• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, June 17, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Ruhin Bukar Usman

WAƘE

Khalid Imam by Khalid Imam
May 11, 2024
in Adabi
0
Ruhin Bukar Usman

Dokta Bukar Usman

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ruhin Bukar Usman

(Wake)

Related posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026

Khalid Imam

*****

Dokta Bukar Usman, OON

Ganga ta jikin Bukar ce,
Ke zaune garin Abuja,
Ruhin Bukar Usman duka
Ni na shaida da kaina,
Suna Biu cibiyarsa,
Ni Khalidu ni da kaina,
Zahiran na gani idona.

Garin Biu ne mahaifa,
Gun Bukar Usmanu gwarzo,
Ita dawa tushiyarta,
Asalinta da salsalarta,
Jijiyar bishiya gidanta,
Ko tai inuwa da rassa,
A maƙota babu shakka.

Na je Biu na ziyarci,
Gidan su Bukar gwanina,
Ɗan dangi ne cikakke,
Shi ba inuwa ba ne ba,
Ta giginya ko alama,
Ya amfana wa dangi,
Kogi ne shi ga kowa.

A garin Biu babu shakka,
Bukar Usmanu giwa,
Rijiya na tsakiyar gari ne,
Kowa na shan ruwanta,
Mutan Biu ni Imamu,
Sun shaida min da kansu,
Bukar ɗa ne na kishi.

Dattijawa har saraki,
Malaman Biu har matasa,
Mata da maza da yara,
Sun yaba wa Bukar da gaske,
Jinjina sun yi wa ɗansu,
Darajar Biu ya ɗaga ta,
Duniya duka ta yi shaida.

Ƙasar Biu tarihinta,
Bukar Usman fasihi,
Ya taskace duk a kundi,
Shi yai aikin da kansa,
Duniya yau ta karanta,
Bukar ɗa ne na karimi,
Ɗa mai kishin mahaifa,

Jarin sana’a ga mata,
Maza manya matasa,
Bukar Usmanu Dokta,
Ya ba dubbai da kansa,
A Garin Biu ya yi bohol,
Ruwa ya ba maƙota,
Bukar bai manta tushe.

Irin noma da taki,
Na zamani a kyauta,
Bukar ya raba na noma
Domin bunƙasa noma,
Amfani yai yabanya,
Arziki jama’a su samu,
A ƙasar Biu kewayenta.

Ilimin tata da gyara,
Na mai na gyaɗa da sannu,
Kamfaninsa Bukar ya kawo,
Ƙasar Biu don manoma,
Kishin jama’a ƙasarsa,
Tasa shi hakan da kansa
Bukar gwarzo na nuni.

__________

(HM) Khalid Imam
Garin Biu
5.50 NY
11 ga Afirelu, 2024

Previous Post

Visit to Biu

Next Post

Ziyara Biu

Related Posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Adabi

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Next Post
Visit to Biu

Ziyara Biu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ƊANLADI HARUNA

ƊANLADI HARUNA

July 12, 2024
NO TO WAR

NO TO WAR

June 20, 2025
KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

August 9, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

February 9, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
  • BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA
  • Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

June 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.