ABDU SALA MALUMFASHI:
MUN YI RASHIN ƊAN UWA/ABOKI

__________
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Cike da alhini da nauyayyar zuciya, na samu labarin rasuwar ɗan uwanmu kuma abokinmu da muka taso tare a rayuwa, #Abdu_Sala_Malumfashi.
Sala, kamar yadda muke masa lakabi, ya rasu ne a daren jiya Alhamis 23-12-1446 (Hijiriyya), 19-06-2025 (Miladiyya), ba tare da rahoton wata jinya ba.
Allah da ikonsa da rabon mu yi ganawar ƙarshe da shi, domin kuwa kwanaki uku da suka gabata, na haɗu da shi a ƙofar gidan marigayi Alhaji Yaro Bakanike, inda muka yi ta wasan barkwanci da shi kamar yadda muka saba, duk lokacin da muka haɗu (kasancewar dukkanmu ba mu zaune a Malumfashi, sai lokacin da muka zo). Ashe ganawarmu ta ƙarshe ke nan.
Marigayi Abdu Sala, babu shakka mutumin kirki ne na gaban sahu. Ni dai a tarayyata da shi, tun muna ƙuruciya, ban taɓa shaidar wani abin assha daga gare shi ba. Mutum ne mai mai haƙuri da wasa da dariya.
Idan Allah ya kai mu ƙarfe 10 na safiyar yau Juma’a, za a yi masa jana’iza a Malumfashi.
Muna roƙon Allah da ya ji ƙan shi da rahama, ya kyautata bayansa. Mu kuma da muka rage, Allah ya sa mu cika da kyau da ingantaccen imani.
AMIN-AMIN-YA-ALLAH
__________












