Abubakar Dalhatu Zurmi: Zahirin Ɗan Kasa Nagari Mai Kishin Ƙasa
Daga Abba Hikima

•••••••
Sunansa Dr. Abubakar Ɗalhatu Zurmi, Ph.D., wanda yanzu haka shi ne Kwanturola na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) mai kula da yankin Kano da Jigawa, wanda kuma a yanzu haka yanke dab da yin ritaya daga aiki.
Yakan je wurin aiki da ƙarfe takwas na safe kuma ba ya tashi sai wata ƙarfe takwas ɗin da dare. Ba ya amfani da motar gwamnati idan ya tashi daga aikin ofis. Yakan yi amfani da wata tsohuwar motarsa ƙirar Fijo. Kuma a kanta yakan lallaɓa, idan tafiya ta kama shi zuwa Abuja kuma ya dawo cikin kwanciyar hankali.
Idan ka je hedkwatar Hukumar Kwastam ta Jihar Kano, za ka iya samun shi yana zaune a waje, ƙarƙashin inuwa, yana sauraron jama’a kai tsaye. Lokacin da na tambaye shi dalilin da ya sa ya fi zama a waje fiye da ofis, sai ya ce:
“Hikima, ni Kwantutrola ne na Hukumar Kwastam, kuma ana ɗauka cewa babban mutum ne ni. Idan zan riƙa zama a ofis kullum, masu zuwa da buƙatu za su riƙa fama da tsaiko mai wahala, saboda yanayin tsarin aikin da ke haddasa haka. Haka kuma, a matsayina na sabon shugaba, idan ban fita waje ba, zan rasa fahimtar abubuwan da ke faruwa a wajen ofishina.”
Wataƙila masu son ƙulla cuta ko wata almundahana ba za su ƙaunace shi ba, amma tabbas tsarin shugabancinsa ne ya kawo ƙarshen tsarin cin hanci da karɓar rashawa da suka daɗe suna faruwa a hukumar da ke wannan shiyya.
Na tuna wata rana da na shiga ofishinsa, jim kaɗan bayan wani mutum ya zo ya ba shi tayin cin hanci na miliyoyiin Naira, wanda ya ƙi karɓa nan take. A lokacin da na je ofishin nasa, mutumin da ya ba shi tayin hancin, bai kai ka barin ofishin ba. Na iske shi Kwanturola Zurmi yana yi masa gargaɗi da nasiha game da illar cin hanci da rashawa. Kan haka ma ya ce mani in taimaka masa, in ƙarfafa saƙonsa na yaƙi da cin hanci da rashawa da makamantansu.
Kafin a turo shi Shiryar Kano da Jigawa, manyan masu safarar kaya da dama sun rufe kamfanoninsu saboda tsananin cin hanci da ƙwace kaya da jami’an Kwastam suke yi a hanyoyin Alaba da daga Kudancin Ƙasa zuwa Arewa. A can baya, duk wata motar kaya kafin ta isa Kano sai an kashe aƙalla ₦500,000 a kan hanyar. Kowane shingen bincike, sai an karɓi aƙalla ₦50,000, kuma akan samu irin waɗannan shingaye fiye da goma. ‘Yan kasuwa da direbobi sun shiga tashin hankali, har wasu kamfanoni sun rushe a sakamakon irin wannan zalunci.
Amma lokacin da mutumin nan ya zo, sai ya kawo gyara, ya gano kurakurai a tsarin tafiyar da aikin nasu, inda ya ba da umurnin cewa kayan da doka ta sahale a shigo da su, a ƙyale su amma kuma ba wanda ya isa ya zalunci masu kaya. Ya zuwa yanzu ‘yan kasuwa masu safarar kaya na gaskiya, suna jin daɗin gudanar da ayyukansu. Ɗaya daga cikinsu ya gaya mani cewa yanzu yana samun fiye da Naira miliyan 20 a wata.
Wani abokina lauya wanda ke hulɗa da Kwastam sosai ya ce mani: “An samu sabon jami’in Kwastam mai tsauri a gari.”
Wani daga cikin jami’ansa ya gaya mani cewa saboda tsarin aikin ubangidansa Kwanturola Zurmi, yanzu bai samun damar yin doguwar hira a waya da masoyiyarsa kamar yadda suke yi a baya, har ma ta fara fushi, tana barazanar rabuwa da shi. Ya ce da rana suna aiki sosai har ba ya samun damar magana da ita kuma da daddare ma bai iyawa saboda gajiya ƙwarai.
A fannin tara kuɗaɗen haraji ga gwamnati kuwa, Abubakar ya toshe hanyoyin ɓarna, yadda abin da ake tarawa a shekara ɗaya, yanzu ana tara shi a cikin watanni uku kawai. Wannan nasara ce ga gwamnati da al’umma baki ɗaya.
Tsarin aikin Kwanturola Zurmi babban abin misali da kwaikwayo ne. Ya fara aikin Kwastam ne daga ƙaramin jami’i na ƙasan-ƙasa amma ya yi ta samun ƙarin girma bisa cancanta har ya kai babban muƙamin Kwanturola. Ya shiga aikin ne da takardar sakandare (O-Level) kawai, amma ya dage, ya tashi ya yi karatu har sai da ya samu Digirin Digirgir, watau Ph.D. Yanzu shi ne Kwanturola mai Digirin Digirgir, jami’i mai daraja, wanda rayuwarsa ke nuna sakamakon tsayin daka, ladabi da neman ci gaba.
Mutane da dama da na sani suna yaba masa sosai. Ina da tabbataci da yaƙinin cewa Dokta Zurmi mutum ne mai gaskiya, mai kirki kuma mai kishin ƙasa. Kuma na san za ku shaide ni da cewa, shi ne mutum na farko mai kaki, wanda na taɓa rubuta irin wannan yabo a kansa, domin na gani, na ji kuma na tabbatar.
Kodayake Zurmi na dab da yin ritaya daga aiki amma bai gaji ba. Shi ne irin shugabannin da Najeriya da ’yan Najeriya ke buƙata a irin wannan lokaci.
_______________
SANARWA: Hikima, babban lauya ne. Ya rubuta wannan muƙala ce a shafinsa na Facebook da Turanci, wakilinmu ya fassara zuwa Hausa saboda muhimmancinsa.












