• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, April 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 19, 2023
in Sarauta
0
KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

KWATAM HUBA, Hajiya Halima Ahmad Tahir

170
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

~~~~~~~

Related posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025

Hajiya Halima Tahir fitacciyar ‘yar jarida ce, musamman ta fuskar rediyo da talabijin. Haka kuma ita Basarakiya ce, kasancewar tana ɗaya daga cikin masu riƙe da Sarautun Gargajiya a Masarautar Hong da ke Jihar Adamawa. Ita ce KWATAM HUBA. A tattaunawar ta da Bashir Yahuza Malumfashi, ta bayyana tarihinta da irin gwagwarmayar da ta sha a fagen aiki, kamar kuma yadda ta yi cikakken bayani game da sarautarta ta KWATAM, da tasirinta a Masarautun Gargajiya a Nigeria. Ta taɓo al’amuran yau da kullum, musamman ƙuncin rayuwa da ake ci, sannan ta ba da shawarwarin yadda gwamnatoci da attajirai za su fitar da jaki daga duma. A matsayinta na mace Uwargida kuma, ta ba magidanta maza da mata shawarwarin yadda za su zauna da iyalansu lafiya da haƙuri. Lallai ne ku karanta wannan ‘Bunƙasasshiyar Tattaunawa’ ta Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya, a cikin Taskar Gizago:
~~~~~~~

Hajiya Halima Ahmad Tahir

 

Hajiya Halima tare da mijinta

TG: Kina ɗaya daga fitattun mata ‘yan jarida a Arewa. Ko za ki bayyana mana tarihinki a taƙaice?

HAJIYA HALIMA: Assalamu alaikum. Sunana Halima Ahmad Tahir (Kwatam Huba). An haife ni ne a Unguwar Nassarawa ‘Yan Shanu, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato, a ranar 26-8-1976. Asalina, ni ‘yar ƙabilar Kilba ce daga Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Mahaifina ne ya dawo Jos, sakamakon hada-hadar kasuwanci. A nan Kuma aka haife ni tare da ‘yan uwana maza da mata, yayye da ƙanne mu 25 ya haifa (maza 12, mata 13).

Na yi karatun Firamare a ECAN Primary School Chwelyap Jos. Bayan na kammala sai na tafi Ibrahim Memorial Secondary School, inda na fara karatun sakandare matakin farko (JSS). Bayan na kammala aji uku, sai aka yi mani aure. Daga nan na koma karatu a Muslim Community Education Center. A nan na kammala karatun sakandare, inda daga nan na je Jami’ar Jos Gangare Campus.

A nan na yi karatun Diploma a Fannin Aikin Jarida (Mass Communication). Daga nan na koma Makarantar Horon ‘Yan Jarida (NTA College), inda na yi karatun Satifiket da Diploma a Fanin Aikin Talabijin ( TV Journalism). Sannan na koma makarantar koyon kwamfuta, mai suna Credac. A nan na yi karatun Diploma in Computer Science. Daga nan sai na samu aikin wucin-gadi a Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA, Jos).

Ban daɗe da fara aiki a wajen ba, na samu wani aikin a Kamfanin Dillancin Labarai na Rediyo da Talabijin na Daar communications Plc, AIT/Raypower, inda suka ɗauke ni a matsayin mai gabatar da shirye-shirye a talabijin. Ina aikin sai kamfanin ya ba ni dama in je in ƙaro ilimi. Sai na sake komawa karatu a TV Collage, inda na yi karatun digiri a fannin Aikin Jarida (Bsc. Mass Communication), ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Bayan na koma, na ci gaba da aiki a matsayin mai gabatarwa a talabijin da rediyo na tsawon lokaci. Daga nan sai na koma Sashin Labarai (News Production), inda na fara rubuta labarai da fassara daga Turanci zuwa Hausa. Hakazalika, ina tace labarai (news editor), sannan ina karanta labarun Turanci ( newscaster) da na Hausa. Sai da aka wayi gari ni kaɗai ce a wannan lokacin nake rubuta labarun Turanci in fassara, sannan kuma in karanta, a lokaci guda kuma ina gabatar da shirye-shirye da dama; tun daga na siyasa, al’amurran yau da kullum da Kuma na addini, a rediyo da talabijin. Ina kuma harkar tallace-tallace a kamfanin.
Bayan wani lokaci ne kamfanin ya naɗa ni Shugabar Sashin Hausa, daga bisani kuma na zama Shugabar Kamfanin Reshen Jihar Bauchi. Daga nan kuma bayan na koma Abuja tare da mijina, na bar aiki a kamfanin; na koma na zama ‘yar Jarida Mai Zaman Kanta.

