• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

Binta Tukur by Binta Tukur
August 12, 2023
in Babban Labari
2

Zainab Ahmad, Jarumar Kaduna

183
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

~~~~~~~
Hajiya Zainab Ahmad, wacce ake wa laƙabi da Bint Hijazi Jarumar Kaduna, mace ce jajirtatta, mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum, mai tallafa wa al’umma kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam. BINTA TUKUR ta tattauna da ita, musamman kan al’amuran da ake ciki a ƙasar nan na ƙuncin rayuwa da kuma matsalar juyin mulki a Nijar. Haka kuma ta yi magana game da masu cin zarafin mutane, musamman mata a soshalmediya. Ga yadda tattaunawar ta gudana:

Related posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026

~~~~~~~

Zainab Ahmad, Bint Hijazi

TG: Da farko za mu fara da gabatarwa. Shin wace ce Zainab Ahmad?

ZAINAB AHMAD: Ina yi wa kowa sallama irin ta addinin Musulunci. Assalamu alaikum wa rahmatullahi, wa barakatuhu. To da farko kamar yadda kika sani, sunana Zainab Ahmad, wadda aka fi sani da Bint Hizaji. An haife ni a Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara amma asalin mahaifana Kanawa ne. Zama ne ya kai su can saboda aiki da aka tura mahaifina. Na fara karatun firamare a L.E.A Tudun Wada Gusau, kafin na koma Shekara, makarantar firamare ta kwana, ina ƙarama. To bayan an rufe Shekara kuma sai na koma Makarantar Ibrahim Gusau, inda na ƙarasa firamare. Bayan nan na tafi makarantar ‘yan mata ta Kabo, Jihar Kano, inda na yi Ƙaramar Sakandare, sannan na wuce Taura, inda na yi Babbar Sakandare. Da na gama Taura sai aka yi min aure. Daga nan na ci gaba da karatu a FCE Kano, inda na yi Advance Diploma. A yanzu kuma ina karatu a Jami’ar Jihar Nassarawa da ke Keffi, inda nake ƙoƙarin haɗa takarduna na gaba.

TG: A matsayinki na mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum, me za ki ce game da yanayin da al’ummar Najeriya suka wuto a shekara 8 na mulkin Baba Buhari?

ZAINAB AHMAD: Abin da zan faɗa a kan shekaru takwas da suka wuce, watau abu ne da nake masa kallo ta fuskoki daban-daban. A gaskiya sai in ce ba mu taɓa shiga tsanani da firgici da tashin hankali ba irin na shekaru takwas ɗin nan da suka wuce. Sai dai a duk yanayin da bawa ya samu kansa, dole ya gode wa Allah da Ya bar mu da ranmu da lafiyarmu har kuma muka iya cinye wannan jarabawa.

Mutanenmu na Arewa sun shiga jarabawai da yawa. Misali, a shekaru takwas da suka wuce ne wato ta’addanci ya fi yin ƙarfi a Arewa. A cikin shekaru takwas ɗin nan da suka wuce ne, Arewa ta samu kanta a cikin yunwa da talauci da fatara, duk da an ce in aka bi ta ɓarawo a bi ta mabi sawu, wani lokaci mu ma ba mu tausaya wa kanmu amma tabbas akwai yanayin da bawa in ya samu kansa, to sai dai a miƙa wa Ubangiji. Sannan a wannan lokacin ne muka ga yadda farashin kayan abinci suka fara tashin gwauron zabo. To duk komai dai yanayin da ƙasar nan take ciki a yau, ni gaskiya zan alaƙanta shi da shekarun takwas na bayan nan, saboda a cikin shekaru takwas ɗin nan ne duk wata taɓarɓarewa ta taɓarɓare a Arewa da ma ƙasar nan gaba ɗaya.

TG: Me za ki ce game da Juyin Mulki a Nijar da abin da ya biyo bayansa game da alaƙar Nijar da Najeriya?

