• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 28, 2023
in Labarai
0
Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris
7
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

~~~~~~~
JAWABIN MINISTAN YAƊA LABARAI DA WAYAR DA KAI, ALHAJI MOHAMMED IDRIS, A TARON MANEMA LABARAI, DANGANE DA HUKUNCIN SHARI’AR ZABEN SHUGABAN ƘASA DA KOTUN ƘOLI TA YANKE

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026

~~~~~~~

Bayan sallama.

1. Bari in fara da yi maku barka da zuwa wannan taron manema labarai, wanda mu ka shirya bayan hukuncin shari’ar da Kotun Ƙoli ta yanke jiya. Hakan ya kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafen ƙararrakin da aka riƙa shigarwa a kotuna game da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

2. Kotuna dai sun zartas da hukuncin su, shi kuma Shugaban Ƙasa da APC sun yi maraba-lale da wannan nasara da kotunan su ka tabbatar.

3. Mun gode wa kotuna saboda juriyar gudanar da wannan gagarumin aiki, wanda su ka nuna haƙiƙanin sauke nauyin da dokar ƙasa ta ɗora masu, a matsayin su na wurin kai kuka ko ƙorafin da ya shafi zaɓe na ƙarshe a matakan shirya zaɓe a ƙasar nan.

4. Yanzu dai mun wuce maganar shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa, yanzu lokaci ne da za mu tunkari aikin tafiyar da gwamnati ba tare da wani abu ya ɗaukar mana hankali ba.

5. Tabbas wannan babban ƙalubale ne, musamman a wannan lokaci da tattalin arziki ke fuskantar mawuyacin hali, ba a Nijeriya kaɗai ba, har duniya baki ɗaya.

Saboda haka tilas mu taru mu haɗa hannu wuri ɗaya, domin magance wannan ƙalubale da ke tunkarar mu. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a fili cewa shi Shugaban Ƙasa ne na kowane ɗan Nijeriya, ba tare da bambancin yanki, ƙabila, siyasa ko addini ba.

6. Tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga Mayu, ya na ta aiki tuƙuru wajen ƙoƙarin samun nasarar Ajandar Farfaɗo da Nijeriya, wadda ta na daga cikin dalilan sa na kishin zama shugaban ƙasa.

Ya aiwatar da manyan tsare-tsaren da duk da yake dai su na da tsauri sosai, to amma tsaurin na wani taƙaitaccen lokaci ne. Kuma ta haka ne aka gina tubalin girka ƙasaitaccen tattalin arziki, samar da yalwar da kowane ɗan Nijeriya ya cancanci ya samu.

7. Kamar yadda ku ka sani, cire tallafin fetur abu ne ya samo tushe daga Dokar Fetur ta 2021, wadda yanzu ta ke ƙara tanadar wa Gwamnatin Tarayya da Jihohi maƙudan kuɗaɗen da za su riƙa yin ayyukan inganta rayuwa da bunƙasa ƙasa.

8. Sabon tsarin hada-hadar musayar kuɗaɗen waje, an bijiro da shi ne domin toshe ramukan da kuɗaɗe ke zurarewa tsawon shekaru da dama. Hakan kuwa ya na janyo wa gwamnati asarar biliyoyin dala.

9. Waɗannan tsauraran tsare-tsaren sun taru sun yi wa ‘yan Nijeriya rubdugun dukan da su ke jin jikin raɗaɗin tsadar rayuwa, lamarin da Shugaban Ƙasa bai taɓa kauda kai ko yin biris da shi ba.

10. Babu gwamnatin da ta san abin da ta ke yi za ta jefa al’ummar ta cikin halin ƙunci da gangan. Shi ya sa mu ke jaddada cewa wannan hali da ake ciki zai wuce cikin taƙaitaccen lokaci nan gaba. Daga nan sai mu shiga yanayin yalwa da sawaba.

11. A ranar 1 ha Oktoba, 2023, Shugaba Tinubu ya ce, “Tsare-tsaren da aka bijiro da su akwai ƙuntatawa, amma fa sai an sha wuya akan sha daɗi. Ba abin farin ciki ba ne mu riƙa ganin ‘yan Nijeriya na ci gaba da fama da tsadar rayuwar da tuni ya kamata a ce mun wuce wurin. Na yi fatan cewa da ma ba mu tsinci kan mu cikin wannan mawuyacin hali ba. Amma kuma tilas mu ci gaba da juriya domin kafin a sha zuma sai an sha hayaƙi. Gwamnati na ta na bakin ƙoƙarin ta domin sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya tsadar rayuwar da su ke fama da ita.”