A batun iyali kuwa, ina da mijina Dokta Ibrahim Bello Dauda. Allah kuma Ya albarkace ni da ‘ya’ya shida, guda huɗu maza da mata biyu. (Ina da ‘yan uku a cikisu).

TG: Wane irin ƙalubale kike fuskanta a matsayinki na ‘yar jarida?

HAJIYA HALIMA: Gaskiya Alhamdu lillah. Ba zan iya cewa na fuskanci wani ƙalubale na a zo a gani a aikin jarida ba. Ka san aikin jarida ya sha banban da kowane irin aiki saboda aiki ne da babu ruwansa da jinsin mutum ko ƙabila ko addini balle ɓangaranci. Aiki ne da ya tsaya a kan gaskiya da amana. Saboda ɗan jarida jakada ne na wanzar da zaman lafiya da kuma fayyace gaskiya komai ɗacinta. Shi ya sa mutane da dama suke ganin ɗan jarida kamar malaman addini wajan faɗar gaskiya. Misali, za ka ga ko mutane na musu a kan wani labari, sai ka ji da zarar wani ya ce ai na ji labarin a kafafen yaɗa labarai ne, sai a yarda. Kuma na yi aiki ne a wajen da kusan kashi 99 na ma’aikatan wajen ba addinina ɗaya da su ba. Kuma a garin da yake da tarihi wajen rikicin addini da na ƙabilanci amma wannan bai sa na fuskanci tsangwama ko wata barazana ba.

Sannan na yi sa’a saboda al’ummata, musamman malaman addini sun yi mun ƙoƙari sosai wajen ba ni haɗin kai da ƙwarin gwiwa a lokacin da nake aiki kuma sun ba ni ayyuka da dama waɗanda su ne kusan kashi 60% wajen bayar da gudumawar da ta sa tashar ta bunƙasa a wannan lokacin. Akwai ƙananan abubuwa da suka faru, a wasu lokuta inda ta kai ga mutum ya fuskanci barazanar rasa ransa amma wannan bai taɓa sa na karaya ko kuma na ja baya ba. hasali ma dai ya ƙara mani ƙarfin gwiwa ne saboda a matsayina na Musulma, na dogara ga Allah kuma na san ya isar mani. Saboda haka a gani na, babu wata matsala da na fuskanta. Wataƙila ina da sa’a ne. (Dariya).

TG: Waɗanne nasarori kika samu a aikinki na jarida?

HAJIYA HALIMA: Gaskiya Alhamdulillah saboda ka san an ce sabo da maza jari. Yana daga cikin nasarorin da na samu, bayan sanin aikin jarida shi kansa, na samu damar yin mu’amula da mutane daban-daban, daga kuma matakai daban-daban da suka haɗa da shugabannin ƙasashen, attajiri da kuma talakawa. Na kuma yi amfani da damar da na samu wajen tabbatar da an tabbatar da adalci da gaskiya ta wajen tabbatar da an yi adalci ga waɗanda aka zalunta. Na Kuma samu damar tallafa wa musamman marayu da marasa galihu, wajen inganta rayuwar su. Babu abin da yake mun daɗi, kamar in ga na sa farin ciki a fuskar mabuƙata. Gaskiya, Alhamdu lillah, na smu dama ta hanyar aikin jarida.

TG: A matsayinki na Basarakiya mai rike da Sarautar Kwatam Huba, ko za ki yi mana bayani game wannan sarauta da kuma gidan sarautar da ta naɗa ki?da sarautarki ta gargajiya?

HAJIYA HALIMA: Gidan Sarautar Hong, gida ne mai ɗinbin tarihi cikin Sarautun Gargajiya da ke Jihar Adamawa ko kuma in ce a Nigeria baki ɗaya. An fara Sarautar Hong a ƙasar Kilba, a garin Hong da ke jithar Adamawa ta Tsakiya tun Hijira na da shekara 1356. Yau sarautar na da shekaru 659 tun kafin Zuwan Turawan Mulkin Mallaka.

Sarautar KWATAM, sarauta ce mai dubun tarihi, tun kafuwar Masarautar Kilba. Sarauta ce mai matuƙar daraja da girma da kuma muhimmanci a ƙasar ta Kilba, Sarauta ce da ba kowacce ake bai wa ba, sai fitar Sarki, ‘yar starki, ƙanwar Sarki ko matar Sarki. Sarauta ce ta ‘ya’yan jinin sarauta. Ba sarauta ce da ake bai wa kowa ba.

