NASIHARMU TA YAU (53)
Mu Guji Hassada (8)
__________
Babban matakin da ya kamata a bi domin magance ciwon hassada shi ne, idan mutum ya ga wani alheri a hannun wani, to sai ya yi masa addu’ar albarka, sannan ya mayar da hankali kan neman falalar Allah. Ya jajirce ya yi aiki ko sana’a, ba zaman banza da sanya ido ga rayuwar wasu ba.
Ta yaya za mu guje wa dukkan illolin hassada? Musulunci ya kawo mana hanya mafi dacewa ta tsarkake zuciya. Wannan hanya ita ce ta neman tsari da kuma tsarkake zuciya daga ƙazantar zargi da ƙiyayya. Surorin Alƙur’ani biyu (Falaƙi da Nasi), Allah ya saukar da su ne domin su zama garkuwa ga al’umma daga dukkan sharri, ciki har da sharrin mai hassada.
Muna roƙon Allah ya kiyashe mu daga ciwon hassada kuma ya kare mu daga sharrin hassada da masu hassada gare mu da al’ummarmu. Amin-Summa-Amin!
(Mun Kammala)
___________













