• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Sharhin Littafin Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria)

SHARHIN LITTAFI

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
May 9, 2024
in Adabi
0
A Review of Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria

Bangon littafin Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria da marubucinsa, Farfesa Abdullahi Y. Shehu

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sharhin Littafin Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya
(Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria)

Bukar Usman

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026

 

Wannan shi ne sharhin da Dokta Bukar Usman ya rubuta a kan littafin Boko Haram Da Sauran Kalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria). Ambasada Abdullahi Y. Shehu ne ya rubuta littafin kuma aka ƙaddamar da shi a zauren taro na Shehu Musa ’Yar’adua Centre, Abuja, a ranar 19 ga Afrilu, 2024.

Marubuci, Abdullahi Y. Shehu

√ Taƙaitaccen Tarihin Ambasada Abdullahi Y. Shehu

An haifi Abdullahi Yibaikwal Shehu, OON a ranar 15 ga Oktoba, 1963. Yana da shaidar karatun digirin digirgir kuma Farfesa ne a Ilimin Laifuffuka. Haka kuma yana da shaidar ƙwarewar fiye da shekaru 30 a fannin ayyukan al’umma daban-daban, waɗanda suka haɗa da harkokin tsaro, tabbatar da doka, hulɗar jakadanci da kuma koyarwa a aji.

Ambasada Shehu ya taɓa zama Jakadan Najeriya a ƙasar Rasha da kuma kujerar jakadanci ta dindindin a Jamhuriyar Belarus. A can baya kuma, shi ne Shugaba na farko na Hukumar Yaƙi da Almundahanar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma wato Inter-Governmental Action Group (GIABA) da kuma Hukumar Daƙile Zambar Kuɗaɗe wato Financial Action Task Force (FATF). Kafin ya samu wannan muƙami, ya kasance Daraktan Bincike da Horarwa na Hukumar wato Economic and Financial Crime Commission (EFCC) ta Najeriya.

Haka kuma Ambasada Shehu ya taɓa yin aiki na taƙaitaccen lokaci a Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Sashin Binciken Laifuka da Miyagun Ƙwayoyi wato United Nations Office on Drugs and Crime (UNODC) a Vienna, ƙasar Austria a matsayin Ƙwararren Jami’i (bangaren Yaƙi da Almundahanar Kuɗi/Halatta Kuɗin Haram). Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Babban Jami’i Mai Ba Da Shawara ta Fuskar Gudanarwa (Yaƙi da Almundahana) na Hukumar UNODC a Najeriya. Haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin Mashawarci Na Musamman ga Gwamnan Jihar Filato, ɓangaren Mu’amala Tsakanin Hukumomin Gwamnati.

Ambasada Shehu sanannen marubuci ne da ya wallafa littattafai guda takwas kuma ya rubuta takardun bincike da suka shafi kimiyya sama da guda 50.

Littafin Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria

√ Sharhin Littafi

Sunan Littafi: Boko Haram Da Sauran Kalubalen Tsaro A Najeriya
(Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria)
Yawan Shafuka: 669
Marubuci: Abdullahi Y. Shehu
Kamfanin Wallafa: National Open University of Nigeria
Shekarar Wallafa: 2024
Farashi: Ba a bayyana ba
Mai Sharhi: Bukar Usman

Bari mu fara nazarin littafin nan tun daga Babi na 13, wanda shi ne babi na ƙarshe. Kamar yadda na tantance, an kammala rubuta littafin nan a cikin watan Fabrairu, 2023, bayan an kammala babban zaɓe a Najeriya, kafin shugabannin da aka zaɓa su kama aiki a watan Mayu na shekarar. Amma duk da haka, an yi bayanai dalla-dalla masu gamsarwa game da al’amura wadanda har yanzu ke kawo damuwa a Najeriya wajan tsaro.

Dokta Bukar Usman, a yayin da yake gabatar da sharhi a kan littafin Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria).

