• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

ILLOLI DA MATSALOLIN DA ƘUNGIYOYI DA ƘUNGIYANCI KE HAIFAR WA MUSULUNCI DA MUSULMI

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 31, 2025
in Addini
3
ILLOLI DA MATSALOLIN DA ƘUNGIYOYI DA ƘUNGIYANCI KE HAIFAR WA MUSULUNCI DA MUSULMI

Musulunci Ɗaya Al'umma Ɗaya

35
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ILLOLI DA MATSALOLIN DA ƘUNGIYOYI DA ƘUNGIYANCI KE HAIFAR WA MUSULUNCI DA MUSULMI

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025
Musulunci Ɗaya Al’umma Ɗaya

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Allah Ka ƙara tsira da aminci ga fiyayyen talikai, cikamakin annabawa da mursallai, Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Bayan haka, wannan sharhi ne da tsokaci da na ƙuduri aniyar gabatarwa, domin bayyana fahimtata da tsinkayena game da yadda ƙungiyoyin addini da ƙungiyanci ke kassara addinin Musulunci da rarraba kan Musulmi. Haka kuma, manufata ce da wannan tsokaci, in yi nasiha da tunasarwa ga ni kaina da ɗaukacin al’ummar Musulmi da mu farka, mu kawo gyara, mu kawo ƙarshen ƙungiyanci, mu zama Musulmi na ƙwarai masu son juna, a bisa Kalma Ɗaya – لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهُ مُحَمَّدٌ رَسُولُ ٱللَّٰهِ‎

•••

Da farko dai ya kamata mu tuna kuma mu fahimci cewa, Allah (swt) ya gina Musulunci ne guda ɗaya kuma ya ɗora shi bisa hanya ɗaya. Sannan kuma ya nemi Musulmi da mu gudanar da shi cikin HAƊIN KAI da ƙaunar juna, a ƙarƙashin lema ɗaya ba tare da rarrabuwa cikin ƙungiyoyi da firƙoki ba.

Allah Ya faɗa a ‘Alkurani mai girma – Al-Imran (Sura ta 3, Aya ta 103), yana cewa:

وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعٗا وَلَا تَفَرَّقُواْۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ كُنتُمۡ أَعۡدَاۤءٗ فَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم بِنِعۡمَتِهِۦٓ إِخۡوَٰنٗا وَكُنتُمۡ عَلَىٰ شَفَا حُفۡرَةٖ مِّنَ ٱلنَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنۡهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Ma’ana: “Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi maku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haɗa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo ‘yan uwan juna a sakamakon ni’imarsa, a da kuma kun kasance a kan gaɓar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana maku ayoyinsa don ko kwa shiriya.” (Sadaƙallahul Azim).

Haka kuma, an samo daga Manzon Allah (saw) ya ce, Musulmi ɗan uwan Musulmi ne. Ya ce Musulmi da Musulmi kamar katanga ce, kowane sashi yana ƙarfafa sashin ɗan uwansa.

Daga wannan aya da hadisi masu albarka da suka gabata, Musulunci na nufin TURKE ƊAYA wanda ya killace ɗaukacin Musulmi a inuwa ɗaya. Ma’ana dai ana son Musulmi mu kasance UMMA ƊAYA, tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Zama a turken Musulunci ɗaya ni’ima ce babba, alhali rarrabuwa cikin ƙungiyoyi fitina ce babba, wacce za ta haifar da rarrabuwar kai da haddasa gaba da ƙiyayya da faɗa juna.

Bari mu koma baya cikin tarihin Musulunci tun da farko: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda shi ne Allah Ya aiko da shiriyar Musulunci, ya yi zamaninsa gaba ɗaya wajen jaddada Musulunci ɗaya da al’umma ɗaya. Ya yi nasara ne ta hanyar bunƙasa haɗin kai tsakanin mabiyansa. Ko kaɗan bai bari mabiyansa sun rarrabu ba, ya ɗinke duk wata ƙofa da za ta haifar da gaba da rarrabuwar kan al’ummarsa. Kuma a haka ya bar mana MUSULUNCI GUDA ƊAYA bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnarsa, sannan ya umurce mu da mu ɗabbaƙa sunnarsa wajen gudanar da addininmu da rayuwarmu gaba ɗaya.

