Buthelezi Ɗan Kishin Ƙasa Ya yi Bankwana Da Duniya
Daga Hamadani Buba
Shahararren ɗan kishin ƙasar nan na Afrika ta Kudu, Mongusuthu Buthelezi ya yi bankwana da duniya a yau Asabar, bayan ya kwashe lokaci a gadon jinya.
Mai shekara 95, Buthelezi ɗan ƙabilar Zulu, ya yi gwagwarmayar neman ‘yancin al’ummarsa daga Turawan mulkin mallaka da masu nuna wariyar launi na ga baƙaƙen fata.
Kafin mutuwar tasa, ya kasance jagoran Jam’iyyar Inkatha Freedom Party na tsawon lokacin yaƙi da wariya har zuwa mutuwarsa.
Ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Afrika ta Kudu da bai canza tsarin rayuwarsa daga al’adu da tarbiyya ta gida da ya samu don burge Turawa ba
Ya yi fama da ‘yan siyasa da Turawan ƙasarsa da neman hana cin zarafin baƙaƙe.
Za daɗe ana tuna shi, kamar dai yadda ake tunawa da magabacinsa, marigayi Nelson Mandela, a fagen kishin ƙasa da yaƙi da wariyar launin fata.