Marubucin ya rubuta littafin ne a yayin da yake kan aiki a matsayinsa na Jakadan Najeriya. Ya ce duk da tarin aikin da ke gabansa, yakan samu lokacin a ƙarshen mako ya rubuta littafin. Bayan ya gama rubuta littafin, sai kuma tsautsayin na’ura ya gitta, inda gaba ɗayan abin da ya rubuta ya ɓace. Kan haka ya sake dawowa baya, ya fara rubuta littafin tun daga farko. Babu shakka wannan babban darasi ne abin koyi ga ma’aikatan gwamnati da ke da ra’ayin rubutu.

√ Dalilan Da Suka Sanya Aka Rubuta Littafin

Tun daga shafukan farko marubucin ya bayyana dalilan da suka sanya ya rubuta wannan littafi. Ya bayyana cewa ɗaya daga dalilansa na rubuta littafin shi ne, kishinsa na bunƙasa ilimi game da matsalolin tsaro da suke fuskantar ƙasarsa. Ya faɗaɗa bayani a kan haka, a shafi na 34, inda ya ce, yana buƙatar ya samar da gamsassar fahimta game da al’amarin Boko Haram da sauran matsalolin tsaro da suka danganci ta’addanci, satar mutane domin amsar kuɗin fansa da suke faruwa, musamman ma a Arewacin Najeriya. Marubucin ya samar da bayanai game da tushen faruwar matsalar, dalilan faruwar su da kuma yadda al’amarin ya barbazu zuwa sassa daban-daban. Haka kuma ya tattauna irin matakan da hukumomin tsaro suka riƙa ɗauka dangane da matsalolin na tsaro da kuma irin tasirin matakan. Daga nan kuma marubucin ya faɗaɗa bayaninsa, inda ya gabatar da muhimman shawarwarin yadda za a magance waɗannan matsaloli na tsaro da ke faruwa a yanzu da kuma yadda za a daƙile faruwar su a nan gaba.

Haƙiƙa, ba domin ya samu kuɗi ya rubuta littafin nan ba, kamar yadda ya bayyana mani, a lokacin da ya buƙace ni da in rubuta sharhi a kan littafin. Ya bayyana mani cewa, dukkan adadin kuɗin da aka samu daga littafin, a yayin ƙaddamarwa, zai sadaukar da su ga gidauniyarsa, ‘domin bayar da tallafin ga mutanen da ibtila’in Boko Haram ya faɗa ma wa da kuma sauran mabuƙata da ke fuskantar matsaloli daban-daban, a sakamakon rikice-rikice a Najeriya.

Ya kuma sadaukar da littafin nasa ga sojoji, masu tabbatar da doka da oda da sauran jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a yayin yaƙi da ta’addanci da sauran ayyukan ɓarna da laifuffuka a Najeriya. Haka su ma farar hula a Najeriya, waɗanda suka cutu daga ayyukan ta’addancin ’yan bindiga da masu kama mutane domin kuɗin fansa, duk an tuna da su a wannan littafi.

Wasu daga cikin mahalarta taron, tare da marubucin littafin, Farfesa Abdullahi Y. Shehu (na zaune daga hagu, a layin gaba).

Marubucin ya bayyana cewa tun da farko, Mohammed Yusuf ne ya kafa ƙungiyar Boko Haram, duk da cewa wasu bayanan na daban sun nuna cewa wasu ne suka kafa ƙungiyar a can baya, kafin bayyanar shi. Abin da dai aka sani shi ne, Mohammed Yusuf ne ya kai ƙungiyar Boko Haram zuwa Maiduguri, Jihar Borno, inda a sannu-sannu har ta ƙaddamar da harin ta’addanci da tada ƙayar baya a shekarar 2009. A shekarar 2014 ce Gwamnati ta soke ƙungiyar, tare da ‘yar uwarta ta Ansaru, a lokacin da aka fahimci cewa sun tsunduma cikin ayyukan ta’addanci a zahiri.

