KANO 2024: Tattaunawa Da Zakaran Gasar Marubuta Balannaji
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A makon nan ne aka gudanar da bikin raba kyaututtuka ga gwarazan da suka lashe Gasar Rubutun Hausa, wacce Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i Ta Jihar Kano ta gudanar a ashekarar da ta gabata (2024). Marubuci, Malam Zubairu Musa Balannaji ne ya lashe gasar, ya zama ZAKARA. A yayin bikin ne aka miƙa masa kyautar Naira dubu ɗari biyar (₦500,000). Wakilinmu ya tattauna da shi, inda ya bayyana tarihinsa da yadda irin farin cikinsa da lashe wannan gasa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
•••••••
TG: Za mu so ka fara da gabatar da kanka, wato tarihinka a taƙaice.
Balannaji: Assalamu alaikum. Sunana Zubairu Musa Balannaji, kuma an haife ni ne a ranar 4 ga watan Satumbar shekarar 1992. Na fara karatuna a Makarantar FEDWA Nursery School. Daga nan na wuce Demonstration Primary school. Bayan na kammala makarantar firamare sai na koma Staff Secondary School da ke cikin F.C.E Kano, inda na fara karatun sakandare; har na kammala a can. Daga nan na sake komawa F.C.E ɗin dai a shekarar 2012, na yi karatun NCE, inda na karanci Ingilishi da Hausa.
TG: Tun yaushe ka fara harkar rubutu kuma me ya ja hankalinka zuwa wannan harka ta rubutu?
Balannaji: Na fara harkar rubutu ne tun ina makarantar firamare. Amma ban samu damar buga littafina na farko ba sai a shekarar 2006. Haka kuma bai kai ga shiga kasuwa ba sai a farkon shekarar 2008.

Abin da ya ja hankalina na fara rubutu kuwa shi ne; na kasance ma’abocin karance-karance tun ina makarantar firamare. Daga baya kuma sai na fara sha’awar ni ma na ga na rubuta nawa na ƙashin kaina. Saboda a wasu lokutan idan ina karanta littafai sai na dinga cin karo da gyare-gyaren da nake jin ina ma ni ne marubucin littafin, da na saka kaza da kaza a ciki, wasu kuma sai na dinga ji a raina da ni ne marubucin littafin da ba zan saka wasu abubuwan da aka saka ba a ciki. Wannan dalilin ne ya ba ni ƙwarin gwiwar cewa to bari na gwada rubuta nawa na ƙashin kaina, na gani ko zan iya. To da haka na fara jagwalgwala rubutu har zuwa yanzu.
TG: Ko za ka bayyana mana sunayen wasu daga littattafan da ka wallafa?
Balannaji: Daga fara rubutuna zuwa yanzu dai na wallafa littatafai guda 22 ne, waɗanda suka haɗa da 1- Zakaran Da Allah Ya Nufa… 2-Ranar Wanka, 3-Ƙarshen Butulu, 4-Haƙƙi, 5-Tasku, 6-Adon Mata, 7-Adon Masoya, 8-Mu Roƙa Da Kanmu, 9-Ingantattun Addu’o’i, 10-Halimatussa’adiyya, 11-Kundin Nishaɗi, 12-Ba Za Ta Saɓu Ba, 13-Ƙanwata, 14-Auren Gayya, 15-Farin Cikin Iyali, 16-Guzurin Uwargida, 17-Jirgin So, 18-Jagoran Masoya, 19-Mowar Mata, 20-Sirrin Mallakar Maigida da sauransu.
TG: Ga shi ka samu nasarar zama zakara a Gasar Rubutu, wacce Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i Ta Jihar Kano ta gudanar. Yaya ka ji da wannan nasara?
Balannaji: Gaskiyar magana, farin cikin da nake ciki a dalilin wannan nasara ba zan iya kwatanta shi ba. Sai dai kawai na ƙara gode wa Allah da Ya zaɓo ni, Ya nufe ni na lashe wannan gasa, wacce a lokacin da na shiga ko a zagayen farko, inda ska tantance labaru 50, ban kawo wa raina cewa labarina zai tsallake ba; bare har na kai ga karɓar kambun na ɗaya. Alhamdu lillahi.
TG: Yaya sunan labarin da ka shiga gasar da shi? Ko za ka ɗan yi mana bayani game da jigon labarin da kuma darussan da yake koyawa?
Balannaji: Sunan labarin da na shiga da shi “Bahaushiyar Al’ada.” Kuma jigon labarin yana magana ne a kan kyawawan al’adun Hausawa na baya da a yanzu muka yi watsi da su, dalilin da ya sanya mu ka tsinci kanmu ke nan a cikin wannan hali da muke ci, muke ta shan wahalar rayuwa. Darussan da suke cikin labarin kuma su ne a yayin rubuta labarin Bahaushiyar Al’ada na fito da yadda a zamanin da Hausawa suke taimakekeniya a tsakaninsu, ta hanyar yin ciyayya da tallafawa duk gidan da aka yi rasuwa; ta hanyar kai musu abinci daga ‘yan uwa da maƙwabta, ba tare da su sun ɗora tukunya ba, da kuma al’adar zaman ajo da ake gudanarwa a yayin biki, wanda ake haɗa wa ango maƙudan kuɗin da zai daɗe yana rayuwa da ,su ba tare da ya tagayyara ba. Da shi kansa tsarin neman auren irin na zamanin baya. Da kuma sauran kyawawan al’adun Malam Bahaushe da suke da muhimmanci a rayuwarmu.

TG: Wace shawara za ka ba marubuta waɗanda ke son shiga irin wannan gasa ta rubutu?
Balannaji: Shawarar da zan ba wa ‘yan uwana marubuta masu sha’awar shiga gasa ita ce; su kasance masu yin bincike da kuma yin rubutu mai inganci a duk lokacin da za su yi kowanne irin rubutu, ko da ma ba na gasa ba ne, ta yadda duk wanda ya karanta rubutun zai san cewa wanda ya rubuta labarin ya san abinda ya ke yi.
Sannan kuma su fahimta da cewa, faɗuwa a gasa kar ya taɓa sarar musu da gwiwa, ya kasance ma shi ne babban abin da zai ƙara musu ƙarfin gwiwa, saboda ita kanta shiga gasar har ka kai matakin tantancewar Alƙalai nasara ce gagaruma. Babban misali a kaina shi ne, na sha shiga gasa daban-daban, wasu na ci wasu kuma na faɗi. Amma tun da nake, faɗuwa ba ta taɓa hana ni shiga wata gasar ba.
TG: Wane kira za ka yi ga gwamnati da al’umma dangane da harkar rubutu da adabi?
Balannaji: Kiran da zan yi ga gwamnati da kuma sauran al’umma, musamman ma waɗanda suke da hali shi ne; ya kamata su dinga ƙarfafar marubuta ta hanyar shirya musu ire-iren waɗannan gasar domin tallafar harkar Adabin Hausa, wanda ya tasar wa durƙushewa saboda mutuwar kasuwar littafi a yankin Arewa da ma ƙasar Hausa baki ɗaya. Su sani cewa marubutan nan wakilan al’ummarsu ne a ko’ina a faɗin duniya, sannan su na bayar da gudunmawa marar iyaka wajen bunƙasa harshen Hausa a faɗin duniya. Da gudunmawar tasu ce ma harshen ya kai matakin da yake kai a yanzu, ta yadda aka san Hausawa a ko’ina a duniya, tare da sanin kyawawan al’adunmu tun na Iyaye da kakanni.