12. Gwamnatin Tinubu na ɗaukar dukkan matakan da su ka wajaba domin sauƙaƙe wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da su ke fama da ita a yanzu. Daga cikin hanyoyin akwai:

a. Ƙarin Naira 35,000 kan albashin ma’aikata, har tsawon watanni shida a jere.

b. Kafa Asusun Gina Ayyukan Raya Ƙasa na Jihohi.

c. Ƙaddamar da sayen motoci na masu aiki da gas, domin sauƙaƙa tsadar zirga-zirgar motoci.

d. Sa hannu kan Dokar Ƙarfin Ikon Shugaban Ƙasa har guda biyar, domin inganta harkokin kasuwanci da ƙara wadata kuɗaɗen hada-hadar musayar kuɗaɗen waje.

e. Kafa Kwamitocin Tsarin Kuɗaɗe da Kwamitin Sauya Tsarin Karɓar Haraji. Kuma an rage wa ‘yan Nijeriya yawan haraji.

f. Mu na kusa ga kammala shirye-shiryen fara biyan tallafin Naira 25,000 ga mutum miliyan 15, kuɗaɗen da za a tsittsinka masu a cikin watanni uku.

g. Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin a fitar da metrik tan 200,000 na kayan abinci ga marasa galihu a jihohi 36 da Gundumar Babban Birnin Tarayya domin hakan ya rage tsadar farashin kayan abinci. Sai kuma metrik tan na takin zamani, iri da sauran kayan aikin gona ga manoma.

h. Shirin bayar da lamuni ga ƙanana da matsakaitan masu sana’o’i, wanda Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar ba da daɗewa ba. Za a raba naira biliyan hamsin lamuni ga masu sana’o’i miliyan 1 daga yanzu zuwa Maris, 2024. Sai kuma naira biliyan 75 da za a bai wa masu masana’antu da sauran su.

i. Mun ƙaddamar da shirin 3MTT domin horas da dabarun fasaha ga matasa miliyan 3 daga nan zuwa 2025.

j. Shirin NATEP wanda aka ƙaddamar, domin samar wa matasa miliyan 1 ayyuka nan da shekaru 5.

k. Nan da 2024 za mu fara shirin bai wa ɗalibai rance.

13. Wasu daga cikin waɗannan shirye-shirye ana kan aiwatar da su, ko kuma za a gudanar da su tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.

14. Waɗannan fa daban ne, domin su ma jihohi su na ta bijiro da nasu tsare-tsaren daban-daban, domin amfanar jama’a.

15. Ba za mu taɓa sauka daga kan turbar nauyin da ke kan mu a matsayin Gwamnatin Tarayya ba, amma ya na da muhimmanci mu bayyana cewa ba za mu iya cimma waɗannan nasarori mu kaɗai ba. Jihohi da ƙananan hukumomi su ma su na da gagarumar rawar da za su taka.

16. A wannan makon yayin Taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), a ranar Litinin, an amince da wasu kuɗaɗen da za a bai wa jihohi domin su kai ga nasarar wasu tsare-tsare, ciki har da samun damar cimma nasarar ilmantar da ‘yan mata.

17. Ana kan aikin tsare-tsaren Kasafin Kuɗi na 2024. Saboda haka ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalin su. Wannan kasafin kuɗin na farko na Gwamnatin Tinubu zai kasance na farko wanda kacokam ya maida hankali kan samar da bunƙasar tattalin arziki da samun yalwa ga kowa da kowa.

18. Ina ƙara yin kira ga ‘yan Nijeriya da mu ci gaba da haƙuri, ƙasar nan za ta warware, ta bunƙasa ba da daɗewa ba.

19. Mu na fatan samun ƙasaitacciyar ƙasar da kowa zai amfana da cin moriyar bunƙasar ta.

20. A namu ɓangaren, za mu ci gaba da gudanar da aiki tsakani da Allah, yadda al’umma ba za su riƙa tababa ko shakkun gaskiya da sahihancin bayanan da mu ke yaɗa maku na aikace-aikacen gwamnati ba.

21. Zan rufe jawabi nawa da wani kalami da Shugaba Bola Tinubu ya yi, bayan bayyana hukuncin Kotun Ƙoli, inda ya ce: “Ajandar Farfaɗo da Nijeriya zuwa ƙasaitacciyar ƙasa ta ƙara samun karsashi. Zan ci gaba da yin aiki ba dare ba rana domin gina ƙasar da ta cancanci nagartattun mutane irin ɗaukacin mu baki ɗaya ke fatan samu.”

22. A nan, ni ma ina ƙara gode maku da samun damar halartar wannan taron manema labarai.

~~~~~~~

Alhaji Mohammed Idris, fnipr
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai
Abuja, Nijeriya
27 ga Oktoba, 2023

~~~~~~~

Previous Post

PHOTO GALLERY: Hajia Rabi Attends UNICEF Training

Next Post

GASAR ƘIRƘIRA: Pharmacist Isa Ya Ci Kyautar Naira Miliyan 10 Daga Pharm Musa A. Bello

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Next Post
GASAR ƘIRƘIRA: Pharmacist Isa Ya Ci Kyautar Naira Miliyan 10

GASAR ƘIRƘIRA: Pharmacist Isa Ya Ci Kyautar Naira Miliyan 10 Daga Pharm Musa A. Bello

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

October 9, 2025
Niger First Lady calls for unity in the state

Niger First Lady calls for unity in the state

September 9, 2023
The World Converge and Pay Final Respects to Late President Muhammadu Buhari at Daura Burial

The World Converge and Pay Final Respects to Late President Muhammadu Buhari at Daura Burial

July 16, 2025
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.