Haka kuma, duk da cewa a shekarar 2018 Gwamnati ta shelanta cewa ta durƙusar da Boko Haram, amma abin takaici; har zuwa yau (2024) da aka wallafa littafin nan, ana ganin ayyukan assha na ƙungiyar, duk da cewa ba manya ba ne kamar a can baya, kamar kuma yadda ake ta fama da munanan sakamakon ayyukan ƙungiyar da suka aikata a can baya.

A ƙoƙarinsa na ganin cewa mai karatu ya fahimci al’amuran sosai, marubucin ya sadaukar da Babi Na Biyu na littafin, inda ya riƙa fassarawa da samar da bayani dalla-dalla dangane da bambance-bambancen da ke akwai tsakanin ‘ta’addanci’ da ‘tayar da ƙayar baya.’ Ya samar da gamsasshen bayani game da al’amuran biyu a Babi Na Uku.

Kamar yadda aka sani, ’yan ta’adda na buƙatar kuɗi domin gudanar da rayuwarsu da kuma gudanar da munanan hare-harensu, marubucin ya yi bayani a Babi Na Shida, game da batutuwan ‘ɗaukar nauyin ta’addanci,’ ‘harƙallar kuɗin haram’ da sauran hanyoyin da ƙungiyar ke samun kuɗi a cikin gida da kuma ƙasashen waje. A nan ina kira da babbar murya ga masana da jami’an tsaro da su maida hankali sosai a wannan. Fahimtar hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar zai zama jagora ga jami’an tsaro, yadda za su samar da hanyoyin daƙile yadda ’yan ta’addan ke samun kuɗin gudanar da munanan ayyukansu. Hakan zai sanya al’umma su tsira daga alkaba’in waɗannan muggan ƙungiyoyi.

Wani abin da ya kamata a sani shi ne, su al’ummar ƙasa, babu abin da suke buƙata daga jami’an tsaro da hukumomi, illa a samar masu da yanayin walwala da kuma yanayin da zai ba su damar gudanar da al’amuransu na rayuwa a ko’ina kuma a kowane lokacin, ba tare da suna fuskantar cikas ko barazana ba.

√ Al’amuran Da Aka Tattauna

Al’amarin Boko Haram shi ne babban jigon tattaunawa a littafin nan. An bayyana haka ɓaro-ɓaro cikin launin fari, a haruffan da aka rubuta sunan littafin. Kodayake kuma kaso mafi yawa na littafin yana ƙunshe ne da nazari, tattaunawa da tariyar al’amuran da suka faru dangane da tayar da ƙayar baya da kuma ta’addanci, inda aka kalli batun a matsayin wani al’amari da ya zama ruwan dare, gama duniya. An tattauna kan al’amuran da suka yi sanadiyyar samuwar ƙungiyoyin na ta’addanci da yaɗuwar su da kuma irin hanyoyi da sale-salen yadda aka tunkari yaƙi da su domin daƙile su ko kuma kawar da su gaba ɗaya.

Hagu Zuwa Dama: Mai Girma Mai Shari’a Yargata Nimpar, Kotun Ɗaukaka Ƙara, Wakiliyar Mai Girma Mai Shari’a Mariam Aloma Mukhtar, GCON, tsohuwar Babbar Jojin Najeriya (Uwar Taro); Dokta Bukar Usman, mai sharhi kan littafin “Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya” (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria); Birgediya-Janar IU Babangida, Wakilin Prince (Engr) Arthur Eze, OFR, Shugaban Kamfanin Atlas Oranta Petroleum (Babban Baƙo Mai Ƙaddamarwa); Manjo-Janar Paul C. Tarfa (mai ritaya), CON (Shugaban Taro); Dokta Aliyu Modibbo Umar, Mataki na Musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ta Ɓangaren Ayyuka, Wakilin Mataimakin Shugaban Ƙasa (Babban Baƙo na Musamman); Janar Yakubu Gowon, GCFR, tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya (Uban Taro); Umar Usman Kadafur, Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Wakilin Gwamnan Jihar Borno.

