• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TAURARON GIZAGAWA: M.K. ADAM GOMBE

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 7, 2023
in Gizago
2
TAURARON GIZAGAWA: M.K. ADAM GOMBE

M.K. Adam Gombe

100
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Gizago

Malam M.K. Adam Gombe, shi ne Tauraron Gizagawa a wannan lokaci. Shi ne mai Lambar Gizago GZG-027- GMB.

Related posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026

Wane Ne M.K. Adam Gombe?
Sunansa Muhammad Kabir Adamu. An haife shi a garin Kumo, Ƙaramar Hukumar Akko da ke Jihar Gombe, shekaru hamsin da suka gabata.
Ya yi karatun Islamiyya da na Boko. A halin yanzu yana kasuwanci ne, kamar kuma yadda yake sana’ar noma da kiwon kaji da sauran tsuntsaye. A cikin Jihar Gombe yake zaune kuma a nan yake sana’arsa.

Matsayinsa A Ƙungiyar Gizago:

Malam M.K. na ɗaya daga cikin mutane na farko da suka kasance cikin Gizagawan Zumunci. Hasali ma, yana daga cikin mutane uku na farko da suka ba da shawarar kafa wannan ƙungiya

Jajirtacce shi a dukkan lamuran Gizagawa. Dalili ke nan ma ake kiran shi da laƙanin Agogo Sarkin Aiki. Shi ne ma Sakataren ƙungiyar na farko a lokacin da aka kafa ta. A yau kuwa shi ne Shugaban ƙungiyar na ƙasa. A yau ya shafe sama da shekara 6 yana jagorancin Gizagawa.

Ra’ayinsa Game Da Zumunci:

“Gaskiya sai dai in ce Alhamdulillah! An yi zumunci, an haɗa zumunci kuma ana kan zumunci, za kuma a ci gaba da zumunci har zuwa ƙarshen iya wa’adin rayuwata. Fatana Allah Ya karɓa mana, Ya tara mu a ladan baki ɗaya.”

Tsokacinsa Game Da Gizago:

M.K. tare da Uban Gizagawa, Marigayi Mahmoon Baba Ahmad a taron Gizago

“Wai! Wannan amsar ai ba za ta ɗauki wannan filin ba, sai dai na taƙaita bayani. A yanzu dangi na kusa da na nesa, da sun ji na ce ba na gari, mafi akasari cewa suke ka tafi aikin Gizagon naku ne? Ka ga ke nan wannan yana nufin Gizago ta shiga lungu da saƙo na ‘yan uwana da abokaina. Akwai ma waɗanda suke kira na da Gizago.

“A ɓangaren ita kanta Ƙungiyar Gizago kuma, babu abin da zan ce sai son barka, domin idan na ɗaga waya na ce ga abin da za a yi mini a jihohin Arewa da wasu daga cikin jihohin Kudancin ƙasar nan, babu ɓata lokaci ake aiwatar mini da shi. Wannan na samuwa ne duk albakacin wannan ƙungiyar.”

Shawara 5 Ga Gizagawa:
1-Ku kasance masu yi don Allah.
2-Ku riƙa kyautata zato a junanku.
3-Ku zamo masu haƙuri.
4-Ku riƙe zumunci da kyau.
5-Ku za mo masu juriya da dauriya, domin duk abin da za a yi sai an daure an jure. Wannan shi ne dalilin da ya kai mu sama da shekaru 15 muna tare cikin zumunci.

Previous Post

Yau Maulidin Safinah Saleeth Adam

Next Post

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

Related Posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana
Gizago

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

September 5, 2026
Next Post
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

Huɗubar Jumu'a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

Comments 2

  1. Muhammad Kabir mk Adam says:
    3 years ago

    Masha Allah Allah Ya karawa wannan kafa albarka

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Madalla da Shugaban Gizagawa. Agogo Sarkin Aiki. Allah ƙara zumunci.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

October 14, 2023
Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

March 23, 2026
BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

December 13, 2023
Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

October 23, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.