Sojoji Sun Bankaɗo Kamfanin Ƙera Bindigogi A Kafanchan
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
~~~~~~~
A ƙoƙarin Rundunar Sojojin Najeriya na daƙilewa da kassara dukkan ‘yan ta’adda da masu ɗaukar nauyinsu, a wani shiri na musamman mai taken “Operation Safe Haven, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Runduna ta Uku, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, sun bankaɗo wani ɓoyayyen kamfani da ake ƙera bindigogi a Kafanchan, Ƙaramar Hukumar Jema’a, Jihar Kaduna.
A wata takardar manema labarai da ta fito daga ofishin Jami’in Watsa Labarai na Shirin “Operation Safe Haven” Kyaftin Oya James, wannan nasara da sojojin suka samu, ta biyo bayan binciken sirri na tsawon mako ɗaya, inda suka kai ga kama wani ɗan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, mai suna Napoleon.
“Wanda aka kama, ya amsa laifinsa, inda daga bisani ya jagoranci sojojin zuwa wani ɓoyayyen kamfani, inda wani mai suna Monday Duniya ke ƙerawa da sayar da bindigogi iri-iri. Ya ce ya kwashe shekara biyar yana wannan sana’a da ke haddasa rikice-rikice da kashe-kashen jama’a a jihohin Kaduna da Filato” inji Kyaftin Oya.
Ya ƙara da cewa, a yayin binciken ɓoyayyen kamfanin a daren Juma’a zuwa safiyar jiya Asabar, an gano samfurin bindigogi guda 22 da suka haɗa da fistol-fistol da AK 47 da aka kwaikwaya da alburusai da tukunyar gas da sauran kayan aikin ƙereƙere.
Haka kuma an gano tare da ƙwato yunifom na ‘yan sanda da wando da hular kwano na sojoji da layu da guraye da sauran kayayyaki. Sai dai kuma jagoran ‘yan ta’addan (an sakaya sunansa) ya tsere amma rundunar ya sha alwashin kamo shi.
A yayin da yake yaba wa sojojin da suka yi wannan babban aiki, tare da gode wa al’umma bisa goyon bayan da suke ba jami’an tsaro, Janar A.E Abubakar ya sha alwashin kamo jagoran da ya tsere da sauran yaransa, domin su fuskanci hukunci. Ya gargaɗi duk wasu ‘yan ta’adda da masu ɗaukar nauyinsu, da su tuba, su rungumi rayuwar lumana bisa doka.
~~~~~~~