ZAINAB AHMAD: Nijar da Nijeriya uwa ɗaya ce uba ɗaya, duk inda ka bi salsali, ka bi tarihi, ka bi komai, Nijar da Nijeriya ƙasa ɗaya ce, al’umma ɗaya. Don haka ni ban ga dalilin da zai sa a ce za a yaƙi Nijar ba, a kan abin da mutanen ƙasar nan sun fito sun nuna ra’ayinsu ne.

Ba yadda za a yi ka je ka tursasa wa mutum ya ɗauki abin da ba ya ra’ayi, tun da sun nuna abin da suke so ke nan ra’ayinsu ne; don mi za a je a yaƙe su? Ni fa abin da nake kallo, duk wanda ya ce a je a yaƙi Nijar, to kamar ana yaƙar Arewacin ƙasar nan ne. Da ma Arewa yanzu yaya muka ƙare balle an ɗauko mana yaƙi? Sakkwato na da iyaka da Nijar, Yobe na da iyaka da Nijar, Barno da Chadi da Katsina na da iyaka da Nijar.

To waɗannan mutanenmu ake so a tagayyara. A gaskiya ni ba ni goyon bayan wannan, a ƙyale mu da ‘yan uwanmu ‘yan Nijar. Muna son su suna son mu, muna ƙaunar su suna ƙaunar mu. A bar mu da zumuncinmu yadda muke. Ba mu yarda da wannan yaƙin ba, ba mu yarda da yaƙi ba gaskiya.

TG: Ta ɓangaren Ilimi, ɗaliban jami’a da sauran manyan makarantu suna kuka da sabon tsarin ƙarin kuɗin makaranta. Ko yaya kike ganin makomar talaka ta ɓangaren Ilimi a ƙasar nan?

ZAINAB AHMAD: Wato duk waɗannan tambayoyin da kike min duk yana daga cikin wannan abubuwan da na faɗa a baya na maganar cire tallafin mai ɗin nan. Ni ta wata sigar ma sai in ga kamar ko ba a son ɗan talaka ne ya yi karatu, tun da in ba ana neman a hana wa ‘ya’yan talakawa karatu ba, wannan kuɗin a ina ake tunanin za su samo su?

Ya ilahi talaka da me zai ji? Da kuɗin lantarkin da aka ƙara, aka ƙara, aka ƙara yadda ba kowa ma zai iya amfani da shi ba? Ko ɗan man da yanzu ya zama ɗan sarki, talaka ba zai iya siyen shi ba? Ko kuwa da ‘ya’yanka da ka tura makaranta kana neman ka ba su rayuwa mai kyau, aka zo aka ƙara kuɗin makaranta za ka ji? A’a ko kuwa da kuɗin abin da za ka ci ma yanzu da yake neman ya gagare ka za ka ji?

Gaskiya duk waɗannan abubuwan ni banga ta inda suka ƙari talaka ba. A dai koma a zauna a duba, a hanga a kuma tausaya wa bayin Allah, a kawo masu ɗauki.

TG: Ga shi kuma muna cikin wata na uku na sabuwar gwamnati, ko me za ki ce game da halin matsi da al’umma suke ciki, musamman dangane da tsadar fetur da kayan abinci?

ZAINAB AHMAD: To a gaskiya idan zan fito in yi magana ta Allah, wato wannan sabuwar gwamnatin ta zo wa talaka da uƙubobi kala-kala. Wato da ta fara ma da azaba ta taho mana kuma har yanzu ina mai tabbatar maki cewa hatta su manyan suna cikin yanayin da muke cewa jiki magayi. Tabbas talaƙa yana cikin ha’ula’in rayuwa. Yanzu ki dubi mai, Ya Ilahi ta ina ake tunanin talaka ya rayu?

