• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 11, 2025
in Gizago
2
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

A dama, Dokta Bala Shehu ne yake amsar Kambin Karramawa daga Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Alhaji Mukhtar Abdullahi City

113
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
A dama, Bashir Yahuza Malumfashi ne tare da Muhammad Abdullahi Jibson, a yayin gudanar da taron

 

√ Gabatarwa:

Da sunan Allah mai rahama, mai jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, manzon tsira, Annabi Muhammadu (saw).

Bayan haka, wannan bunƙasashen rahoto zai zo ne a sigogi mabambanta. Zai kasance a sigar labari, muƙala, sharhi da tsokaci, dangane da Ƙaramar Hukumar Malumfashi da al’ummarta, musamman ma dangane da kyakkyawan yunƙurin da matasa da shugabanni da malaman addini da attajiri da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da ma’aikata suke gabatarwa ta fuskar bunƙasa yankin da al’ummarsa.

√ Yunkurin Matasa:

A kan haka, aka samu samu zaƙaƙuran matasa suka yunkuri da nufin kafa sabuwar tafiya mai manufa. Tafiyar da za ta zama tsani ko kuma ingizau, wajen samar da dauwamammen cigaba a Malumfashi da kewaye. Waɗannan matasa, sun yi amfani da faffaɗar kafar sadarwa ta soshalmidiya, domin cin ma wannan babban ƙuduri.

Matasan masu kishi na garin Malumfashi, sun yi nasarar shirya gagarumin taro, a ranar Lahadi 12-12-1446 (Hijiriyya), 08-06-2025 (Miladiyya); inda aka samu halartar kusan duk wasu masu ruwa da tsaki ko wakilansu a cikin al’umma. Rukunnan mutanen sun haɗa da sarakai, masu mulki, attajirai, ma’aikata, jami’an tsaro da matasa maza da mata.

√ Taro Ya Yi Armashi:

Taron, wanda ya gudana lami lafiya, an kira shi da sunan Malumfashi Facebook Connect, tare da taken “Mu Haɗu, Mu Gana, Domin Tafiya Tare Kuma Mu Tsira Tare.” Masana sun baje kolinsu, ‘yan siyasa sun baza haja, shugabanni sun ba da jagora, kamar kuma yadda makaɗa da mawaƙa suka nishaɗantar.

Teburin Manyan Baƙi, a zauren taron

√ An Karrama Hadiman Al’umma:

Wani babban abin burgewa da yabawa da wannan taron shi ne, yadda aka zaƙulo wasu jajirtattu kuma nagartattun mutane da suke hudimta wa al’umma, aka karrama su da kambin yabo. Wannan zai ƙara masu ƙaimi da himma, domin su ci gaba da wannan aiki na gina al’umma.

Wasu daga cikin waɗanda aka karrama sun haɗa da Injiniya Muntari Sagir, Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson), Injiniya Tukur Tingilin, Malam Haruna Musa Rugoji, Dokta Bala Shehu da Kabir Malumfashi (KB Lamah).

Sauran sun haɗa da Abdulrahim Sallau Maƙauraci, Ɗandattijo Karfi, CSP Bello, DPO na Malumfashi, Alhaji Sanusi Maiwada, Babangida Usman Hada da Alhaji Yakubu Wada da kuma sauransu. (A rahotannin da za su biyo baya, za mu bi su ɗaya bayan ɗaya, mu zayyano irin ƙoƙarinsu da gudunmawar da suke ba al’ummar Malumfashi da kewaye).

√ Jagororin Shirya Taron:

Shin su wane ne jajirtattun matasa kuma ƙashin bayan shirya wannan taro mai albarka? Malam Yahaya Bawa, shi ne Shugaba, a yayin da Malam Isma’il DD ne Sakataren; sai kuma Malam Jibril Aliyu Datti, a matsayin Sakatare na biyu. Malam Mas’ud Sagir shi ne Ma’aji, inda shi kuma Malam Umar Maihaja ya kasance Shugaban Tsare-Tsare. Akwai Abdul’aziz Sardaunan Matasan Galadima, wanda shi ne Shugaban Gudanarwa da Walwala. Shi kuwa Abdullahi Saleesu, shi ne Jami’in Hulɗa da Jama’a. Haka kuma Ambasada Ibrahim Jaji, shi ne Jami’i Mai Gabatar da Taro.

Sama (H-D): Jibril A. Datti, Yahaya Bawa da Mas’ud Sagir. Ƙasa (H-D): Abdul’aziz Sardauna, Ibrahim Jaji, Umar Maihaja, Isma’il DD da kuma Abdullahi Saleesu

Babu shakka, waɗannan mutane sun cancanci yabo, musamman yadda suka yi tsayin daka domin ganin taron ya tabbata cikin lumana, da kuma ganin cewa taron shi ne irinsa na farko a garin Malumfashi. Muna fatan a baɗi, idan Allah ya kai mu, za a samu babbar nasarar taron fiye da na bana.

A tarbi rahoto na gaba, domin ci gaba da kawo bayanai da sharhin yadda taron na bana ya gudana dalla-dalla, jawabai, mukaloli da ƙasidun da aka karanta a yayin taron.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

Next Post

TSAKANIN IRAN DA ISRA’ILA: ANNABI (SAW) YA YI GASKIYA

Related Posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)
Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI
Gizago

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)

February 20, 2026
Next Post
TSAKANIN IRAN DA ISRA’ILA: ANNABI (SAW) YA YI GASKIYA

TSAKANIN IRAN DA ISRA'ILA: ANNABI (SAW) YA YI GASKIYA

Comments 2

  1. Idris Aminu malumfashiii says:
    9 months ago

    Masha Allah,Allah yakara hada kayunanmu domin cigaban garinmu me albarka malumfashi dakuma wannan jarida ta taskargizago domin tana wayarda kan’al’umma tabangarori dayawa Allah yaqara jagoranci yayanmu Bishir Yahuza malumfashi.Inama kowa fatan alkhairi

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      9 months ago

      Ma sha Allah. Muna matukar godiya da wannan kwarin gwiwa da aka ba mu. Allah saka da alheri. Wasallam.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

August 18, 2023
Na Yi Zaton Gwamna Badaru Ɗan Izala Ne

Na Yi Zaton Gwamna Badaru Ɗan Izala Ne

July 3, 2023
SASSANYAN AMINCI (4)

SASSANYAN AMINCI (4)

September 11, 2025
Ruhin Bukar Usman

Ruhin Bukar Usman

May 11, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.