• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 5, 2026
in Labarai
0
Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Wasu daga cikin makaman da aka kama da kuma matar da ake zargi

17
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Wasu daga cikin makaman da aka kama da kuma matar da ake zargi

                         __________
Sojojin Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun samu gagarumar nasarar ƙwato tarin makamai da harsasai daga maɓoyar wasu muggan masu aikata manyan laifuka a Ƙaramar Hukumar Takum, Jihar Taraba.

A wata sanarwa daga Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedkwatar Operation Whirl Stroke, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu ya bayyana cewa, jami’an sun gudanar da wannan aiki ne a ranar 04 ga Janairu, 2026, bayan samun ingantattun bayanan sirri game da wani shahararren shugaban masu laifi, John Ngata. Sojojin sun kafa shingen bincike a Zaki-Biam, inda suka samu nasarar tare wata matar da ake zargi.

Bayan an yi wa matar da ake zargin tambayoyi, ta jagoranci sojojin zuwa wata maɓoya, inda suka gano rumbun makamai da ƙungiyar masu laifin suka ɓoye a Ƙauyen Amadu, cikin Ƙaramar Hukumar Takum. Binciken ya kai ga ƙwato tarin makamai masu yawa da suka haɗa da bindigogin AK-47 guda 13 da gwangwanin alburusan bindiga (magazines) na AK-47 guda 39 da alburusai masu tsawon kilomita 7.62 guda 690 da kuma gurneti guda 4.

Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation WHIRL STROKE, Manjo Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwarewarsu, saurin ɗaukar mataki da kuma yadda suka yi amfani da bayanan leƙen asiri yadda ya kamata, lamarin da ya kai ga katse hanyar samar wa masu laifi makamai da kuma ƙwato makamai masu haɗari.

Ya sake jaddada ƙudurinsa na ci gaba da ƙarfafa gwiwar sojoji ta hanyar ba da fifiko ga walwalar su, tallafin kayan aiki da kuma shirin ko-ta-kwana na aiki. Haka kuma, ya gode wa al’umma bisa ci gaba da bayar da haɗin kai da kuma sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa goyon bayan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da aikata laifuka a yankin.

Ya ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai cikin lokaci kuma masu amfani, yana ba su tabbacin tsare sirri da ɗaukar mataki cikin gaggawa, domin Operation WHIRL STROKE ta ƙuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a duk yankin da take aikinta.
__________

Previous Post

Hausa/Fulani: Together Forever

Next Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Related Posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta
Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Next Post
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Yunkurin 'Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ACF to TINUBU: MR. PRESIDENT, YOUR GOVERNMENT NEGLECTS AND SIDELINES AREWA

ACF to TINUBU: MR. PRESIDENT, YOUR GOVERNMENT NEGLECTS AND SIDELINES AREWA

August 1, 2025
Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

August 15, 2023
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (4)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (4)

February 3, 2026
Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

March 23, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.