D

aga Bashir Yahuza Malumfashi
A yau Juma’a, 12 ga Zulhijja, 1444 (Hijriyya), 30 ga Yuni, 2023 (Miladiyya), Limamin Masallacin Eriya Malumfashi, Sheikh Mutawakkilu Mustapha ya gabatar da huɗuba da mai taken “Ka Yi Wa Kanka Hisabi Kafin A Yi Maka.”
Bayan godiya ga Allah da salati da yabo ga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ya ja hankalin al’umma kai tsaye dangane da yi wa kai ƙididdiga da hisabi, domin tunkarar rayuwar gobe ƙiyama.
Ya ce muna watan ƙarshe na shekarar Musulunci, don haka kowa ya waiga baya, ya tantance da ƙididdige abin da ya aikata a cikin shekarar, na alheri ko akasinsa. Idan na alheri ka aikata sai ka gode wa Allah kuma ka ɗauri aniyar ninka aikata su a shekara ta gaba idan da rabo. Ayyukan da ka aikata na kuskure, marasa kyau, sai ka tuba tare da nadama, da niyyar guje aikata haka a gaba.
Malam ya tunatar da al’umma cewa zaman duniya dai iyaka gare shi, domin akwai mutuwa. Kasancewar Allah Ya sanar da Manzonsa Muhammadu (saw) cewa shi mai mutuwa ne kuma zai mutu. Don haka, mutum ya sani cewa dole zai mutu, tun da mai daraja, ɗan gatan Allah ma ya mutu. Ke nan ya kamata mutum ya zama mai tuba daga ayyukan zunubbansa, domin kowane lokaci, mutuwa na iya zuwa gare shi.
Malam ya ce shi Hisabi kala biyu ne, zai riƙa yi a kansa. Na farko, kafin mutum ya aikata komai, ya yi nazari, shin abu ne mai kyau, wanda ya dace da Shari’a? Sai ya aikata shi. Idan kuma wanda ya saɓa ne, sai ya guje wa aikata shi.
Na biyu kuma shi ne Hisabi bayan mutum ya aikata aikin. Idan mai kyau ne sai ya gode wa Allah. Idan kuma zunubi ne sai mutum ya yi gaggawar tuba.
Malam ya gargaɗi mutane da a ji tsoron Allah. Ya nemi da mu riƙa ziyartar maƙabarta, inda za mu ɗauki izina daga matattu, waɗanda a cikinsu akwai sarakai da masu mulki da attajirai da talakawa. Hakan zai sa mutum ya ƙara imani da cewa zai mutu shi ma, kowane ne shi.
Malam ya ja hankalin mutane game da halin matsi da ake ciki, inda kayan masarufi suka yi tsada, talakawa na wahala da rashin abinci da rashin lafiya.
Ya yi kira ga ‘yan kasuwa da attajirai da masu mulki da su ji tsoron Allah, su sassauta al’amura domin taimakon mabuƙata daga cikin al’umma. Ya nemi ‘yan kasuwa da su daina ɓoye hatsi don ya yi tsada, su ci riba mai yawa.
Dangane da wannan yanayi na matsi da al’umma ke ciki, ya buƙaci ‘yan kasuwa su ji tsoron Allah, su daina tsauwala farashi.
Ya ba da wani misali da wasu ‘yan kasuwa a Malumfashi, inda ya ce ya samu rahoton sun ɓoye hatsi. Ya ce wasu attajirai sun nemi sayen buhu 60 don rabawa ga mabuƙata, amma aka rasa sai da aka je Funtuwa aka samu. Ya ce wannan abin kunya ne kuma abin Allah wadai.
Malam ya ƙarƙare da addu’ar Allah Ya kawo mana sauƙin al’amura, Ya yafe mana kurakurenmu.












