• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamna Ya Rantsar da Sabbin Manyan Sakatarori A Jihar Katsina

DIKKON KATSINAWA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 6, 2026
in Labarai
0
Gwamna Ya Rantsar da Sabbin Manyan Sakatarori A Jihar Katsina

Dikkon Katsinawa (3)

7
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamna Ya Rantsar da Sabbin Manyan Sakatarori A Jihar Katsina

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rantsar da sabbin Manyan Sakatarori guda huɗu, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sassauci wajen tabbatar da cancanta, gaskiya da adalci a harkokin gudanar da mulki ba.

Related posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026

Sabbin Sakatarorin da aka rantsar sun haɗa da Malam Abdu Usman, Dakta Sani Suleiman, Dakta Shamsuddeen Yahaya Suleiman da Dakta Hussaini Hamisu Yanduna. An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Laraba, 5 ga Agustan 2026, a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Manyan Sakatarorin Jihar Katsina suna amsar rantsuwa

Da yake jawabi bayan rantsar da su, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa an zaɓi sabbin jami’an ne bisa cancanta, ƙwarewa da jajircewa wajen aiki, ba tare da la’akari da alaƙa, sanayya ko wani tasiri na daban ba.

Ya buƙaci sabbin Sakatarorin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci, yana mai bayyana cewa irin waɗannan kyawawan ɗabi’u ne za su taimaka wajen ƙara inganta ayyukan gwamnati da kuma samar da ingantacciyar hidima ga al’ummar Jihar Katsina.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da tsarin da ke tabbatar da adalci wajen ba da damar ci gaban ma’aikatan gwamnati, domin ƙarfafa ƙwazo da haɓaka ingancin aikin gwamnati.

Hakazalika, ya yi kira ga manyan jami’an gwamnati da su mayar da hankali wajen horar da matasa ma’aikata tare da koya masu aiki, su goge, domin samar da ƙwararrun ma’aikatan da za su ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati cikin inganci a nan gaba.

Bikin rantsarwar ya nuna wani mataki na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda na ƙarfafa tsarin aikin gwamnati ta hanyar bai wa ƙwararru damar jagorantar manyan sassan gudanarwa, domin inganta ayyukan gwamnati da bunƙasa hidimomin da ake kai wa al’ummar jihar.
__________

Previous Post

Governor Dikko Flags Off Construction, Expansion of 3-Kilometre Mashi Township Road

Next Post

Governor Radda Swears In New Permanent Secretaries

Related Posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro
Labarai

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Next Post
Governor Radda Swears In New Permanent Secretaries

Governor Radda Swears In New Permanent Secretaries

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

NASIHARMU TA YAU 14

NASIHARMU TA YAU 14

October 7, 2026
Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

March 23, 2026
Gen. Buratai Celebrates John Mahama’s Second Coming as Ghana’s President 

Gen. Buratai Celebrates John Mahama’s Second Coming as Ghana’s President 

December 10, 2024
Rusau A Kano: Ja’afar-Ja’afar Ya Soki Rusa Hasumiyar Algaita

Rusau A Kano: Ja’afar-Ja’afar Ya Soki Rusa Hasumiyar Algaita

June 14, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
  • NASIHARMU TA YAU 17
  • NASIHARMU TA YAU (16)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
NASIHARMU TA YAU 17

NASIHARMU TA YAU 17

October 10, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.