Tarihin Sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya Manjo-Janar Waidi Shaibu
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Major Janar Waidi Shaibu, DSS DSO(LR) FTAM psc fdc(+) CM FCM FCMH MSS MA MNIM, shi ne sabon Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya. An haife shi a ranar 18 ga Disamba, 1971 a Ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi. Ya samu shiga Makarantar Tsaro ta Najeriya (Nigerian Defence Academy – NDA), Kaduna, a matsayin ɗan ajin 41 Regular Course a shekarar 1989, kuma aka ba shi muƙamin Second Lieutenant a rundunar Armour Corps ta Sojojin Ƙasa a ranar 17 ga Satumba, 1994.
Janar Shaibu soja ne mai ilimi sosai kuma ƙwararre a fannin kimiyya da dabarun tsaro. Ya samu digiri na farko a fannin Mechanical Engineering daga NDA, a 1993. Sannan ya karanci Ilmin Gudanar da Harkokin Jama’a (Public Administration) a matakin difloma a Ghana Institute of Management and Public Administration. Haka kuma yana da digiri na biyu a fannin Ilimin Gudanar da Harkokin Jama’a daga Jami’ar Calabar da kuma digiri na biyu a fannin Nazarin Dabarun Tsaro (Strategic Studies) a Jami’ar Ibadan. Bugu da ƙari, yana da digiri na biyu a fannin Tsaro da Dabarun Soja (Security and Strategic Studies) daga National Defence University, Washington D.C., Amurka.
Ya halarci Harvard Kennedy School of Government, inda ya yi karatu a kwas ɗin “Leadership for the 21st Century: Chaos, Conflict and Courage.” Haka kuma ya samu takardar shaidar ƙwararru a fannin Jagoranci da Tsare-Tsare (Applied Leadership and Strategy) daga National Productivity Senior Executive Programme. Yanzu haka yana cikin karatun Digirin-Digirgir (PhD) a fannin Strategic Studies a Jami’ar Ibadan.
A tsawon aikinsa na soja, Janar Shaibu ya halarci darussa da horo da dama a gida da ƙasashen waje. Ciki har da: Young Officers Course (Armour) a Makarantar Sojojin Tanki (Bauchi, 1995); Young Officers Course (Infantry) a Jaji (1996); Company Amphibious Operation Course a Calabar (1997); Platoon Commanders Course (Armour); Communication Instructors Course (Armour); Junior da Senior Staff Courses; Company da Battalion Commanders Courses; da kuma wasu ƙarin horo na musamman a fannin Defence Management and Counter-terrorism a Kenya da Amurka. Ya kuma halarci Counter Terrorism Fellows Programme a College of International Security Affairs, Washington D.C. (2017), wanda ya ƙara masa ƙwarewa sosai a fannin dabarun shugabanci da tsare-tsaren ayyukan soja.
A fagen aiki, Janar Shaibu ya taka rawa sosai a cikin manyan ayyukan tsaro na cikin gida da na ƙasashen waje. Ya halarci Operation HARMONY, BOYONA, ZAMAN LAFIYA, LAFIYA DOLE, TURA TA KAI BANGO, HAƊIN KAI, DESERT da LAKE SANITY. A ƙasashen waje, ya yi aiki a African Mission in Sudan, United Nations Mission in Liberia, da kuma Nigeria’s Foreign Training Assistance Mission to Liberia, inda ya nuna ƙwarewa da ƙwazo wajen shugabanci da aiki cikin ƙwarewa.
A lokacin aikinsa, ya riƙe muƙamai da dama masu muhimmanci, ciki har da:
– Platoon Commander, 245 Recce Battalion
– ADC ga General Officer Commanding 3 Division
– GSO II Operations, Army Headquarters
– Principal Staff Officer/Military Assistant ga Chief of Staff, Armed Forces of Liberia
– Company Commander, 242 Recce Battalion
– Chief of Staff, 23 Brigade Headquarters, Yola
– Chief Instructor, Nigerian Army Armour School
– Director Coordination and Directing Staff, National Defence College, Abuja
– Commander, 21 Special Armoured Brigade, Bama
– General Officer Commanding (GOC) 7 Division/Commander Sector 1, Operation HADIN KAI.
Ya kuma yi aiki a matsayin Acting Chief of Training (Exercises and Training) a Army Headquarters, Director of Defence Administration a Defence Space Administration, da Theatre Commander, Joint Task Force (North East) Operation HAƊIN KAI. Kafin naɗinsa a matsayin Babban Hafsan Sojojin Kasa, shi ne Director of Armour Research a Nigerian Army Heritage and Future Centre.
Janar Shaibu soja ne da aka girmama da lambar yabo da kyaututtuka masu yawa ciki har da:
– Distinguished Service Star (DSS)
– Distinguished Service Order (LR)
– Foreign Training Assistance Medal (FTAM)
– Pass Staff College (psc)
– Fellow National Defence College (fdc+)
– Command Medal (CM)
– Purple Heart Medal don ayyukan yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas
– Field Command Medal (FCM)
– Field Command Medal of Honour (FCMH)
– General Operations Medal (GOM)
– Defence Operations Medal (DOM).
Shi kuma memba ne na Nigerian Institute of Management (MNIM).
A wajen aikinsa, Janar Shaibu mutum ne mai son karatu, tattaki da safe da kuma yin tunani mai zurfi. Ya yi aure, kuma Allah Ya albarkace shi da ‘ya’ya.
_______________