A gaskiya ya kamata a wannan sabuwar gwamnatin ta fahimci cewa fa mulki fa sai akwai mutanen ma kake mulkar su. To in dai ba kashe mutane ake so a yi ba, ni ban ga abin da ake nema da talaka ba.

Yanzu talaka bai isa ya ci masara da ya saba siya yana ɗan lallaɓawa, yau a yi dambu, gobe a yi tuwo, jibi a yi mene ne da dawa; duk gaba ɗayansu yanzu fa sun fi ƙarfin talaka. To Ya Ilahi, ina ake so talaka ya sa kansa?

Gaskiya ina mai kira ga sababbin shugabanninmu da su dubi Allah. Idan ma maganar cewa wai tallafin mai ake yi, to ai sun san mutanen masu satar tallafin mai ɗin. Me zai hana a kama su saboda ragowar su ɗauki darasi? A kan wasu mutane ƙalilan za a ce wai mutane sama da miliyan ɗari biyu suna cikin ha’ula’i na rayuwa? Saboda wasu ƙalilan a kasa yadda za a yi da su? Gaskiya ni ina ganin wannan ba adalci ba ne. A kama mutanen nan da ake cewa suna karɓar tallafin mai ɗin nan dukkansu, gwamnati yanzu ta yi ba sani ba sabo. Duk wanda aka san yana kawo wa gwamnati cikas a ƙasar nan, to ya kamata lokaci ya yi da ya kamata su fara girbar abin da suka shuka. Amma ba zai yiwu saboda son zuciya a ce an saka mutane cikin irin wannan uƙubar ta rayuwa ba. Ni dai gaskiya a ganina, wannan shi ne ra’ayina.

TG: Kina daga cikin mutanen da ke shan kwaramniya a Soshalmidiya, inda har ma kika kai ƙarar wasu da suka ɓata maki suna. Ko za ki yi mana ƙarin bayani?

ZAINAB AHMAD: Lallai wannan babbar tambaya kika yi min kuma in Allah Ya yarda zan ba ki amsarta. Tabbas ina daga cikin mutanen da suka daɗe a soshiyalmidiya amma dai an rufe min saha ta ta farko-farko da na buɗe ta tun a shekarar 2007 ko 2008. To yanzu wannan sahar tawa sabuwa ce kuma ni a baya waɗancan sahar tawa gaskiya ni ban cika samun matsala da kowa ba saboda duk mabiyana muna mutunta juna. To amma abu ɗaya da na fahimta da soshiyalmidiya shi ne, mutane da yawa suna ganin kamar idan suka ci zarafin wani ko suka ci mutuncin mutum ta yanar gizo kamar ba a san ko su su waye ba ko kuma ba za a gane su ba. Wanda wannan ba haka ba ne, yanzu duniya ta ci gaba.

Duk lokacin da mutum ya aikata abu to sai idai idan an ga dama an ƙyale shi. To da farko dai na daɗe ina jan kunne a kan mutane da ke zuwa shafina, su ɗauki hotona suna amfani da shi, ba tare da izinina ba kuma na daɗe ina jan kunne a kan cewa a da dai an yi ta ci mana zarafi muna kawar da kai amma a yanzu duk wanda ya ci mana zarafi to ba za mu ƙyale shi ba. Gaskiya waɗannan yaran wato wulaƙancin da suka yi ya wuce hankali, ya kuma wuce yadda mutum zai iya ɗauka.

Da farko sun ɗauki hotona da na yaayana suka je suka kafa shi a shafukansu, suka yi rubuce-rubuce na ɓatanci da tozarci. To ni dai ba yarinya ba ce ƙarama, tun da ni ƙaramin ɗana ma, autana yanzu shekarunsa ashirin da bakwai. Ya Ilahi abin da ban yi a baya ba shi ne zan yi yanzu? Kuma idan ma siyasa ce, ni siyasarsu na shiga? Ni ban taɓa zuwa na zagi wanda suke cewa su yaransa ba ne ko wani abu.

