ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU (NSA)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan gaisuwa mai ƙima irin ta addinin Musulunci, na zaɓi in aiko maka wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa saboda in jawo hankalinka, dangane da abin da ke faruwa a ƙasar nan; sannan in ba ka shawara ɗaya ko biyu, da nufin samun gyara a lamurran al’ummarmu.
Da farko dai sunana Bashir Yahuza Malumfashi. Ni marubuci ne kuma sha’iri. Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa, mawallafi kuma Babban Editan Mujallar Taskar Gizago ta intanet.
Ranka ya daɗe, Malam Nuhu Ribadu, kai ne mutum mafi girma ta ɓangaren harkokin tsaro a Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ka fito daga yankin Arewa. Ka kama aiki kimanin shekara ɗaya da ta gabata. Babu shakka akwai buƙatar ka tashi tsaye, ka jajirce ka yi abin da ya kamata, domin ganin an samu gamsasshen tsaro a Arewa da ma Najeriya baki ɗaya, musamman domin ka kare martabar kanka da yankinka da ma ƙasa baki ɗaya.
A matsayinka na Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara ta Fuskar Tsaro (NSA), duk da cewa na san ka fi kowa sanin irin barazana da matsalolin tsaro da suka yi katutu a Arewa da ma ƙasa baki ɗaya amma duk da haka, zan sake jaddada su a nan domin tunatarwa da burin ƙara maka himma, domin a tunkare su kai tsaye, a magance su.
Ya mai girma NSA, a yau ba sai gobe ba, Arewa tana gab da durƙushewa. Gabas da yamma, kudu da arewa da dukkan kusurwowin Arewa ana fuskantar barazanar tsaro. ‘Yan bindiga suna cin karensu babu babbaka. Suna sace mutane don kuɗin fansa. Suna korar mutane daga muhallansu. Suna hana noma da kiwo. Suna mayar da mata da yawa zuwa zawarawa. Suna mayar da dubban yara zuwa marayu. Sansanonin ‘yan gudun hijira sai ƙaruwa suke yi. Dubban magidanta sun koma mabarata a ƙasarsu ta haihuwa.
Yunwa da talauci suna daga cikin abubuwan da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a Arewa. A yau, dubban matasa majiya ƙarfi babu aikin yi, babu sana’a. Wasu da dama daga cikinsu, sun gama karatu har matakin digiri na ɗaya da na biyu amma ba su da zarafin yi, babu aiki babu sana’a.
A yau magidanta da yawa da yunwa suke kwana suke tashi. Ba su da wata madafa sai zaman durshan da tsammani, tare da juyayi – talauci ya ta’azzara. Don haka, ya kamata ofishinka ya yi wani abu domin kawo sauƙi a lamarin, domin kuwa ina da tabbacin cewa wannan na ɗaya daga cikin ayyukan ofishinka – samar da yanayin kwanciyar hankali ga al’umma domin tabbatar da tsaro.
Sanin kanka ne cewa, duk mutumin da bai ajiye ba kuma bai ba wani ajiya ba, kuma yana zaman durshan, to bai da babban aboki sai shaiɗan.
Ya mai girma NSA Ribadu, na san ka sani, a yau saboda tsananin ƙunci da rashi, matasa a Arewa sun harzuƙa. Sun fara yunƙurin gudanar da zanga-zanga, kamar yadda suke ta shelantawa, nan da ranar ɗaya ga watan Agusta mai zuwa. Lallai ne a zauna a saurari lamarin nan, a kawo mafita da za ta daƙile wannan babbar fitina, wacce idan ta faru (Allah Ya kare) ba mu san iya inda za ta tsaya ba.
A gani na, ga wasu shawarwari da zan ba ka, domin ka tunkari Shugaban Kasa da su, domin sauƙaƙa al’amura ga al’ummar ƙasa baki ɗaya. Shawara ta farko ita ce, a sauke farashin fetur ya dawo Naira 200 kowace lita. Shawara ta biyu, a kafa ƙaƙƙarfar hukumar ƙayyade farashin kayan masarufi. Shawara ta uku, a ba ‘yan kasuwa damar shigo da kayan abinci daga waje ba tare da harajin ko kwabo ba. A samar da hanyoyin aiki da sana’a ga matasa cikin lokaci. Dukkan waɗannan matakai masu yiwuwa ne, domin kuwa Allah Ya sanya ɗimbin arziƙi a ƙasar nan. Na san haka. Kai ma ka san haka. Kuma kowa ma ya san haka. Don haka babu wani dalili da zai sa talakan Najeriya ya riƙa kwana da yunwa.
Ranka ya daɗe Ribadu, idan gwamnatin nan ta samu nasara, ka samu nasara. Idan ta ruguje, kai ma ka ruguje. Sunanka zai ɓaci, yadda a kullum za a riƙa kafa misali da kai a tarihi har abada. Don haka, don Allah kada ka bari sunanka ya faɗa cikin mummunan tarihi. Ka yi duk abin da ya kamata domin ka rubuta sunanka a kundin tarihi na zinari.
Ranka ya daɗe NSA, kafin in rufe wannan wasiƙa, bari in ɗan tuna maka baya, irin ƙima da martabar da kake da ita a idanun al’ummar ƙasar nan. A can baya, kai ne fa gogarman yaƙi da zalunci da azzalumai. Kai ne ka shahara wajen kare martabar ƙasar nan daga zalunci da almundahanar azzalumai. Kai ne gogarman da duk wani azzalumi ke tsoro a ƙasar nan. Yadda ka kafa wannan babban tarihi a jiya, yau ma za ka iya. Lallai ya kamata ka ba mara ɗa kunya. Ka tashi tsaye, ka jajirce domin aiwatar da duk abin da ya kamata, domin ganin an fitar da jaki daga duma.
Ina roƙon Allah Ya ba ka iko da nasarar aiwatar da dukkan abin da zai kawo zaman lafiya, arziƙi da kwanciyar hankali a ƙasar nan. Allah Ya sa mu dace, Amin.
Ka huta lafiya.
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, wanda ke burin ganin ka samu nasara.
__________
Laraba, 11-01-1446 (Hijriyya)
17-07-2024 (Miladiyya)













