TUNAWA DA BASHIR YAHUZA MALUMFASHI A CIKAR SA SHEKARA 58 – MAI TUNZURA ALKALAMI, MAI ZABURAR DA ZUCIYA ko
Daga Jibrin Yusuf Kaila
A yau, cikin farin ciki da godiya, muna taya ɗaya daga cikin fitattun jaruman adabin Hausa murnar zagayowar ranar haihuwarsa – Bashir Yahuza Malumfashi – wanda ya cika shekara 58 a doron duniya. Ba wai kawai marubuci ba, ba kawai ɗan jarida ba, amma murya ce da ta tayar da hankulan matasa da dama su rungumi rubutu da cikakken girmamawa.
Ni da kaina zan iya cewa, shi ne madubina na farko a fagen rubuce-rubuce. A lokacin yana aiki a ma’aikatan jaridar Aminiya, yana wallafa labarai da sharhi da rubuce-rubuce masu jan hankali, wadanda ke ɗaukar zuciya, suna zaburar da rai. A lokacin da nake fara jin niyyar zama marubuci, rubuce-rubucensa su ne suka zame mun allurar zabura – suka motsa ni, suka gina sha’awa a cikin raina, har na ɗauki alkalami da takarda da gaske.

Yanzu kuwa, Bashir Yahuza Malumfashi ya ci gaba da barin sawu a duniyar adabi da kafafen zamani ta hanyar gidan jaridar sa na intanet mai suna Taskar Gizago. Wannan shafi ba kawai wajen yada labarai ba ne, amma ya zama wata taska ta hikima, ilimi, da al’adu. Rubuce-rubucensa na yau da kullum a wannan dandalin suna ci gaba da gina al’umma, suna ilmantar da masu karatu, suna kuma tuna wa da muhimman darussa na rayuwa.
A cikar sa shekara 58, muna cewa: Kai haske ne, kai tunzura ne, kai ginshiƙi ne ga marubutan Hausa. Mun gode da irin gudummawar da ka bayar, muna fatan Allah Ya ƙara maka lafiya, basira, da ikon ci gaba da haskaka zukatan mutane da kalmomin ka masu armashi.
Bashir Yahuza Malumfashi, kai gwanin gwanaye ne, mai sharhi, mai fasaha, kuma mai gina al’umma da rubutu. Allah Ya ƙara maka shekaru masu albarka.
Marubuci
Jibrin Yusuf Kaila
15 May 2025