Marubucin ya yi ƙoƙari matuƙa wajen kwance bayanan al’amuran, tare da madogara daga cikin gida da ma na waje. Ya samar da bunƙasassar ƙididdiga, kodayake wasu ƙididdige-ƙididdigen akwai shakku a tare da su, musamman ma waɗanda suke ɗauke da bayanan takamaiman adadi; kasancewar abu ne mai sauƙi a iya jirkita su, ko a samar da na bogi. Marubucin ya tatso hujjoji daga bayanan shugabannin ’yan tada ƙayar baya da kuma wasu daga mabiyansu da jami’an tsaro suka kama.

Sakamakon binciken marubucin ya nuna cewa ‘a cikin gida’ aka ƙirƙira kuma aka reni ƙungiyar Boko Haram. A Jihar Borno aka dasa ta kuma aka yanke mata cibiya, kafin daga bisani ta yaɗu zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan. A ta bakin marubucin, da tun da farko gwamnati ta saurari rahotannin sirri da shawarwarin masana harkar tsaro da kunnuwan basira kuma da ta ɗabbaƙa shawarwarin kwamitocin da ita kanta gwamnatin ta kafa tun da farko, domin binciken al’amarin, da tuni an kawar da ƙungiyoyin da munanan ayyukansu na ta’addanci daga cikin al’umma. Kodayake bayanai marasa makama da shaci-faɗi sun cika ko’ina, wanda hakan ya haddasa aka rasa fahimtar al’amarin na Boko Haram gaba ɗaya, sannan kuma aka gaza fuskantar matsalar kai tsaye domin magance ta. Gwamnati ta riƙa ƙyamatar yin tattaunawar sulhu da zuciya ɗaya, da nufin gano koken ’yan Boko Haram ɗin. Haka kuma a farkon al’amarin, sojoji ba su da isassun kayan aikin da za su iya tunkarar masu tada ƙayar bayan da tsarin faɗansu na sari-ka-noƙe, wanda ba tsari ne na faɗan gaba-da-gaba ba, da aka saba gani.

Hatta lokacin da matsalar ’yan Boko Haram ta warwatsu, tattaunawar sulhu da gwamnatocin jihohi suka riƙa ƙullawa ba su samar da nasara ba, domin kuwa an samu ƙaruwar ƙungiyoyin ’yan ta’addan daji da sauran ƙungiyoyin tada ƙayar baya. An girke jami’an sojoji a kusan ko’ina a sassan ƙasar nan, domin samar da tsaro da zaman lafiya. An yi ta samun zarge-zargen almundahana da ɗinbin kuɗaɗen da gwamnati ta samar domin sayen makamai da kula da walwalar jami’an tsaron.

Hagu Zuwa Dama: Manjo-Janar Paul C. Tarfa (mai ritaya) CON, Shugaban Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa Maso Gabas (Shugaban Taro); Janar Yakubu Gowon, GCFR, tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya (Uban Taro); Umar Usman Kadafur, Mataimakin Gwamnan Jihar Borno (Wakilin Gwamnan Jihar Borno); Farfesa Abdullahi Y. Shehu, marubucin littafin Boko Haram Da Sauran Kalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria); Dokta Bukar Usman, mai sharhi kan littafin “Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya” (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria); Dokta Aliyu Modibbo Umar, Mataimaki Na Musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ta Ɓangaren Ayyuka (Wakilin Mataimakin Shugaban Ƙasa (Babban Baƙo na Musamman).

Marubucin ya bayyana gaskiyar yadda aka riƙa samun wasu matsalolin tsaro na daban, waɗanda suka haɗa da satar mutane domin amsar kuɗin fansa, faɗace-faɗace masu nasaba da ƙabilanci ko yanki – wasu daga waɗannan matsalolin dama can akwai su, tun kafin bayyanar matsalar Boko Haram, wadda ta rikiɗe zuwa tayar da ƙayar baya.

