• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Gwamna Namadi Ya Ladabtar Da Shugabannin Babban Asibitin Gumel

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 1, 2023
in Babban Labari
0
Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Gwamna Malam Namadi

25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamna Namadi Ya Ladabtar Da Shugabannin Babban Asibitin Gumel

Biyo bayan ziyarar ba zata da Gwamna Malam Umar Namadi ya kai Babban Asibitin Gumel a ranar Juma’ar da ta gabata, dangane da yadda gwamnan ya sami asibitin cikin wani mummunan yanayi, yanzu haka an ɗauki matakan ladabtarwa ga manyan jami’an gudanarwa na wannan asibiti.

Related posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026

Matakan sun haɗa da rushe hukumar gudanarwar asibitin nan take da kuma mayar da ɗaukacin manyan jami’an wannan asibitin zuwa hedikwatar Ma’aikatar Lafiya da ke Dutse, inda za su jira hukuncin da zai hau kansu bayan an kammala bincike.

Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da: Daraktan Gudanarwa, Daraktan Kula Da Ayyukan Jinya, Shugaban Kula da Magani, Shugaban Medical Director, Director Ɗakin Bincike da kuma Akawun asibitin.

A kwanakin baya ne Gwamnan ya ziyarci asibitin, inda ya kewaya sassa daban-daban a cikin asibitin ya gane wa idonsa yadda ake tursasa wa marasa lafiya biyan kuɗin kayayyakin da ya kamata a samar da su a asibitin.

“Alal misali, Gwamnan ya tattauna da marasa lafiya da dama waɗanda suka tabbatar masa da cewa ana tilasta musu biyan kuɗi har Naira 7,000 kafin a ɗauki jinin da ‘yan uwansu suka ba su gudunmuwa. Haka kuma ya gano cewa hatta auduga da ake amfani da ita a asibitin, marasa lafiyar ne suke saye da kuɗinsu, wanda kuma hakan ya saɓa wa manufar gwamnatin jiha na samar da waɗannan abubuwa kyauta, musamman ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu shayarwa,” inji Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Hamisu Gumel, a wata takardar da ya raba wa manema labarai.

Ya ƙara da cewa, baya ga wannan kuma Gwamnan ya gane wa idonsa yadda asibitin yake fama da matsalar isasshen ruwan famfo, duk kuwa da kuɗaɗen da gwamnati take samarwa asibitin a kowane wata. Bugu da ƙari kuma, Gwamnan bai sami shugabannin asibitin a bakin aikinsu ba a lokacin wannan ziyarar.

Bayan ziyarar ce, sai Gwamna Namadi ya yi taron gaggawa da manyan jami’an Ma’aikatar Lafiya da na hukumomin da ke ƙarƙashinta a safiyar Litinin da ta gabata, inda nan take ya umarci Kwamishinan ma’aikatar da ya ɗauki matakan ladabtarwa a kan wannan halayya ta ma’aikatan kiwon lafiyar.

Previous Post

Amina Gambo Ta Yi Bankwana Da Freedom Radio

Next Post

Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Related Posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi
Babban Labari

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
Next Post
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Gwamnan Katsina Ya Raba Ma'aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

May 29, 2023
INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

March 6, 2025
TY BURATAI LITERARY INITIATIVE: Unveiling the Young Literary Giants

TY BURATAI LITERARY INITIATIVE: Unveiling the Young Literary Giants

November 4, 2024
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Katsina Governor Inaugurates Committees to Distribute Palliative

September 27, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.