Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________

√ Me Ya Sa Suke Kiran Masu Adawa Da Su Fulani?
Wani abin mamaki da rashin tunani na Hausawan Bogi, ‘Yan Ba-Zata shi ne, a kullum suka ga mutumin da ya saɓa da ra’ayinsu ko kuma yake tona asirin makircin da suke ƙulla wa al’umma, sai su ƙaƙaba masa rigar Fulani, su riƙa cewa shi Bafulatani ne, koda kuwa shi Bahaushe ne.
Haka kuma, tun daga lokacin za su ɗauki karan tsana su ɗora masa, koda kuwa ba su taɓa saninsa ko ganinsa ba a zahiri. Za ka ga suna tsine masa, suna ƙirƙirar labarun ƙarya suna jingina masa.
Waɗannan mutane suna yin haka ne da gangan kuma bisa manufar jefa ƙyama da tsanar ƙabilar Fulani. A gefe ɗaya kuma, domin su gwara kan Musulmi da haɗa husuma tsakanin al’ummar Arewa.
Su a rashin adalcinsu, duk wani mutum da ya fito daga ƙabilar Fulani, to ɗan ta’adda ne, komai gaskiyarsa, komai son zaman lafiyarsa, koda bai taɓa kashe ɗan tsako ba. Suna ɗora wa dukkan Fulani laifi ne saboda laifin da wasu ƙalilan na baragurbin Fulani ke aikatawa na ta’addanci. Amma kuma a gefe ɗaya, za ka ji suna yabon ‘yan ta’addan IPOB ko ‘yan ta’addan Birom da suke kashe Hausawa a Filato da sauran yankunan da suke kira Middlebelt.
Ni kuwa na ce, anya wannan adalci ne kuwa? Ta yaya za ka hukunta wata ƙabila gaba ɗayanta, bisa laifin da wasu tsirarun cikinta suke aikatawa?
Ko a jiya, wani mutum mai suna Salmanu Gwanzo, wanda nake kyautata zaton ɗan Ƙungiyar Hausawa Zalla ne, ya ƙalubalance ni, ya ce wai ina ba Fulani ‘yan ta’adda kariya; don haka Allanbaran ni Bafulatani ne. Shi ne na ba shi amsa kamar haka:
Ka ji tsoron Allah. Ka kawo mani rubutu ɗaya nawa, inda na taɓa kare FULANI ‘YAN TA’ADDA? Bal, ni ina cikin mutane sahun gaba da suke adawa da SULHUN DA AKE YI DA SU!
Idan ba ka taɓa gamuwa da rubutuna inda nake adawa da su ba, bari yau in jaddada matsayata a kan DUK WANI ƊAN TA’ADDA:
√ Ba na tare da duk wani mutum da ya ɗauki makami yana kashe al’umma, ko wane ne shi, ko wane ƙabila ne shi – BALARABE, BAHAUSHE, BAFULATANI, IBO, YORUBA, KATAF, ANGAS, BIROM, KANURI da sauransu.
√ Duk wanda ya aikata laifi (ƙarami ko babba) a hukunta sh,i shi kaɗai bisa laifin da ya aikata. AMMA KADA A SAKA DUKKAN ‘YAN ƘABILARSA, waɗanda ba su aikata laifin komai ba.
√ Laifin da ‘yan IPOB suka aikata, ba za a ɗora wa dukkan ƙabilar IBO ba.
√ Laifin da Area Boys suka aikata, ba za a ɗora wa dukkan YARABAWA ba.
√ Laifin da FULANIN DAJI suke aikatawa, ba za a ɗora wa dukkan ƙabilar FULANI ba.
√ Adalci shi ne, hukuma ta kama tare da hukunta duk wanda yake aikata laifi, shi kaɗai. Ba dukkan ‘yan ƙabilarsa ba, waɗanda ba su aikata laifin komai ba.
√ INA ROƘON ALLAH YA LA’ANCI DUK WASU ‘YAN TA’ADDA, KOWACE ƘABILA SUKE, KOWANE ADDINI SUKE, DA DUK MASU TAYA SU, DA DUK MASU JIN DAƊIN ABIN DA SUKE YI, DA DUK MASU ƊAURE MASU GINDI!
√ WANNAN ITA CE MATSAYATA HAR KULLUM!
__________













