WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
A wannan zamani da yake cike da hayaniya, gaggawa da ruɗani, idan ka cire littattafan addini, littattafai kaɗan ne suke samar da natsuwa da ƙarfafa zuciya da saita rayuwa. Littafin “When the Spirit Whispers” (Shiriya Daga Ruhi), wanda bai kai ga fitowa ba tukuna, wanda Uwargida Jumai Ahmadu ta rubuta, ɗaya ne daga cikin irin waɗannan littattafai kaɗan da ke amfanar al’umma.
Ba littafi ne na addini kai tsaye ba, kuma ba kawai an tsara shi domin saita zuciya da samar da jagora da motsa rai ba ne amma babu shakka an rubuta shi ne da nufin saita tunani da inganta rayuwa.
Kowane shafi yana ɗauke da saƙo na musamman, wani lokaci tunatarwa, wani lokaci nasiha, wani lokaci gyara, wani lokaci kuma magani kai tsaye ga zuciya.

Muryar marubuciyar littafin nan ta zo da nutsuwa amma tana da ƙarfi, yadda kalaman nata suke ƙwankwasa murfin zuciya, domin magana kai tsaye ga ruhi. A cikin wannan aiki nata, Uwargida Jumai ta binciko alaƙar da ke tsakanin ƙwarewar ɗan Adam da shaidar ruhi ta nusar, tsakanin tunanin kara-zube da tsantsan tunani na zahiri, mai amfani. Haka kuma yana fayyace gaskiya, tsakanin tunanin da ke bijirowa na kuskure da kuma mai samar da jagora da farfaɗo da ruhi.
Littafin ya ƙunshi bayanai da tunani masu zurfi, waɗanda suke jan hankali ga masu karatu, domin kaiwa ga ƙudurori na gaskiya. Ya kasance littafin da ya dace da kowane zamani, domin yana koya mana yadda za mu saurari tunanin da ke bijiro mana daga ruhi, wanda ke zuwa cikin nutsuwa; wanda galibi hikima ce da ba ta buƙatar hayaniya.
“When the Spirit Whispers,” littafi ne da ya bambanta da tsarin da aka saba bi wajen rubuta sauran littatafai. Littafi ne na ilimi da kuma falsafa, taswira ce ga hankali kuma abinci ne ga ruhi. Ta hanyar littafin nan, Uwargida Jumai tana koyar da mai karatu yadda zai saurari kansa da kansa, yadda zai yi magana ga ruhinsa da kansa, yadda zai yi tunani cikin natsuwa, sannan ya yi martani ga mabambantan maganganun da ke bijiro masa cikin hikima.
Littafin yana ƙalubalantar masu karatu, domin su yi nazarin kansu da kansu, su tambayi kansu mahimman tambayoyi game da rayuwa: Shin mene ne ruhi yake faɗi, a lokacin da duniya ta cika da hayaniya? Ta yaya za mu bambance tsakanin kwaɗayi da buri? Waɗannan tambayoyi ne da suka ɗaga martabar littafin nan, ya bambanta shi daga wasu irinsa, masu bijiro da tunanin motsa rai kawai, ya samar da bayanai na zurfin binciken halayyar ɗan Adam, domin mutum ya san kansa, ya san muhallinsa da mutanen da ke kewayensa da kuma sanin mahaliccinsa.

Game da natsuwa kuwa, littafin yana girmama ƙarfin tattaunawa tsakanin mutum da tunaninsa. Yana fito da gaskiyar da ta fi sauƙi amma mai ƙarfi, cewa hikima tana zuwa cikin tunani mai sanyin rai, ba cikin ihu da hayagaga ba. Ta haka, marubuciyar take gayyatar mai karatu zuwa ga kusanci ga kansa, yadda zai riƙa tacewa da tsaftace tunaninsa da kansa.
A littafin, kowane babi madubi ne. Wani lokacin yana taussa zuciya, wani lokacin yana gargaɗi amma koyaushe yana jagorantar ruhi, domin samar da canji mai amfani. Kira ne na gyara ɗabi’u, warkar da raunukan zuciya da kuma sake gano kusanci da Allah a rayuwar mutum ta yau da kullum.
A ɓangaren ilimi, “When the Spirit Whispers” ainihin aji ne na rayuwa. Yana koyar da dabarar sarrafa zuciya ta hanyar fahimtar ruhi. Yana jagorantar mai karatu zuwa daidaita hankali da ji, lissafi da tantancewa. Yana ƙarfafa al’adar tunani da rayuwa mai ma’ana, abin da ke da amfani ba ga mutum ɗaya kawai ba, har ma ga iyalai, makarantu da cibiyoyi masu neman gina al’umma mai tausayi, ladabi da manufa. Darussan da ke cikinsa ba su ta’allaƙa da lokaci ba kaɗai, sun dace da ɗalibi, malami, shugaba da kowane mai neman ilimi.
A ɓangaren falsafa, littafin ya shiga cikin jerin ayyuka da ke tambayar ma’anar zama mutum na gaskiya. Yana binciko fuskar ɗabi’a da ma’anar rayuwa ta hanyar kalmomi masu sauƙi amma masu zurfin ma’ana. Maimakon ya zama wa’azi, Uwargida Jumai ta buɗe tattaunawa game da haƙuri, tawali’u, gafara, godiya da musharaƙa. Tunaninta yana motsa hankali yayin da yake kwantar da zuciya, yana tuna mana cewa ilimi shi kaɗai bai isa ba; dole ne a haɗa shi da hikima da alheri.
Yayin da duniya ke jiran fitar littafin, “When the Spirit Whispers” ya riga ya zama babban tambari. Motsi ne na tunani da ji, juyin juya hali ne na yaƙi da gurɓatattun tunani da ke bijirowa a cikin rai. Mai karatu ba zai karanta shi kawai ba; zai ji kamar yana rayuwa da shi ne. A kowane shafi, zai haɗu da zurfin ƙimar rayuwa da kalaman saita tunani, waɗanda aka bayyana a cikin salo mai tausasa ruhi. Sabon aikin Uwargida Jumai Ahmadu tunatarwa ce da ta zo a lokaci mafi dacewa. Yunkuri ne na samar da natsuwar zuciya. Hikima ce mai sanar da gaskiya mai warkarwa, mai koyarwa, tare da canza rayuwa daga gurɓatatta zuwa nagartatta.
_______________













