• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sharhi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

SHARHIN LITTAFI

Abubakar AbdurRahman Dodo by Abubakar AbdurRahman Dodo
December 24, 2024
in Sharhi
0
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Bangon Littafin

48
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Daga Abubakar AbdurRahman Dodo

Related posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

November 16, 2023
Bangon Littafin

 

•••••••

Sunan Littafi: Mu Haɗa Ƙarfi Don Shawo Kan Tu’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi.
Marubuci: John Fagbola.
Mai Fassara: Abubakar AbdurRahman Dodo.
Farashi: Ba A Bayyana Ba.

•••••••

Wannan littafi mai suna “MU HAƊA ƘARFI DON SHAWO KAN TA’AMMALI DA MIYAGUN ƘWAYOYI,” wanda Mista John Fagbola ya wallafa cikin harshen Ingilishi, kuma Abubakar AbdurRahman Dodo ya fassara cikin harshen Hausa, faɗakarwa ce KAN ILLOLIN DA KE TATTARE DA TA’AMMALI DA MIYAGUN ƘWAYOYI a Nijeriya, har ma da faɗin duniya baki ɗaya. Don haka a gabatarwar wannan littafi aka ruwaito cewa:

“Shan ƙwaya ko kayan maye ta zama matsala a faɗin duniya. Gwanatin Tarayyar Najeriya (musamman Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta NDLEA), da gwamantocin jihohi da ƙananan hukumomi da Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, duk suna fafutikar yaƙi da sha da fataucin miyagn ƙwayoyi.

Don haka wannan littafin faɗakarwa ce ga ƙasashen duniya, kan su ɗauki ƙwararan matakan da suka dace wajen shawo kan shan ƙwayoyi da kayan maye ta ko’ina.

“Yaƙi da miyagun ƙwayoyi dole ne a fafata shi, musamman tun daga gida, tun da tarbiyya ma daga gida take farawa. Wajibi ne a fara ta kan yara da matasa saboda su ne ke tattare da haɗarin afkawa cikin sha’anin shaye-shaye.

Wasu daga cikin abubuwan da ke zama ƙwaya

Saboda manufar shawo kan shan miyagun ƙwayoyi da kayan maye a tsakanin matasa, ya zama dole a tarairaye su ta hanyar gudanar da shirye-shiryen faɗakarwa, ta yadda za su farga su fahimci irin haɗarin da ke tattare da miyagun ƙwayoyi ko kayan maye.

“Wannan ne dalilin bijiro da buƙatar ganin makarantu sun kafa ƙungiyoyin faɗakarwa kan illar da ke tatare da miyagun ƙwayoyi da kayan maye, don kauce musu (DRUG-FREE CLUBS), inda za su riƙa gudanar da shirye-shiryen faɗakarwa da za a riƙa yi wa yara da matasa a yankunan karkara da birane.”

Bayan gabatar da matsalar miyagun ƙwayoyi ga alumma, musamman iyaye da malamai, sai aka nusar da su alamun da za su gane cewa, ɗa ko yarsu na taammali da kayan maye. Cewa:

                    ALAMU A GIDA
1. Watsi da harkokin iyali da ‘yan uwa.
2. Rashin bin dokokin iyaye.
3. Ƙin sauke nauyin da ya rataya a kan mutum.
4. Yawan zage-zage.
5. Kwatsam mutum ya daina cin abinci ko ƙara yawan abin da yake ci.
6. Rashin dawowa gida a kan lokaci.
7. Ƙin bayyana inda suka je.
8. Yawan bayar da uzuri kan abin da yake/take aikatawa.
9. Yawan zama a cikin ɗaki.
10. Yin ƙarya kan abin da ya/ɗa suka aikata.
11. Ƙin shiga jama’a.
12. Yin shiru a kowane lokaci.
13. Riƙe alamun da ke nuni da shan ƙwaya, kamar fankon ashana da
abin kunna wuta ‘lighter’ da takardar yin kwarkwaron murza molin
shan tabar wiwi.
14. Dariya ba-kai-ba gindi rashin natsuwa.
15. Harzuƙa da tashin hankali

              ALAMU A MAKARANTA
1. Faɗuwa jarrabawa da rashin ci gaba.
2. Ƙin ji ko rashin biyayya ga malamai, da rashin zuwa makaranta.
3. Rashin sha’awar karatu.
4. Barci a cikin aji.
5. Ƙin yin aikin gida.
6. Yi wa hukumar makaranta tawaye.
7. Yawan mantuwa da ƙin mayar da hankali.
8. Ƙin sanar da iyaye taron iyaye da malamai (duba shafi na 24).

Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi kan haddasa hauka

Wanda duk ya karanta wann littafi, haƙiƙa zai fahimci ma’anar ƙwaya, wato cewa, “Ƙwaya da kayan maye curin sinadarai ne saɓanin abinci, wanda in aka yi amfani da shi a jiki ake samun sauyin tunani (na ruɗani) ko wani motsi (zogi) a jiki.” Uwa-uba, an bayyana masu alfanu, wato nauukan magungunan da likita ko jamiin kula da lafiya ya bai wa majinyaci. Kuma su ma irin waɗannan magungunan idan aka sha su ba bisa ƙaida ba, tabbas za su yi wa jiki illa mummuna, musamman ƙwaƙwalwa, tamka yadda aka yi bayani a shafi na ɗaya a littafin.

A cikin wannan littafi na faɗakarwa, an nusar da alumma, musamman matasa, kan nauukan miyagun ƙwayoyi da sauran kayan maye, har ma da tsirrai da ke fitowa a yankuna da dama na ƙasar nan. Kodayake wasu nauukan hatsi ne ake sarrafawa, don kawai a rikita ƙwaƙwalwar alumma masu sha ko shaƙa, har ma da masu yi wa kansu allurar hodar ibilis. Sannan an yi bayani game da sinadaran marmari, waɗanda ake juya akalar amfaninsu, har su illata jiki da ƙwaƙwalwar ɗan Adam.

               SINADARAN MARMARI
Sinadaran marmari kayan ci da sha ne da aka aminta da su a zamantakewar al’umma. Waɗannan sinadaran marmari suna iya zama ƙwaya ko kayan maye, domin idan aka yi amfani da su, za su iya zama abubuwan ci da sha ne da aka dogara da marmarin amfani da su a yau da kullum. Nau’ukan waɗannan ƙwayoyin sinadaran marmari sun haɗa da taba da giya da goro da gahawa (coffee) da giyar da aka sarrafa da ruwan da aka tatso daga kwakwar manja (duba shafi na 3).

Sannan a shafi na 19, an jero halayen da ƙwaya ke haifarwa kamar haka: Alamun daina shan ƙwaya ko kayan maye. Waɗannan alamu kan bayyana ne kwatsam da zarar an daina shan ƙwaya ko rage shan ƙwayoyin magani barkatai ko kayan maye da ke cusa wa mutum nishaɗi.

Dawowa daidai Wannan yanayi ne da shan ɗimbin ƙwayar da aka saba sha ke haifar da irin tasirin da aka saba ji tun farko.

             Ƙarin Sinadaran Marmari
Ƙwaya ce da ake amfani da ita ke haifar da ƙarin yawan sindaran marmari (irin su gahawa- ‘coffee’ da goro da taba da makamantansu) da ake ta’ammali da su. Don haka da zarar mutum ya daina shan ƙwaya ko kayan maye da ke ƙara masa/mata kuzari, sai ya/ta ji kawai ko a ga yana/tana amfani da irin nau’ukan sinadaran marmari, don maye gurbin abubuwan da ya/ta saba sha. Halayen da ƙwaya ke haifar wa ƙwayoyin kashe zafin ciwo da kyautata annashuwa da jin daɗin barci. Wato nau’ukan waɗannan ƙwayoyi na magani ne da ake yi wa laƙabi a Inglishi da ‘Narcotics.

A ƙarshen littafin an yi nuni da yadda ake baza kayan maye kyauta, ta yiwu ana nufin kamar gidan biki, to dama kan samu ga masu neman na ɓagas, har su lalata tunaninsu. Misali cewa: SAMUN ƘWAYOYIN CIKIN SAUƘI: Idan ƙwayoyi suka samu da yawa a kyauta, sai mutane su samu sauƙin samun su, har su sha yadda za su bugu ko su yi musu illa. Alal misali, barasa da taba da ire-iren nau’ukan kayan maye, waɗanda suka shahara a Nijieriya.