Sahabban Manzon Allah (saw), KHULAFA’UR RASHIDUNA – Abubakar, Umar, Usman da Ali (Allah Ya ƙara masu yarda), har ma da waɗanda suka biyo bayansu da shiriya, sun tsaya ne a cikin MUSULUNCI ƊAYA, bisa haɗin kai da juna. Duk kuwa da cewa an samu saɓanin fahimta a tsakaninsu, amma dai ba su bari wannan ya RABA KAN TSARIN MUSLUNCI GUDA ƊAYA BA – ma’ana, su da kansu, ba su ƙirƙiri ƙungiyoyi a Musulunci ba. A zamanin da suke raye da juna, duk girman saɓaninsu, a cikin Musulunci ɗaya suka tafiyar da rayuwarsu, bisa fahimtar Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (saw).

A tarihi, Musulmi da Musulunci sun fara samun matsala ne bayan da suka fara rarrabuwa ta hanyar ƙungiyoyi da firƙoƙi. Wanda kuma tuni Allah da Manzonsa suka yi hani da haka, kamar dai yadda muka gani a Alkur’ani, Sura ta 3, aya ta 103, kamar kuma yadda muka gani a hadisai da dama na Manzon Allah (saw).

Ƙungiyanci a Musulunci ya taimaka wajen kawo rarrabuwar kai da zaizayewar izza da muhibbar Musulmi da Musulunci. A sakamakon haka, Musulmi sun koma yi wa ƙungiya da shugabannin ƙungiya hidima da bauta, ba Musulunci ba.

Misali, Idan wani al’amari ya zo, ɗan Izala zai kalle shi da fuskar ƙungiyarsa tukunna. Haka shi ma ɗan Ɗariƙa ko ɗan Shi’a ko ɗan Ƙur’aniyyun. Ke nan sai mutum ya fara kare muradun ƙungiya, kafin ya kare na Musulunci. Ke nan babu ruwan ɗan Izala da abin da ya samu ɗan Ɗarika ko ɗan Shi’a ko ɗan Haƙiƙa da sauransu.

A tsarin Ƙungiyanci, duk abin da shugaban ƙungiya ya kawo, koda ya saɓa wa Musulunci, mabiya za su amshe shi, su kare shi. Idan ya yi kuskure ko ya bijiro da son zuciyarsa, haka za su bi shi bisa son rai, saboda ƙungiyanci.

A tsarin Musulunci na gaskiya, idan wata musiba ta shafi wani Musulmi, wajibi ne kowane Musulmi ya tausaya, ya jajanta. Amma a tsarin Ƙungiyanci, idan musiba ta samu mutum, ‘yan ƙungiyarsa kaɗai za su taya shi jaje da alhini, alhali sauran ‘ya’yan wasu ƙungiyoyin sai su yi ta murna da dariya. Misali, a lokacin da ibtila’i ya faru da Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, aka yi masa kisan gilla, wasu ƙungiyoyin murna suka riƙa yi. Haka ma a lokacin da aka kashe Sheikh Albany, waɗanda ba ‘yan ƙungiyarsa ba, ba su nuna wata damuwa ba – domin a ganin su, tun da ba ɗan ƙungiyarsu ba ne, to babu ruwansu. Haka ma a lokacin da aka samu saɓani tsakanin ‘yan Shi’a da Gwamnatin Jihar Kaduna, har ta kai ga wasu ‘yan Shi’a suka rasa rayukansu, a yayin da shi kuma shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa suka samu raunuka, ‘yan Shi’a kawai aka bari da alhini da jimami, a yayin da sauran ƙungiyoyin Musulunci suka yi ta murna.

Haka kuma idan wani alheri ya samu wata ƙungiya ko ɗan ƙungiyar, su kaɗai za su yi murna, alhali sauran ‘yan ƙungiyoyi za su yi ta baƙin ciki da wannan. Wanda kamata ya yi a tsarin Muslunci, idan Musulmi ɗaya ya samu wani abin alheri a Najeriya, to sauran duk Musulmin duniya, kamata ya yi su taya shi murna, ba su yi baƙin ciki ba.

