• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 31, 2023
in Labarai
0
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

14
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta wallafa cikakken bayani kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba a matakin rumfunan zaɓe a zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi a ranar Asabar ta makon gobe.

Related posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026

Hakan ya biyo bayan taron da hukumar ta yi a ranar Litinin domin sake nazarin shirye-shiryen da ta ke yi na zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin uku a ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

A sanarwar da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai Da Ilmantar Da Masu Zaɓe a INEC, Mista Sam Olumekun, ya rattaba wa hannu, hukumar ta ce: “Kamar yadda aka yi a zaɓuɓɓukan baya-bayan nan, ciki har da Babban Zaɓen 2023, hukumar ta wallafa cikakken bayani kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba a jihohin uku a matakin rumfunan zaɓe.

“Haka kuma bayanin ya bada yadda aka rarraba rumfunan zaɓen a Yankunan Ƙananan Hukumomi, Cibiyoyin Rajista ko Mazaɓu, da sunayen rumfunan zaɓen, da alƙaluman lambobin su, da yawan masu zaɓe da su ka yi rajista, da kuma yawan katittikan masu zaɓe da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba.

“Shi ma wani muhimmin abu shi ne, jadawalin ya ba da sunaye da inda rumfunan zaɓe guda biyu da ake da su a Jihar Bayelsa da 38 da ake da su a Imo waɗanda ba su da masu zaɓe da su ka yi rajista.

“Lissafin na jihohin uku ya nuna cewa daga cikin masu zaɓe 1,056,862 da su ka yi rajista a Jihar Bayelsa, mutum 1,017,613 sun karɓi katittikan su, sannan ba a karɓi 39, 249 ba. A Jihar Imo, masu zaɓe da su ka yi rajista su 2,419,922 ne, waɗanda daga cikin su mutum 2,318,919 sun karɓi katittikan su amma 101,003 ba su karɓa ba, yayin da a Jihar Kogi, daga cikin masu zaɓe 1,932,654 da su ka yi rajista, mutum 1,833,160 sun karɓi katittikan su, sannan 99,494 ba su karɓa ba.”

Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin zaɓuɓɓukan da su yi la’akari da cewa duk fa wata ƙuri’a da aka samu a rumfar zaɓe wadda ta haura yawan ƙuri’un da aka karɓa to shaida ce cewar an yi aringizo kenan.

Ta ƙara da cewa za a yi amfani da yawan katittikan zaɓe da aka karɓa wajen lissafa tsarin wanda ke kan gaba.

Previous Post

BABANA

Next Post

Literature in Northern Nigeria: Past, Present and the Future

Related Posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta
Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Next Post
Literature in Northern Nigeria: Past, Present and the Future

Literature in Northern Nigeria: Past, Present and the Future

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

November 26, 2025
BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

September 2, 2025
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

July 10, 2025
A CELEBRATION OF WISDOM

A CELEBRATION OF WISDOM

December 10, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.