√ Abubuwan Da Suka Haddasa Matsalolin Tsaro

Marubucin littafin ya gano tare da zayyano abubuwan da suka haddasa matsalolin tsaro a faɗin ƙasar nan. Wasu daga cikinsu sun haɗa da rashin kyakkyawan shugabanci, wasu matsalolin tun zamanin ’yan mulkin mallaka suke da kuma rashin ɗaukar matakan da suka dace tun daga tushe, domin magance matsalolin tun suna ƙanana. Rashin kyakkyawan shugabanci ya bayyana ta hanyar samuwar almundahana da dukiyar al’umma. An samu zarge-zarge masu yawa da suke nuna cewa, a sakamakon wawure dukiyar al’umma da wasu jami’an gwamnati suka yi, sun gina manyan gidaje a ƙasashen waje kuma sun mallaki jiragen sama na ƙashin kansu.

Wasu daga cikin abubuwan da suka haddasa tare da ta’azzara matsalolin ta’addanci, tada ƙayar baya da satar mutane domin amsar kuɗin fansa sun haɗa da:

– Miyagun Ƙwayoyi.
– Shiga Cikin Ƙungiyoyin Ta’addanci.
– Ɗabi’ar Taurin Kai.
– Bindigogi Da Safarar Mutane.
– Al’adar Tsanar Mutane.
– Addini.
– Ɗaukar Fansa.
– Aƙida.
– Talauci wanda ke samuwa saboda rashin ayyukan yi.
– Jahilci.
– Rashin Muhalli.
– Almundahana/Rashawa saboda rashin kyakkyawan shugabanci da rashin ƙarfin hali da niyyar kawar da su daga cikin al’umma.
– Hannun Ƙasashen Waje.

Marubucin dai ya amince da cewa ba za a ɗora wa talauci laifi kacokan ba, a matsayin abin da ya haddasa ayyukan ta’addanci. Ya bayar da wasu misalai da wasu sassan duniya, inda wasu mutane ke tsunduma cikin ayyukan ta’addanci domin kare aƙidojin addini. Amma duk da haka, talauci, rashin aikin yi da jahilci suna ta’azzara matsin rayuwa ga mutane, wanda hakan zai sa mutum ya kai kansa cikin ƙungiyar ta’addanci ko ta satar mutane domin amsar kuɗin fansa. Babu shakka ana samun wasu da akan tursasa su, su shiga cikin ƙungiyoyin ba da son ransu ba, kamar dai yadda ƙungiyar Boko Haram ke yi.

√ Batun Hannun Ƙasashen Waje A Al’amarin

Ga al’amura biyu da marubucin littafin nan ya tattauna dangane da batun hannun ƙasashen waje a ayyukan ƙungiyar Boko Haram: Mahangar ƙungiyar Boko Haram da mahangar Gwamnatin Najeriya. Dangane da mahangar ƙungiyar Boko Haram, akwai gamsassun hujjoji da shaidun da suka nuna cewa lallai akwai hannun ƙasashen waje cikin al’amarin, musamman saboda la’akari da wasu jawaban shugabannin ƙungiyar da ke tabbatar da haka. Haka kuma akwai bayanan bidiyo da ke nuna cewa lallai ƙungiyar Boko Haram tana da alaƙa da wasu ƙungiyoyi irinta da ke ƙasashen waje da suke samun tallafi daga gare su, musamman ta fuskar kayan aiki, kuɗin gudanarwa da kayan horarwa. Irin yadda aka riƙa samun tambari da yanayin wuraren da suke gudanar da al’amuransu, tabbas suna nuna alamomin cewa akwai hannun wasu ƙasashe a cikin al’amarin.