Sai dai a yau, lamarin Ƙungiya da Ƙungiyanci sun kassara haɗin kan Musulmi. A yanzu al’ummar Musulmi a Najeriya babu shugabanci ɗaya. A yau, babu wani tsari guda ɗaya da yake jagorancin Musulunci da Musulmin Najeriya. A yau, babu wani shugaba guda ɗaya da zai yi magana ko ya ba da umurni, ɗaukacin Musulmi su yi masa biyayya gaba ɗaya. Ɗan ƙungiyar Izala, shugabansa kaɗai yake saurare, shi yake yi wa ladabi da biyayya. Haka shi ma ɗan ƙungiyar Ɗarika ko ɗan Shi’a ko ɗan Haƙiƙa – Babu shugabanci ɗaya, babu ƙaunar juna ɗaya, sai rarrabuwa da gaba da ƙiyayya da juna. Tabbas wannan tsarin ya saɓa da koyarwar Allah da Manzonsa.

Wani munin abin ma shi ne, a halin da ake ciki a Najeriya, Musulmi sun rarraba fiye da ƙima. Hatta a cikin ƙungiyoyin, an sake haifar da wasu ƙungiyoyin – rarrabuwa cikin rarrabuwa. A ƙungiyar Izala, an karkasu gida-gida. Akwai Izalar Kaduna, akwai ta Jos. Akwai ma mabiya Salafiyya. A Ɗarika, akwai ‘yan Haƙiƙa da sauransu. A Shi’a, akwai mabiya Zakzaky, akwai Rasulul A’azam a Kano, akwai wata a Kaduna kuma akwai wasu ‘yan Shi’a da suke biyayya ga shugabansu na Katsina kadai, ba su yin biyayya ga Sheikh Zakzaky. Haka Musulmi ke rayuwa cikin ƙungiyoyi da firƙoƙi.

Aƙalla dai ƙungiya da ƙungiyanci sun haifar wa Musulunci rarrabuwar kai. Sun haddasa gaba da ƙiyayya tsakanin Musulmi. A yau a Najeriya, manyan malamai suna gaba da juna, suna hawa mumbari suna zage-zage da muzanta juna. Rarrabuwar kan Musulmi ta kai ga manyan malamai sun koma kamar ‘yan siyasar jam’iyya, suna adawa da juna. MUSULMI SUN ZAMA ABOKAN GABA DA ADAWA DA FAƊA DA JUNA A NAJERIYA.

TUNASARWA:

Ya kamata al’ummar Musulmi mu sani, babu abin da zai gyara mana addini sai mun koma baya mun bi umurnin Allah da Manzonsa. Sai mun zama tsintsiya ɗaya, sai mun watsar da ƙungiyoyi da ƙungiyanci. Sai mun so juna, mun taimaki juna bisa turba ɗaya. Sai mun yi rayuwar Musulunci kamar dai yadda Musulman farko suka yi. Sai mun bi umurnin Allah da Manzonsa, kamar yadda Ya umurce mu a Alkur’ani, Sura ta 3, Aya ta 103.

Ya Allah Ka sanya mu a shiriyarKa, Ka ƙarfafa dugaduganmu a Musulunci, Ka sa mu dace da daidai, mu cika da imani, Amin!

________________

© Bashir Yahuza Malumfashi, Juma’a 01-08-1446 (Hijriyya), 31-01-2025 (Miladiyya).

Previous Post

SHIRIN GWAMNA ABBA GIDA-GIDA NA RABA TALLAFIN AWAKAN KIWO YANA KAN DAIDAI

Next Post

ENDING BANDITRY AND KIDNAPPING IN THE NORTHWEST: WHETHER DIALOGUE IS THE ANSWER

Related Posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi
Addini

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban
Adabi

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025
Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa
Addini

Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

November 21, 2025
Next Post
ENDING BANDITRY AND KIDNAPPING IN THE NORTHWEST: WHETHER DIALOGUE IS THE ANSWER

ENDING BANDITRY AND KIDNAPPING IN THE NORTHWEST: WHETHER DIALOGUE IS THE ANSWER

Comments 3

  1. Abdulkadir ma'aruf says:
    12 months ago

    Wannan maganar gaskiya ne

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      12 months ago

      Ma sha Allah. Allah ya sa mu dace da daidai, Amin.

      Reply
  2. Amadu yahaya says:
    7 months ago

    Gaskiya ne

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

July 2, 2023
Taron Duniya: Minista ya sha alwashin Nijeriya za ta ɗau nauyin sabuwar makarantar UNESCO a Nijeriya

Taron Duniya: Minista ya sha alwashin Nijeriya za ta ɗau nauyin sabuwar makarantar UNESCO a Nijeriya

November 8, 2023

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

June 30, 2025
Gen. SK Usman Now a Distinguished Knight for World Peace

Gen. SK Usman Now a Distinguished Knight for World Peace

September 22, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.