Katsina A Makon Jiya (21 Zuwa 27-09-2026)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
A makon da ya gabata, wanda ya faro daga ranar Litinin, 21-09-2026, al’amura masu yawa kuma masu muhimmanci ga ci gaban al’ummar Jihar Katsina sun gudana, bisa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, CON.
Ɗaya daga cikin muhimman al’amuran, shi ne inda mai girma Gwama Raɗɗa, a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma, ya jagoranci ayarin gwamnonin shiyyar, su bakwai zuwa Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81, a birnin New York na Amurka.
Gwamna Raɗɗa ya gabatar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci gaban Arewa maso Yamma na shekarar 2026–2030 a taron na bana, inda ya yi wa abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, masu zuba jari, cibiyoyin hada-hadar kuɗi da masu ruwa da tsaki a kamfanoni masu zaman kansu bayani kan muhimmancin haɗin gwiwar yankin wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ci gaban Arewa maso Yamma.
Wani al’amarin mai muhimmanci da ya gudana a Jihar Katsina a makon da ya gabata, shi ne yadda aka kafa sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Najeriya (Ɓangaren Intanet) Reshen Jihar Katsina kuma aka zaɓi shugabannin riƙon ƙwarya.
Waɗanda aka ɗora wa alhakin sgugabancin ƙungiyar na riƙon ƙwarya, sun haɗa da a matsayin Shugaba. Sai Mustapha Saddiq, a matsayin Sakatare da kuma Zaharaddeen Ishaq, a matsayin Ma’aji.
Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a yayin da yake taya sabbin shugabannin murna, ya yi kira ga ‘yan jaridar da su riƙa gudanar da aikinsu bisa bin doka da ƙa’idojin da aikin ya tanada; yana mai cewa su riƙa tantance labari kafin su yaɗa shi, domin kauce shiga haƙƙin al’umma.
Haka kuma, a makon na jiya ne Jihar Katsina ta cika shekaru 39 da ƙirƙirowa, don haka a yayin bikin murna, Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta tsaro da ci gaban jihar.
Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya wakilce shi a wajen taron, kasancewar shi yana ƙasar Amurka, inda ya jagoranci Gwamnonin Arewa maso Yamma babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
A yayin bikin, Gwamna ya ce tun bayan ƙirƙirar jihar a ranar 23 ga Satumba, 1987, Katsina ta samu ci gaba a fannoni daban-daban, duk da wasu ƙalubalen da har yanzu ake fuskanta.
Ya ce a fannin noma, gwamnatinsa ta samar da taraktoci 400, injinan girbi 10, injinan noma 4,000 da kuma injinan dasa iri 2,000, waɗanda aka rarraba a faɗin ƙananan hukumomi 34.
Ya kuma bayyana shirin samar da rijiyoyin ban ruwa 3,000, wato guda dubu a kowace shiyyar Sanata.
A fannin tsaro kuwa, gwamnan ya ce an ɗauki jami’an Community Watch Corps 3,000 da ’yan sa-kai 1,500 domin ƙarfafa tsaron al’umma.
Ya ce gwamnati na kuma tallafa wa waɗanda hare-haren ’yan bindiga suka shafa da iyalan da suka rasa matsugunansu.
A ɓangaren tattalin arziki, Gwamna Raɗɗa ya ce sama da ƙananan sana’o’i 5,000 sun samu tallafin Naira biliyan 2.5, wanda ya taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi dubu 15.
Haka kuma, mata 14,450 sun samu kayan fara sana’o’i da darajarsu ta haura Naira miliyan 700.
A fannin ilimi, gwamnan ya ce an gina makarantun sakandare 152 karkashin shirin AGILE, tare da kafa makarantu uku na zamani da gina ko gyara azuzuwa 3,090.
Ya ce malamai dubu 20 sun samu kwamfutocin hannu da horo kan fasahar zamani.
A bangaren lafiya kuea, an inganta cibiyoyin lafiya shida zuwa manyan asibitoci, yayin da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko 271 daga cikin 361 aka inganta tare da samar musu da kayan aiki.
Gwamna Raɗɗa ya kuma ce gwamnatinsa ta biya sama da Naira biliyan 45 na kuɗaɗen ritaya ga ma’aikatan da suka yi ritaya a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
A yayin bikin, Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim M. Ida ya waiwayi tarihin ƙirƙirar jihar ta Katsina da irin ƙalubalen da shugabannin farko suka fuskanta.
Ya ce Katsina ta fara ne da ƙananan hukumomi bakwai da ƙarancin albarkatun kuɗi amma shugabannin farko suka yi amfani da gaskiya da amana wajen kafa muhimman ababen more rayuwa, inda ya ambaci samar da aikin faɗaɗa madatsar ruwan Ajiwa, hedikwatar ’yan sanda, Federal Medical Centre, Babbar Kotun Jiha, filin wasa na Karkanda da kuma Gidan Rediyo da Talabijin na Katsina.
Sanata Ida ya yi kira ga al’ummar jihar da su kiyaye gaskiya da amana, yana mai cewa waɗannan ɗabi’u ne suka taimaka wajen gina jihar tun daga farko.
Kamar yadda aka saba a kowace shekara, a yayin taron, an karrama jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya, ma’aikatan gwamnati da sauran ’yan jihar da suka nuna ƙwazo wajen yi wa Katsina hidima.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Dakta Faisal Umar Kaita da Alhaji Usman Isyaku, Pharm. Yusuf Nasiru da Dakta Mustapha Shehu. Haka kuma, an karrama jami’an ’yan sanda, DSS, Sojoji da Community Watch Corps saboda gudummawarsu wajen tsaron jihar.
Gwamna Radda ya taya waɗanda aka karrama murna, tare da yin kira ga al’ummar Katsina da su ci gaba da haɗa hannu da gwamnati domin samun zaman lafiya da ci gaba.
Waɗannan al’amura da muka tsakuro, su ne kaɗan daga cikin ɗimbin muhimman al’amuran da suka gudana a Jihar Katsina a makon da ya gabata.Da fatan Allah ya kai mu ƙarshen wannan makon, domin da sake zayyano wasu muhimman al’amuran.
_________