Ban taɓa zagin wani ba, ba ni shiga hidimarsu balle a ce an ɗauke ni an yi amfani da wannan an ci zarafina babu dalili. Hotona ni da yayana ne kuma a taro ne, taron ma na zuri’armu ne ba wai na irin je ka na yi ka ɗin nan ba ne aka ɗauka. Suka ɗauki hoton nan suka dinga yi min cin mutunci, har ta kai ‘ya’yana na ganin cewa in ba su dama su ɗauki mataki a kan irin wannan. To idan ka ce za ka bar yara su yi hayaniyarsu ba za a samu abin da ake so ba. To a matsayina na ‘yar ƙasa mai haƙƙi, mai ‘yanci, mai dama sai na ga ni ba mahaukaciya ba ce da zan ɗauki doka a hannuna amma akwai gurbin shari’a, wanda shi na ɗauka kuma na kai su ƙara kotu a kan cin zarafina, ƙazafi, tozarci, ɓatanci da suka yi min a kafar Facebook nake kuma neman kotu ta bi min hakkina.

To Alhamdu lillahi, lokacin da na yi wannan kotu ta ba mu izinin mu saka a shoshalmidiya saboda a ankarar da su to da na yi hakan a ciki ma akwai abin da kotu ta bayar na gargaɗi, wanda ta ce kada wanda ya sake magana a kaina. To amma abin mamaki, da muka saka takardun nan na farko a cikinsu ma sai aka samu wanda suka je suka yi rubuce-rubuce cewa wai su za a yi wa barazanar banza, ba wata kotu, wannan ba kotu ba ce, duk burga ce. Ba irin zagin da ba su yi min ba, duk ina kallon su, ban ce masu komi ba. To dama Hausawa sun ce rana ba ta ƙarya sai dai uwar ‘ya ta ji kunya.

A lokacin da kotu ta ba mu rana ta shiga, to lokacin ne suka ga cewa da gaske ne abun, sannan aka fara kiraye-kirayen cewa a yi haƙuri, a yi waye, a yi waye, to amma wannan maganar ta riga ta wuce hannuna. Lokacin da ɗaya daga cikinsu ya roƙi a yi haƙuri ai an cire sunansa tun kafin abin ya yi nisa, amma yanzu waɗannan kam tabbas za mu gurfana da su a gaban ƙuliya. Za mu je, za mu ja, zan tsaya, don ina so ya zama izna ga masu niyyar cin mutunci ko cin zarafin wani a soshalmidiya.

Zan nemi haƙƙina kuma ko mutuwa na yi ‘ya’yana za su ci gaba da wannan shari’ar. Ba za mu bar ta ba, sai sun fito sun gaya min inda duk suka ga na aikata haka. A cikinsu ma akwai wanda ya ɗauki hoton ‘yar uwata da shi wanda suke cewa sun kare ɗin, har suka saka wani kaman kibiya da nuna wato mazantakar shi wancan.

To duk waɗannan suna daga cikin abubuwan. Wato ita mace duk wacce suke gani suna mata kallon mutuniyar banza ce ko ‘yar iska ce, ko wani abu, to gaskiya wannan shi ne dalilin da ya sa na ɗauki wannan matakin kuma ina fata ranar 15 ga wannan wata da za mu halacci kotu, zan so a ce “Taskar Gizago” kuna nan a tare da mu, don a sanar wa mutane yadda ta kaya. Na gode.
~~~~~~~

Previous Post

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Next Post

Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Related Posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi
Babban Labari

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
Next Post
Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Comments 2

  1. ladidis weahave says:
    3 years ago

    gaskiya naji dadin wannan hira
    Allah yakara tsareki daga wadannan yara marasa kunya Binta hijazi

    Reply
  2. Bashir Yahuza Malumfashi says:
    3 years ago

    Haka ne kam.. Muna godiya.

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

September 22, 2023
GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

August 20, 2023
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

November 10, 2023
GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

September 6, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.