Idan aka dubi al’amarin ta mahangar Gwamnatin Najeriya kuwa, akwai mabambantan tallafin da ake samu daga ƙasashen waje. Akwai batun matakan kwantar da hankali daga Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyoyin gwamnatocin nahiyoyi, waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Haɗa Kan Afirka Gabaɗaya da Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma da sauran ƙungiyoyin bayar da tallafi da ma ɗaiɗaikun mutane. Gwamnati ta riƙa yin ɗari-ɗari da wasu tallafin, inda take zargin cewa akwai wata ɓoyayyar manufa a tattare da su. Wasu ƙungiyoyin na ƙasashen waje, sun fi mayar da hankali wajen suka da yin Allah wadai da yanayin ayyukan sojojin Najeriya, ba tare da suna yin la’akari da munanan ayyukan da masu tada ƙayar bayan suke aikatawa ba. Ta ɓangaren makamai kuwa, wasu ƙasashen sun riƙa jan ƙafa da laƙaƙi wajen sayar wa Najeriya irin waɗannan kayayyakin domin sojojinta. Sukan buƙaci Najeriya ta fara biyan kuɗin makaman tun kafin a ba ta su kuma wasu lokutan, ko da ta cika sharuɗɗan, akan yi jinkirin miƙa mata makaman da ta saya, duk dai domin samar da zagon ƙasa kan ayyukan yaƙi da masu tada ƙayar bayan. Wasu lokutan kuma, ƙiri-da-muzu ƙasashen za su ƙi miƙa wa Najeriya makaman, sannan kuma su shawarci wasu ƙasashe da cewa kada su sake su sayar mata da makamai. Wani abin mamaki ma shi ne, yawancin ƙasashen da ke nuna wa Najeriya wannan halayya, a lokacin da take tsananin buƙata, ƙawayenta ne, wasu ma abokan hulɗarta ne. A can baya ma, irin haka waɗannan ƙasashen suka riƙa nuna wa Najeriya, a lokacin da take cikin Yaƙin Haɗin Kan Ƙasa.

A wannan gaɓa, ina ba Najeriya shawara da babbar murya, cewa madamar tana son ɗorewa, a matsayinta na cikakkar ƙasa mai ’yanci, to dole sai ta dawo daga rakiyar ƙawance da munafukan ƙasashe masu fuska biyu, sai ta daina dogaro da su. Haka kuma sai ta jajirce ta mayar da hankali wajen bunƙasa masana’antar ƙera makamai ta ƙashin kanta. Wannan al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, don haka lallai ne a mayar da hankali a wannan ɓangare domin tabbatar da shi. Lallai ne a ɗauki wannan mataki yanzu-yanzu, tare da ƙaƙƙarfar niyya. Ƙasar nan fa tana da dukkan wadatar da za ta iya yin haka. Akwai ma wasu ƙasashen da ke cikin takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya da sauransu amma suka yunƙura suka kafa masana’antun ƙera makamai. Hakan ya sanya sun sama wa kansu mutunci, domin sun yi maganin azzaluman ƙasashen da ke neman kassara su. Ya kamata Najeriya ta yi koyi da irin waɗannan ƙasashen, ta yi hanzarin bunƙasa masana’antar makamai cikin gaugawa.

Marubucin littafin nan ya kula da wani abu, cewa Gwamnatin Najeriya ba ta matsa ƙaimi wajen neman tallafi daga ƙasashen duniya ba, wajen yaƙi da masu tada ƙayar ba, musamman ƙasashe na nesa da ita. A Yaƙin Basasa, na neman haɗin kan ƙasa, abu ne mai kyau Najeriya ta nesanta daga neman taimako daga manyan ƙasashe na nesa da ita. Amma duk da haka, ganin cewa a wannan zamani da duniya ta zama tamkar gidan kowa, inda ba a daraja iyakokin juna, ƙasa ba ta buƙatar cewa sai ta aika goron gayyata ga dakarun ƙasashen waje. Idan aka yi haka, suna iya hargitsa lamari, kodayake su ma abin ya shafe su ta wata fuskar. Ba lallai ne sai dakarun sun shigo Najeriya a zahiri ba. Abin lura ma shi ne, a wannan zamani na ci gaban kimiyya, ba lallai ne sai an gwabza yaƙi gaba-da-gaba ba da makamai na zahiri. Marubucin nan ya bayyana cewa a duba da hargitsi ya tashi a Nahiyar Turai, hankanlin wasu ƙasashen duk sun koma kan inda kadarinsu ya fi taɓuwa.

