An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi
An samar da sasanci tsakanin fitaccen malamin nan mai wa’azin Musulunci a Jihar Bauchi, Sheikh Abdul’aziz Tutsen Tanshi da Gwamnatin Jihar Bauchi.
Wannan sasanci da shiga tsakani sun biyo bayan yadda Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Umaru Fintiri ya jagoranci shugabannin Kungiyar Izala wajen kai wa takwaransa na Jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammad ziyara game da taƙaddamar da ke tsakaninsa da Sheikh Idris Abdul’aziz din.
Gwamna Fintiri ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shi da Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe da kuma Sheikh Abdulwahab Kano, sun kai ziyarar ce a ƙoƙarinsu na “kawo ƙarshen shari’ar da ake yi wa Sheikh Dutsen Tanshi,” in ji Fintiri.
Kamar yadda ya bayyana, ya ce: “Ina matukar godiya ga Gwamna Bala Mohammed, bisa fahimtarsa da hikimarsa wajen ji daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da manufar samar da zaman lafiya.”
A nasa ɓangaren, Gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewa addini abu ne mai sammatsi da ya kamata mutane su kula. Ya kuma yaba wa malaman bisa fahimtarsa da kuma Dakta Idris Abdul’aziz da suka yi.













Rikicin Dr. Idris Dutsen Tanshi da gwamnatin Ƙaura da yanzu aka fara..!
Don Dr. Idris bai Haƙura ba, kuma bai janye duk korafin sa ga gwamnatin Bala ƙaura ba.
Allah dai ya kyauta 🤲🤲
Amin Amin Ya Allah.