Sarautar Kwatam na nufin Uwar Al’ummar Kilba baki ɗaya. Ma’ana, duk wani ɗan al’ummar Kilba da ke duniya, Kwatam ita ce uwarsu.

Kasacewata jinin sarauta, Allah Ya zaɓe ni, aka naɗa ni Kwatam a ranar 6-4-2022, bayan an shafe shekaru da dama da rasuwar Kwatam ɗin da ke riƙe da sarautar tun 2009; kusan shekaru 12 da suke wuce ke nan, ba tare da an sake naɗa wata mace a kan sarautar ba.

TG: A matsayinki na mace mai ilimi, wace shawara za ki ba magidanta maza da mata, domin ganin ana samun fahimtar juna da rage sake-saken aure a cikin al’ummarmu?

HAJIYA HALIMA: Shawarar da zan bai wa ma’aurata ba komai ba ce, illa maganar nan da iyaye da kakanni suka saba faɗa, cewa a yi haƙuri da juna. A koyaushe na samu kaina a wajen da zan bai wa ma’aurata shawara, nakan ce masu idan abokin zama namiji ko mace suka yi aure; idan a cikin kashi uku na halayen miji ko mata, idan kashi biyu suna da kyau, to a yi haƙuri da mara kyan. Domin kai ko ita ma akwai wani halin da abokin zaman ke da shi ma, wanda ake haƙuri da shi. Sannan kuma babbar matsalar da ake fuskanta a auren zamanin nan ita ce, ba a aure don Allah. Ana aure ne don wasu buƙatu na son zuciya. Saboda idan ka duba zamanin nan, za ka ga yau Idan mutum zai fito neman auren yar mutane Idan har Allah ya sa yana da rufin asiri za ka ga daga iyayen har ‘yar babu ruwansu da halayensa ko ɗabi’unsa ko addininsa. Abin da zai ba ka mamaki, ita ma yarinyar in da za a tambaye ta, ita ma za ta ce tana so koda ba ta san daga inda ya fito ba. Saboda yanzu aure ake don abin duniya. Mata na gudun talauci, sun fi son wanda zai saya masu mota, ya sa ta a fankamemen gida, ga danƙwaleliyar mota; tana ta fita ƙasahsan waje. To irin wannan mijin ko yankar kai yake za a aure shi. Iyaka a ce hassada ake masa don Allah yta rufa masa asiri. Ko da daga baya an gane, sai iyayen su tilasta wa ɗiyarsu zaman gidan, matuƙar suna samun biyan buƙata.

Mata yanzu sun fi son abin da suke kira “Ready Made.” To miji ne ya san ana son shi ne don abin hannunsa. Ya san idan babu wannan abin ba za a zauna ba, dole ko ka ga ya yi wulaƙanci, tun da a zamanin nan mata na iya kashe mazajensu, uban ‘ya’yansu don su mallaki abin da ya tara. Mun ga irin haka da dama, a matsayina na ‘yar jarida. A wani ɓangaren kuma rashin tarbiya ne da kuma rashin sanin haƙƙin auren shi kansa, shi ke jawo taɓarɓarewar aure.

To, koma dai mene ne, ya kamata ma’aurata, su san cewa aure ibada ne mai zaman kansa. Mace ta kalli miji a matsayinsa na mabuɗin shigar ta aljanna. Hakazalika shi ma mijin, ya yi iya yin sa wajen kula da haƙƙoƙin matarsa. Ya sani cewa kada ya yi sake da haƙƙin auren, idan ba haka ba zai iya zama sanadin shigar sa wuta.

Allah (swt) Ya ce zai tambaye ku a kan abin da Ya ba ku kiwo. Mata su tuna cewa aure ba kasuwanci ba ne, ibada ce. Ka da su bari zuciya da son abin duniya ya ruɗe su. Maza kada ku hana matanku su koyi sana’a, don yanzu duniya ta canza, sai da taimakekeniya. Duk abin da za mu tara, a nan za mu bar shi. To me zai sa mutum ya shagaltu da duniya, ya manta da lahira? Me ya yi zafi haka?

Ma’aurata a mutunta juna, a girmama juna, a girmama iyayen juna, ku zama abokan hira da shawara da junanku. A cire ƙyashi da hassada ga juna, a yi haƙuri da rayuwa, sai a zauna lafiya.

TG: Ana fuskantar wani yanayi na matsalolin rayuwa a ƙasar nan. Wace shawara za ki ba gwamnati da attajirai, wajen rage raɗaɗin da ake ciki?