Marubucin littafin ya ƙarƙare da cewa, a yayin da ƙoƙarin gwamnati ya gaza magance matsalolin na tsaro tun daga tushensu, tallafin ƙasashen waje ba zai samu ba ta hanyar tsammani da kyautata zato, musamman ma ganin cewa matsalar Boko Haram da sauran matsalolin tsaro da ke fuskantar Najeriya, sun samu ne a sakamakon rashin kyawun shugabanci, kamar yadda aka bayyana a can baya.

√ Hanyoyin Magance Matsalolin

A taƙaice, marubucin littafin ya samar da wasu shawarwari domin magance matsalolin tsaro a ƙasar nan. Ya bayyana cewa, maganin matsalolin ta’addanci da masu tada ƙayar baya yana nan a ‘cikin gida’ kuma a hannun gwamnati, wacce ita ya kamata ta tunkari magance matsalolin tun daga tushensu. Ya bayyana cewa, duk da cewa ba laifi ba ne a nemi tallafi daga waje, amma ya buƙaci gwamnati da ta samar da ƙuduri mai tasiri ga matasa, ta magance almundahana da hanci da rashawa, a riƙa tantance kowane aiki a kowane ofis domin samar da komai bisa dacewa da kuma tabbatar da ana yin gaskiya da adalci da kuma bai wa kowa haƙƙinsa a yayin gudanar da mulkin ƙasa. Dukkan waɗannan matakai, ba za su samu ba sai an samar da ƙaƙƙarfar gwamnati, mai ƙarfin zuciyar samar da mulki nagartacce. Haka kuma sai an samar da turba mai kyau, wajen samar da nagartattu kuma amintattun zaɓuɓɓukan kujerun mulki. Ya kuma jaddada tare da amincewa da Tsari da Ƙudirin Ƙasa, wanda ya tanadi cewa samar da tsaro shi ne ƙashin bayan bunƙasa da ci gaban ƙasa kuma shi ne ke tabbatar da zaman lafiya da walwala da farin ciki ga ’yan ƙasa. Ko a cikin Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa, an zayyana dalla-dalla, cewa samar da tsaro da jin daɗi da walwalar al’umma, su ne babban ayukan gwamnati.

√ Hanyoyin Samun Dubaru Da Shawarwari

Zan iya tunowa a wasu shekaru can da suka gabata, wata mata mai suna Maria Sokenu, ta zo daga Bankin Wema ta gana da Cif SO Falae, lokacin shi ne Babban Sakataran Gwamnatin Tarayya, a ofis ɗinsa da ke fadar Shugaban Ƙasa da ke Unguwar Tafawa Ɓalewa Square, Legas. A gabana wannan ganawa ta gudana. Babban dalilin zuwan nata shi ne, ta kawo shawarar cewa ya kamata a kafa wani banki shigen bankin ‘grameen bank’ da ke ƙasar Bangladesh. Kuma wannan shawara ta samu amincewa karɓuwa sosai ga shugabanni. Daga farko, an buƙaci a sanya wa bankin suna ‘Bankin Talakawa’ amma sai aka ƙi amincewa, daga bisani aka amince a kira shi da sunan ‘Bankin Al’umma.’ Cikin ƙanƙanen lokaci aka kafa bankin farko a Ajegunle, kafin daga bisani aka ci gaba da kafawa a sauran sassan Najeriya. Wannan banki ne ya yi ta rikiɗa, har zuwa yanzu da ake kiran shi da sunan ‘Bankin Yanki’ ko ‘Banki Mai Gajeren Zango.’ Abin fahimta a nan shi ne, za a iya bijiro wa gwamnati da hikima, dubara ko shawarar ci gaban ƙasa daga ko’ina ne.

