• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, September 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 9, 2023
in Babban Labari
0
Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

Shugaban Hukumar SEPA, Alhaji Muhammad Kabir Usman, yayin gangamin yashe magudanan ruwa a Katsina

106
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Gangamin yashe magudanan ruwa a Katsina

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi da cewa a daminar bana, wasu jihohi, har da Katsina za su fuskanci annobar ambaliyar ruwa, musamman a cewar ta saboda za a samu kwazarin ruwan sama mai yawa a daminar ta bana.

Kamar yadda hukumar ta sanar, ta ce a hasashenta, jihohi 14 da garuruwa 31 ne za su iya samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. Hakan zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli, a cewar gargaɗin.

Kamar yadda sanarwar ta gabata, a Jihar Katsina, yankunan Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa ne ake hasashen samun ambaliyar a bana.

Sauran jihohin da hukumar ta zayyana, waɗanda suke fuskantar bazaranar ambaliyar a bana, sun haɗa da Jihar Filato, a yankunan Langtang da Shendam. Sai Kano, yankunan Sumaila da Tudun Wada. A Jihar Sakkwato kuwa, akwai yankunan Shagari, Goronyo da Silame. A yayin da Jihar Delta, yankin Okwe ne abin zai shafa.

A Jihar Kaduna kuwa, garin Kachiya ne ke kan gaɓa. A yayin da a Jihar Akwa Ibom aka ambata yankin Upenekang.

Sauran jihohin sun haɗa da Adamawa (Mubi, Demsa, Song, Mayo-Belwa, Jimeta da Yola). Jihar Kebbi (Wara, Yelwa da Gwandu). Jihar Zamfara (Shinkafi da Gumi). Jihar Borno kuwa, yankin Briyel ne ake hasashen zai samu ambaliya.

A Jihar Jigawa, yankin Gwaram ne aka bayyana, a yayin da Jihar Kwara aka ambata yankin Jebba. A Jihar Neja, akwai yankunan Mashegu da Kontagora.

A Jihar Katsina dai, rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Jihar tana shirin ɗaukar matakan da suka dace, domin tunkarar al’amarin. Ko a makon da ya gabata, Shugaban Hukumar Kula Da Muhalli Ta Jihar Katsina (SEPA) Alhaji Muhammad Kabir Usman sai da ya jagoranci ma’aikata, inda suka yashe magudanan ruwa da kwashe bola da ta toshe su.

Previous Post

Malam Haƙurau

Next Post

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

February 9, 2024
MALAM DIKKO

MALAM DIKKO

September 11, 2026
No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

August 13, 2026
BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

December 23, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78
  • ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
  • SUNANTA UMMU-KHULSUM

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

September 15, 2026
ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.