shugabannin Afirka ciki har da Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló, Firayim Ministan Nijar Ali Lamine Zeine, da tsohon Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou – alamar girmamawar da marigayi Buhari ya samu a fagen diflomasiyyar yankin.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima; Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar; da Farfesa Yemi Osinbajo, su ma sun halarci jana’izar. Hakan ya nuna haɗin kan ‘yan siyasar Najeriya da girmamawar da ake wa marigayi shugaban ƙasa.
Shugabannin Majalisar Tarayya da suka halarta sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Sanata Kawu Sumaila; Sanata Abdulaziz Yari; Sanata Sani Bello; tsohon Sanata Abu Ibrahim; da tsohon Sanata Yariman Bakura.

Shugabannin tsaro da suka halarci jana’izar sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede; Babban Sufetan Ƴan Sanda, Kayode Egbetokun; da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla. Sauran su ne tsohon Babban Hafsan Tsaro, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), da tsohon Darakta Janar na Hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci ayarin gwamnatin jihar, wanda ya haɗa da Mataimakinsa Faruƙ Lawal Jobe; Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; Sakataren Gwamnati, Barista Abdullahi Garba Faskari; da sauran kwamishinoni.
Daga Gwamnatin Tarayya kuwa, waɗanda suka halarta sun haɗa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Lamurran Siyasa da Wasu Al’amura, Ibrahim Kabir Masari; Ministan Ƙananan Harkokin Lafiya; Ministan Gidaje da Cigaban Birane; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai; Ministan Tsare-Tsare da Tattalin Arziki; Ministan Ƙananan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle; da Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari. Sauran sun haɗa da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, da tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami.
Gwamnonin jihohi da dama sun halarci taron, ciki har da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq. Sauran su ne Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, na Jihar Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf; Gwamnan Kaduna, Uba Sani; Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; Gwamnan Jigawa, Umar Namadi; Gwamnan Kebbi, Nasir Idris; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu; Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun; Gwamnan Edo, Monday Okpebholo; Gwamnan Imo, Hope Uzodimma; da Gwamnan Cross River, Bassey Edet Otu.
Tsoffin gwamnonin da suka halarta sun haɗa da Ibrahim Shehu Shema (Katsina); Ali Modu Sheriff (Borno); Nasir El-Rufai (Kaduna); Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato); da Yahaya Bello (Kogi).

Fitattun ‘yan kasuwa kamar Alhaji Aliko Ɗangote, Alhaji Sayyu Dantata, da Alhaji Ɗahiru Barau Mangal sun halarci jana’izar tare da sauran manyan baƙi. Haka kuma, ɗan Shugaban Ƙasa, Mista Seyi Tinubu, shi ma ya halarta.
Sarakunan gargajiya da suka halarci jana’izar sun haɗa da Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman; Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruƙ Umar Faruƙ; da Sarkin Kano, Mai Martaba Aminu Ado Bayero.
Dukkanin waɗanda suka halarta sun bayyana alhini da jimami a kan rasuwar marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya taɓa shugabantar ƙasar a matsayin Shugaban Mulkin Soja da kuma Shugaban Ƙasa na Dimokuraɗiyya.
Mafi yawan mutanen da suka yi tsokaci da jimami, sun bayyana cewa Janar Buhari ya kasance mutum mai tsananin tsoron Allah, mai gaskiya, da kishin ƙasa, wanda ya bar tarihi mai tasiri a duniya.
An gabatar da addu’o’i domin neman gafara daga Allah da kuma samun Aljannatul Firdaus ga marigayin, tare da addu’ar Allah ya ba iyalansa, mutanen Daura, Jihar Katsina, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya haƙuri da juriya a wannan babban rashi.