Marubucin ya sadaukar da lokacinsa sosai wajen rubuta littafin nan, bayan ya gudanar da bincike da nazari mai yawa. Daga yadda ya tsara littafin, manuniya ce da ke tabbatar da cewa ya naƙalci abin da yake bayyanawa. Saboda haka, ya kamata masu riƙe da ragamar mulki su duba shawarwarin da ke cikin littafin nan, domin ganin yadda za a ɗabbaƙa su wajen bunƙasa al’amuran tsaro a ƙasar nan.

√ Malami Abin Koyi

AY Shehu, marubucin littafin nan ya daraja ni, inda ya kira ni da cewa ni ne Malaminsa da yake koyi da ni. Gaskiya ne cewa mun yi aiki tare da shi kuma mun mu’amalanci juna a Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya. Mun ci gaba da mu’amala da zumunci da juna har zuwa yau ɗin nan. Zan iya cewa wataƙila a yayin mu’amalata da shi, ya ƙaru da wasu hikimomi amma idan ba haka ba, ai shi ma malami ne. Mutum ne shi mai ƙoƙarin nazari da neman ilimi, domin kuwa ya ɗabbaƙa koyarwar addininsa da ke cewa mutum ya tashi ya nemi ilimi koda zuwa ƙasar Sin (China) ce. Lallai kam ya je China amma ba kai tsaye ba, domin kuwa ƙasar Hong Kong ya je, wacce daga baya ta koma zuwa China, inda ya yi karatun digirin digirgir (PhD). Ya shiga aikin koyarwa, inda har ya kai matakin Farfesa. Ni kuwa ban kai nan ba. Ya kasance hamshaƙin ma’aikacin gwamnati na kasa-da-ƙasa, inda ya yi musharaƙa da shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma daban-daban. Ni kuwa ban samu irin wannan dama da muƙami ba. Ya kuma taɓa wakiltar Najeriya a hulɗar jakadanci ta ƙololuwa, inda ya yi aiki a ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya. A yayin gudanar da aikinsa, ya samu fahimta da gogewa da wayewa matuƙa. Baya ga waɗannan littattafai biyu da aka ƙaddamar a yau, inda ya buƙaci in yi sharhi a kan ɗaya daga cikinsu, ya kuma rubuta wasu da dama. Kuma ina da yaƙinin nan gaba ma za a sake jin ɗuriyar wasu sababbin littattafan nasa. Babu shakka ya share hanya ga ma’aikatan gwamnati tsofaffi da masu ci a yanzu, da ma dukkan ’yan Najeriya, su yi koyi da shi, su ma su biyo bayansa. Ta haka ne za a samar da dubaru da hikimomi da shawarwari nagartattu, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa ƙasarmu, abin ƙaunarmu, ta yadda al’ummar da za ta gaje mu za ta yi alfahari da mu.

A nan zan gabatar maku da ɗalibi, wanda ya zarce malaminsa ƙwazo ta fuskoki da dama. Ina miƙa masa godiya mai yawa bisa ga karrama ni da ya yi. Ina roƙon Allah Ya ba shi tsawon rai da ingantattar lafiya da basira, domin ya ci gaba da amfanar al’umma da iliminsa domin inganta Najeriya da al’umma gaba ɗaya.

Ina miƙa godiya ga kowa da kowa.

________
Bukar Usman, OON, tsohon Babban Sakatare ne a Fadar Shugaban Ƙasa kuma a yanzu shi ne Shugaban Ƙungiyar Kula Da Bunƙasa Fasaha Da Hikimomin Al’umma ta Najeriya (Nigerian Folklore Society).

Previous Post

‎Reno Omokri: My Understanding of Islam

Next Post

The Soul of Bukar Usman

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
The Soul of Bukar Usman

The Soul of Bukar Usman

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

November 17, 2025
Hararar Baba Ganduje

Hararar Baba Ganduje

June 29, 2023
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Katsina Governor Inaugurates Committees to Distribute Palliative

September 27, 2023
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

November 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.