• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Nuhu Ribadu Ya Ɗau Hanyar Magance Satar Ɗanyen Mai

Muhammadu Mustapha by Muhammadu Mustapha
August 27, 2023
in Babban Labari
2
Nuhu Ribadu Ya Ɗau Hanyar Magance Satar Ɗanyen Mai

Malam Nuhu Ribadu a bakin aiki

44
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Nuhu Ribadu Ya Ɗau Hanyar Magance Satar Ɗanyen Mai

Daga Muhammadu Mustapha

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026

A wani yunƙuri na ganin hukuma ta daƙile matsalar satar ɗanyen mai a Nigeria, a jiya Asabar ce Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara A Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya jagoranci wani ayari na musamman daga Fadar Shugaban Ƙasa, domin duba cibiyoyin man fetur da iskar gas a garin Owaza da ke Jithar Abia da kuma Odogwa na Karamar Hukumar Etche ta Jihar Ribas.

Kamar yadda jaridar Katsina Times ta ruwaito, Malam Nuhu Ribadu, ya ce har yanzu Nigeria na asarar ganga 400,000 na ɗanyen mai a kullum daga ɓarayin gida da na waje, duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawo ƙarshen  matsalar.

Ya ce ayyukan ɓarayin ɗanyen mai da masu fasa bututun man suna yin illa ga tattalin arzikin ƙasa, wanda kuma haka na daga cikin dalilan da ke haddasa tsadar rayuwa a ƙasar nan.

“Abin takaici ne cewa wasu mutane ƙalilan ne ke sace dukiyarmu, kuma a cikin haka za suke haifar da asara mai muni ga ƙasa ga jama’a.

“Nigeria na da ƙarfin samar da gangar ɗanyen mai miliyan 2 a kullum, amma a halin yanzu muna samar da ƙasa da ganga miliyan 1.6 saboda matsalar masu sata da lalata bututun mai.” In ji Malam Ribadu.

Da yake ƙimanta yawan ɓarnar da ɓarayin ke yi, ya ce: “Muna magana game da ganga 400,000 na ɗanyen mai da ake ɓarnatarwa, da wasu masu aikata laifi da yi wa ƙasa zagon-ƙasa da tattalin arziki ke aikatawa. Dalili ke nan ya sa ba ma samun riba mai yawa.”

Previous Post

RANAR HAUSA TA DUNIYA

Next Post

Bakan Gizo

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post

Bakan Gizo

Comments 2

  1. Yunusa Abdullahi says:
    3 years ago

    Allah Ya taimaka

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Amin Amin. Mun gode, Malam.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023
Al’amuran Tsaro: Musulmin Duniya Sun Taru A Abuja

Al’amuran Tsaro: Musulmin Duniya Sun Taru A Abuja

August 12, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

September 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.