Nasiharmu Ta Yau Alhamis (01)

__________
Ya ɗan uwa, ko ka lura da yadda mintuna suke komawa awoyi, su kuma suke komawa kwanaki zuwa makonni zuwa watanni? Kafin ka ankara shekara ta kama. Wannan ke nuna maka yadda RAYUWA take shuɗewa. Ka yi ƙoƙarin aikata mai kyau a cikin LOKACINKA tun kafin ya wuce.”
__________













