• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 11, 2023
in Addini
0
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Liman, a yayin gabatar da huɗuba

16
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

June 16, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026

A yau Juma’a, 24-01-1445 (Hijriyya) = 11-08-2023, Limamin Masallacin Unguwar Tumbu da ke garin Madallah, Ƙaramar Hukumar Suleja, Jihar Neja, ya gabatar da huɗuba, wacce maudu’inta ya kasance “Muhimmancin Sallar Juma’a A Musulunci.”

Bayan gabatarwa, girmamawa da yabo ga Allah (swt) da sallama da salati ga fiyayyen talikai, Manzon Allah, Muhammadu (saw), Liman ya jawo hankalin al’umma da mu ji tsoron Allah, mu riƙe Musulunci da gaske. Ya ce mu sani fa Allah Ya cika mana addininmu, wanda shi ne babbar ni’imar da babu kamar ta a bayan ƙasa.

Ya bayyana mana cewa Allah Ya farlanta mana rukunonin addini guda biyar, ciki kuwa har da salloli biyar a rana, ciki kuwa har da Sallar Juma’a.

Kamar yadda Liman ya nusar da mu, yana daga falalar Sallar Juma’a mutum ya yi gaggawar zuwa masallaci, domin samun babban rabo. Kada mutum ya sake wani abu ya shagaltar da shi daga halartar Sallar Juma’a.

Liman ya nusar da mu wasu daga ladubban Jumu’a – mutum ya yi wanka, ya yi alwala, ya saka sutura mai kyau da turare mai ƙanshi. Mutum ya yi nafilfili, ya yi salati mai yawa ga Manzon Allah (saw). Mutum ya natsu ya saurari huduba, kada ya yi magana da kowa.

Liman ya sanar da mu wani hadisi na Manzon Allah, wanda ke cewa babu Jumu’a ga duk wanda ya yi magana a yayin huɗubar Jumu’a.

Haka kuma ya sake kwaɗaitar da al’umma game da falalar Sallar Juma’a, inda ya sanar da mu wani hadisi, inda Manzon Allah (saw) ke cewa, duk wanda ya yi alwala, ya je Sallar Juma’a, ya yi nafila, ya samu huɗuba, to an yafe masa zunubbansa na makon, har ma da ƙarin kwana uku gaba.

Liman ya tsoratar da mu ga barin Sallar Juma’a. Ya kafa mana shaida da hadisin Manzon Allah (saw), cewa duk wanda ya yi fashin Sallar Jumu’a sau uku a jere, ba tare da wani uzuri amsasshe ga Shari’a ba, to an rufe zuciyarsa.

Wanda kuwa ya bari Allah Ya rufe masa zuciya, tabbas ya taɓe. Allah Ya kiyashe mu, Amin.

Malam Ya ja hankalinmu da mu guji yin duk wata hulɗa ta kasuwanci ko aiki a daidai lokacin Sallar Jumu’a, domin kuwa haramun ne. Amma babu laifi mutum ya koma bakin aikinsa ko sana’a, da zarar an kammala Sallar Jumu’a.

Malam ya rufe huɗubarsa da kyakkyawar addu’a ga al’ummar ƙasa. Allah Ya sa mu dace da rahamarSa, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da imani da yalwar arziki. Amin.
~~~~~~~

Previous Post

Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Next Post

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

Related Posts

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA
Addini

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

June 16, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Next Post

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan - ZAINAB AHMAD

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
TASKAR GIZAGO Adds category

TASKAR GIZAGO Adds category

September 8, 2023
ALIYU ƘANƘARA YA ZAMA FARFESA

ALIYU ƘANƘARA YA ZAMA FARFESA

October 7, 2025
MUHAMMADU (SAW)

MUHAMMADU (SAW)

October 3, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.