HAJIYA HALIMA: A nan kam abu na farko, zan fara da cewa innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Domin al’umma na cikin jarrabawa kuma wannan bulaliyar kan hanya ce, ba ta bar kowa ba; talaka da attajiri, babban ko yaro. Haƙiƙa, ƙasarmu na cikin mawuyacin hali na ƙaƙanikayi, wanda idan ba wani matakin gaggawa gwamnati ta ɗauka ba, Allah kaɗai Ya san halin da al’ummar ƙasarmu za su kasance nan gaba kaɗan, ko in ce ma an riga an shiga.

Gaskiya ne ana fuskantar yanayi na matsanancin talauci da wahalhalu bisa abin da ya shafi tattalin arziƙi da kuma gudanar da rayuwa a Nigeria da akasarin jama’a ke ciki. Matakan da nake ganin Gwamnatin Tarayya da na jihohi da kuma ƙananan hukumomi ya kamata su ɗauka su ne, da farko dai dole Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Nigeria (CBN) su ɗau matakin daidaita darajar Naira a bisa Dala. Soboda matuƙar darajar Naira ba ta daidaita ba a bisa Dalar Amurka ba, zai yi matuƙar wuya duk ko da waɗanne irin matakan da za a ɗauka su yi tasiri.
Dalili kuwa shi ne, mafi yawan abubuwan da ake amfani da su a kamfanoni, shigowa da su ake yi daga ƙasashen ƙetare. Sannan man fetur har yanzu shigowa ake yi da shi daga ƙasashen waje. Don har yanzu matatun man fetur da muke da su a Nageria ba su aiki. Don haka buƙatar Dalar Amurka ta yi yawa, ta yadda shi Babban Bankin Nigeria ba zai iya samar wa masu shigowa da kayayyaki daga ƙasashen waje isassar Dala ba. Wannan ya sa Dalar ta yi matuƙar tsada kuma hakan ya sa duk abin da ya dogara da sai an sayo da Dala, ya yi matuƙar tsada. Misali, farashin mota ya tashi saboda man fetur ya tashi, don an cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

Na biyu, sai kuma gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta noman damina da na rani, ta hanyar ba da tallafi na musamman a ɓangaren ba da iri, takin zamani, magungunan ƙwari da tarakatocin noma da dai shauransu.

Na uku, waɗannan za su biyo bayan matakai ne na dogon zango (Long Term Plan). Amma a yanzu dole ne gwamnati ta ba da tallafi na gaggawa, ta ɓangaren buɗe rumbunar ajiyar hatsi don raba wa mutane. Domin yunwa da tsadar kayayyaki su ne manyan matsalolin da suka addabi al’ummar Nigeria fiye da komai a yanzu.

Na huɗu, bayan haka sai tallafi ga mata da matasa, ta wajen samar musu sana’o’i daban-daban da kuma samar musu jari da kayan sana ‘a da ba su rance marar kuɗin ruwa ko kuma ta wurin ba su kayan aiki.

Na biyar, sannan gwamnati ta bayar da ilimi da lafiya kyauta, ta hanyar inganta ƙananan asibitocin gwamnati da manyan da kuma inganta makarantun gwamnati; ta yadda ɗan talaka zai samu ilimi kyauta. Ina ganin idan gwamnati za ta yi amfani da waɗannan shawarwari, to za a samu sauƙi matuƙa, in sha Allah.

A ɗaya ɓangaren kuma, su kuma attajirai, kamata ya yi su haɗa kai da gwamnati wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ba da tallafi na musamman ta fannin ba da tallafi ga al’umma. Da yawansu suna da gidauniya ta taimako. Za su iya ƙara yawan kuɗaɗen tallafi da suke ware wa ƙungiyoyin nasu domin ba da waɗannan tallafin gaggawa ga al’umma. Haka kuma ina kira gare su da su daure wajen buɗe kamfanoni da masana’antu a cikin gida Nigeria don matasa su samu aikin yi. Idan gwamnati da attajirai suka yi haka, da yardar Allah za a samu mafita.
~~~~~~~

Previous Post

AUREN ‘YA’YAN YUSUF DINGYAƊI: Saƙon Godiya Da Ban Gajiya

Next Post

GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

Related Posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa
Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’
Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
Next Post
GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

My Takeaways from IBB’s Autobiography

Muhimman Batutuwan Dubawa A Littafin Tarihin IBB

April 3, 2025
General Aliyu Commends Nigerian Army Depot for Relentless and Continuos Excellence

General Aliyu Commends Nigerian Army Depot for Relentless and Continuos Excellence

March 4, 2024
REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

August 21, 2023
Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

June 22, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
  • MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.