• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (4)

MUƘALA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 18, 2025
in Gizago
0
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (4)

Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (4)

44
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (4)

Daga Yahuza Malumfashi

Related posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026

 

Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (4)

•••••
Ƙungiyar Hausawa Zalla Da Batun Ramuwar Gayya:

Ya ku ‘yan uwa masu bibiyar wannan muƙala da jimiri, a wannan fitowa kashi na huɗu, za mu ci gaba da bayani dangane da wasu munanan manufofi da muka ankara da su daga ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla, musamman yadda suke nuna su a kafafen sadarwa na zamani (Soshalmidiya).

Ga duk mai tu’ammali da waɗannan kafafe, babu shakka zai riƙa gamuwa da munanan kalaman masu ƙumajin kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla. Ɗaya daga cikinsu shi ne, za su kafa wannan ƙungiya ce, kacokan da nufin ramuwar gayya da ɗaukar fansa a kan musamman Fulani.

A ƙoƙarinsu na bayyana wannan muguwar manufa, ƙarara za ka ji sun kama sunan Mujaddadi Usman Ɗanfodiyo, suna zagin shi da tozarta shi; sannan kuma suna ƙirƙirar tarihin ƙarya suna jingina masa. Ba shi kaɗai ba, masu wannan ƙungiya ta Hausawa zalla, za ka ga suna ta haƙilon haddasa gaba da husuma tsakanin Fulani da Hausawa.

To, abin tambaya a nan shi ne, shin anya kuwa akwai alheri ga ƙungiyar da take bijiro da irin waɗannan baƙaƙen halaye?

Shin da gaske ne, cewa Sheikh Usman Ɗanfodiyo (ra) bai shuka alheri ba a ƙasar Hausa?

Shin wai ma da suke kiran dukkan Fulani da sunan ‘yan ta’adda, musamman kasancewar wasu daga cikinsu suna garkuwa da mutane da ta’addanci a yankin nan, shin a rigar ƙungiyoyin Fulani suke gudanar da wannan ta’addanci?

Shin wannan ta’addanci da wasu baragurbin Fulani suke aikatawa, Hausawa kaɗai suke kamawa da kash+wa?

Za mu bi tambayoyin nan ɗaya bayan ɗaya, inda da yardar Allah, za mu ida fahimtar gaskiyar manufar masu ƙungiyar Hausawa, cewa ba wani abu suke ɗauke da shi ba sai babbar guba da dasisar wargaza al’ummar da ke zaune lafiya da juna na tsawon zamani.

Game da Sheikh Usman Ɗanfodiyo (ra) kuwa, babu shakka, duk wani mai kyakkyawan tunani, musamman idan dai shi Musulmi ne na ƙwarai; to ba zai taɓa kushe Mujaddadi ba. Domin kuwa Sheikh ya kafa babban tarihi, abin yabawa a duniyar Musulunci. Daular Muslunci ta Sakkwato da ya kafa, tun kimanin sama da shekara 200 da ta gabata, ta kasance daula mafi girma da bunƙasa a Afrika ta Yamma.

Ya jaddada Musulunci. Ya yaɗa ilimi. Ya kafa gwamnati mai tsari, abin alfaharin baƙar fata, tun kafin zuwan Turawa. Ya kafa tsarin tafiyar da al’umma mai cike da adalci da ɗa’a da nagarta – wanda har zuwa yau ana cin gajiyarsa.

Jama’a, yau ma a nan zan dakata. Sai kuma karo na gaba, in sha Allahu. A ci gaba da bibiyar mu da haƙuri. Muna kuma maraba da dukkan martani, ƙarin bayani ko tambaya a Comment Section.

Naku,
Bashir Yahuza Malumfashi,
Editan Mujallar Taskar Gizago (online).

Previous Post

Batutuwan Dubawa Game Da Kafa ’Yan Sandan Yanki

Next Post

MALAM LAWANTI

Related Posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi
Gizago

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Next Post
MALAM LAWANTI

MALAM LAWANTI

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 30-1447

RAMADAN KARIM: 30-1447

March 19, 2026
TAKAICI: Waɗannan… Duk A Cikin Mako Ɗaya?

TAKAICI: Waɗannan… Duk A Cikin Mako Ɗaya?

November 20, 2025
RAMADAN KARIM: 08-1447

RAMADAN KARIM: 08-1447

February 25, 2026
AREWA (A Poem)

AREWA (A Poem)

August 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne
  • NASIHARMU TA YAU (18)
  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

October 11, 2026
NASIHARMU TA YAU (18)

NASIHARMU TA YAU (18)

October 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.