RAMADAN KARIM: 19-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau Lahadi, Allah ya nuna mana rana ta 19 a Ramadan. Yau ma ga nasiharmu:
‘Yan uwa, yau kuma za mu yi nuni ne zuwa ga kyakkyawar mu’amala da juna, musamman ta hanyar kyautata wa juna ta fuskar magana da sauran musharaƙa cikin al’umma. A duk lokacin da za mu yi wata mu’amala da juna, to mu kyautata kalamai. Mu riƙa magana cikin usulubi mai kyau, ba tare da munana ko kausasa harshe ba.
Allah yana faɗa a Suratu Ibrahim 14:24, cewa: “Kalma mai kyau kamar itaciya ce mai kyau.” Haka ma Manzon Allah (saw), a Hadisin Bukhari mai lamba 2989 da Muslim mai lamba1009, yana cewa: “Kalma mai kyau sadaka ce.”
Ke nan, a duk lokacin da ka kyautata kalaminka ga wani ko wata a yayin wata mu’amala, kana samar da aminci da kwanciyar hankali. Kuma yin haka, kana yin sadaka ne. Allah ya sa mu dace, Amin.
__________













