RAMADAN KARIM: 04-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan haka, a yau Allah ya nuna mana rana ta 4 a Ramadan, don haka bari mu ribaci wannan rana da ‘yar nasiha:
A yau za mu yi tsokaci ne game da wata halayya, wacce ke cutar da mu matuƙa. Wannan kuwa ita ce halayyar fushi. Fushi, duk da cewa yana ɗaya daga cikin halayyar ɗan Adam, amma babu shakka yana da fa’ida mu ladabtu da danne shi, domin rage kaifin tasirin ɓarnar da zai haifar mana.
A duk lokacin da muka samu kanmu cikin fushi, to mu kasance cikin juriya da haƙuri. Kada mu sake mu yanke wani hukunci a cikinsa. Idan muna tsaye ne, mu zauna. Idan ma ya ta’azzara, to mu yi ƙoƙarin barin wurin ko kuma mu yi alwala, mu yi nafila, koda raka’a biyu ce.
Jarumi, shi ne ke mallakar fushinsa, wanda kuma yake yafiya ga waɗanda suka munana masa. Allah (swt), a cikin Suratu Ali-Imran 3:134 ya ce, “…masu danne fushi kuma masu yafiya ga mutane.”
Manzon Allah (saw) a Hadisi mai lamba 6114 na Bukhari da Muslim mai lamba 2609, sun ruwaito yana cewa: “Mai ƙarfi shi ne wanda yake danne fushinsa.”
Muna roƙon Allah ya mallaka mana zukatanmu, mu zama masu danne fushi, mu zama masu yafiya ga juna; Amin.
__________













