SHIRIN KATSINAWA DIKKO YA AIKO NI: Jan Hankali Da Ƙarin Haske Ga Umar Tata
Daga Bashir Yahuza Malumfashi.

_______________
Na karanta wani sabon shiri da Alhaji Umar Tsauri, wato Umar Tata Mai Dubu-Dubu ya fito da shi mai taken: “Katsinawa Dikko Ya Aiko Ni.” Ina son in ɗan tofa albarkacin bakina a game da wannan shiri.
Kamar yadda na karanta a shafinsa na Facebook, Umar Tata ya yi bayani dalla-dalla, inda ya ce daga wannan wata zai fara gudanar da shirin, inda a duk wata zai kashe kimanin Naira miliyan 100.
Kamar yadda ya ce, wannan sabon shirin, iri ɗaya ne da wanda ya taɓa gudanarwa, mai taken: ShirIn Ga Kai Ga Fata, lokacin Gwamnatin Masari da ta gabata. Ke nan zai riƙa ba da tallafi da mata da tsofaffi da matasa da ‘yan kasuwa, har ma da tallafi a harkar tsaro da sauransu.
√ Tsokacina:
Umar Tata Idan na fahimce ka, wannan aiki ne kam mai girma kuma babu shakka idan ba gwamnati ce kai tsaye za ta FITAR DA KUƊI ba, to ko #Dangote zai gajiya idan ya ɗauki nufin aiwatar da shi.
Ka ce fa duk wata ana buƙatar a kashe Naira miliyan 100 a shirin. To yallaɓai, daga aljihun wa za a riƙa samun waɗannan adadin kuɗi duk wata? Zakka ce za ka riƙa tattarawa daga attajirai ko kuwa kai za ka riƙa samar da su, KAI TSAYE DAGA ALJIHUNKA? Ko kuwa shi mai girma Gwamna, Malam Dr. Dikko Umaru Radda ne zai riƙa fitar da su daga lalitar gwamnati ya damƙa maka, domin aiwatar da wannan aiki?
√ Ƙalubale:
Idan daga hannun attajirai za ka riƙa lalubo wannan kuɗi, to kana da tabbacin za su riƙa ware Naira miliyan 100 a kowane wata, su damƙa maka ziƙau domin wannan hidima?
Idan kuma daga aljihunka ne za ka riƙa fitar da wannan kuɗi, shin anya za ka iya? Abin da ya sa na yi wannan tambaya shi ne, Naira miliyan 100 a wata, ba ƙananan kuɗi ba ne, ko ga babban attajiri, balle kuma kai.
Idan kuma GWAMNA ne zai riƙa ɗibar wannan daga lalitar gwamnati, ya miƙa maka, to ke nan wata ma’aikata zai buɗe sabuwa daban? Idan haka ne, to za a samar wa Ma’aikatar Jin Ƙai Da Walwala kishiya ke nan?
Alhaji Tata Mai Dubu Dubu, kana da ƙuduri da kuma niyya mai kyau amma anya kuwa ba irin abin nan ne ba na “wayon a ci?” Ka ce fa ba za ka yi takara ba, amma za ka taimaki Gwamna ne. Kana nufin KAMFE ke nan – to ina za a samu wannan kuɗin?
√ Shawara:
Maimakon wannan shiri naka na rarraba kuɗi kai tsaye ga mutane, me zai hana ka taimaka wa mai girma gwamna da shawara, ya saka wannan tsari a gwamnatance, yadda alherin zai shafi kowa da kowa kai tsaye daga gwamnati? Domin a shirin naka, ka yi maganar tallafa wa al’umma ta hanyar sauƙaƙa harkokin sufuri. To, me zai hana a ƙara inganta Hukumar KTSTA? Domin kowa ya san yadda Gwamnati ke taimaka wa al’umma ta wannan ɓangare na sufuri.
Ka yi maganar koya wa matasa da mata sana’o’i da ba da tallafi. Ka manta da cewa akwai makarantu da cibiyoyin koyar da sana’o’i da tallafa wa matasa na gwamnati? Me zai hana Gwamna ya ƙara bunƙasa su, maimakon miƙa maka Naira miliyan ɗari duk wata, domin raba wa wasu tsirarun mutane?
Ka yi maganar inganta harkokin tsaro. Ka mance da cewa Mai Girma Gwama ya ƙirƙiro da Dakarun Community Watch a hukumance? Me zai hana a yi amfani da waɗannan kuɗaɗe duk wata wajen inganta aikinsu da sama masu kayan aiki?
Ita gwamnati, ba a san ta da rarraba kuɗi ga al’umma ba, amma ita mai tsara hanyoyi ne da za su bunƙasa da sauƙaƙa wa al’umma samun rayuwa mai sauƙi da inganci. Don haka, maimakon damƙa wa wasu rukunin mutane kuɗi kai tsaye, kamata ya yi gwamnati ta inganta ma’aikatu da kyautata wa ma’aikata, wajen biyan haƙƙoƙinsu. A inganta asibitoci da kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata. A inganta makarantu da cibiyoyin koya sana’o’i da samar masu da kayan aiki da bunƙasa malamai da biyan su haƙƙoƙinsu. Inganta harkokin noma da manoma.
Idan aka yi haka a gwamnatance, kowa zai amfana kuma GWAMNA ZAI YI FARIN JINI, KOWA YA SO SHI SABODA AIKINSA!
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)