Wasu ƙwayoyin da suka haɗa da maganin barci da masu sanya ƙarfi da kuzarin jiki, ana samun su a shagunan sayar da magunguna, ga su nan birjik da yawa, tun da za a iya sayen su cikin sauƙi.

Saboda littafin an wallafa shi da wani irin salo, tun da farko aka yi bayanin yadda za a shawo kan wannan mummunar ta’ada: Misali a shafi na 33 an bayyana cewa: 

HANA TA’AMMALI DA MIYAGUN              ƘWAYOYI: GUDUNMUWAR IYAYE DA MAKARANTA

√ A kodayaushe iyaye su riƙa binciken ‘ya’yansu maza da mata, tare da duba aljihun ƙananan yara, don tabbatar da cewa ba sa ajiye miyagun ƙwayoyi.

√ Iyaye ka da su riƙa aiken ƙananan yara sayen ƙwayar magani a shagunan sayar da magunguna, domin ta irin wannan hanyar ce za su kare ‘ya’yansu daga sayen magunguna barktai a duk lokacin da suke da kuɗi.

√ Bai kamata iyaye su riƙa ajiye ƙwayoyi ko magunguna sakaka a ko’ina da a cikin gidansu ba. A daina a jiye magunguna a wuraren da ke da sauƙin isa ga ƙananan yara.

√ Malamai da iyaye su riƙa gargaɗin ‘yan makaranta tare da nuna musu illar da ke tattare da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

√ Shugabannin makaranta tare da haɗin gwiwar sauran malamai, ka da su taɓa bari a riƙa hada-hadar cinikin saye da sayarwar miyagun ƙwayoyi a harabar makaranta.

√ Lallai iyaye su lura da irin abokai da ƙawayen da ‘ya’yansu ke hulɗa da su. Yin hakan yana da matuƙar fa’ida don tabbatar da cewa ba sa hulɗa da miyagun abokai ko ƙawaye, domin yin hakan yana da matuƙar fa’ida don tabbatar da cewa ba sa hulɗa da miyagun abokai ko ƙawaye da ka iya rinjayar su su afka ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

√ A duk lokacin da ‘ya’ya suka kamu da rashin lafiya, iyaye su riƙa kai su asibiti da kansu.

Shaye-shayen miyagun muggan ƙwayoyi kan haddasa matsananciyar cuta

Ni dai a nan zan ƙarƙare da shawartar matasa, har ma da masu shaawar taammali da miyagun ƙwayoyi, lallai su san cewa, fataken ƙwaya, dole a fatattake su, don suna lalata alumma.

Su kuwa masu sha da yan zuƙe-zuƙe, wajibi ne su sani cewa, kayan maye, musamman miyagun ƙwayoyi na da matuƙar tasirin haifar da kisan gillar alumma da sare-saren dabbanci da sace-sacen dukiyar alumma. Uwa-uba, mafi yawan mahaukatan da ke gararamba a titunanmu, ƙwayoyi na da tasiri a zamansu haka. Allah Ya sa mu gane, mu nisanci wannan mummunar taada. Amin.
_______________
Abubakar Dodo, ɗan jarida mai zaman kansa kuma marubuci. Ya rubuto wannan sharhi ne daga Kano.

Previous Post

ALLAH YA JI ƘAN DSP ABBA ƊANMALAM

Next Post

EXTINCTION

Related Posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Sharhi

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi
Sharhi

SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

November 16, 2023
REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate
Sharhi

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

August 21, 2023
Next Post
EXTINCTION

EXTINCTION

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

April 13, 2026
Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

July 31, 2025
Ya Zama Wajibi A Ɗauki Mataki A Kan Minista Wike

Ya Zama Wajibi A Ɗauki Mataki A Kan Minista Wike

November 12, 2025
Muhammadu (Saw): Manzon Tsira Sha Yabo

Muhammadu (Saw): Manzon Tsira Sha Yabo

November 14, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.