Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Kwalejin Dabarun Mulki ta Ƙasa (AANI), tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, MD Abubakar, CFR, ya buƙaci al’ummar Najeriya da su yi amfani da Ranar Dimokuraɗiyya ta bana wajen haɗa kai da juna wajen gina ƙasa, domin tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ba tare da nuna wariya ba.
Shugaban, a yayin da yake taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar wannan rana ta dimokuraɗiyya, a wata takardar manema labarai da Sakataren Watsa Labaran ƙungiyar, Birgediya-Janar (mai ritaya), Sani Usman Kuka-Sheƙa ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa:
“A yayin da muke murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya a yau 12 ga Yuni, 2023, lokaci ne da ya kamata mu waiwaya baya, a tarihin siyasar ƙasar nan, wanda ke ƙara nuna himma da jajircewar ‘yan Najeriya, na tabbatar da kafuwar kyakkyawan shugabancin dimokuraɗiyya mai ɗorewa.”
Ya jaddada cewa, tsarin dimokuraɗiyya ya ba ‘yan ƙasa damar bayyana ra’ayinsu, sannan ya ba su ‘yancin zaɓen shugabanninsu da kansu, domin ciyar da ƙasa gaba. “Tsari ne da yake ƙarfafa wa ‘yan ƙasa, su ba da tasu gudunmawa wajen gina ƙasa. Don haka a yayin da muka samu wannan sabuwar gwamnati, sai mu haɗa hannu a dama da mu wajen tabbatar da gudanuwar tsarin dimokuraɗiyya, musamman wajen tattaunawa mai ma’ana da yin aiki tare da juna wajen magance matsalolinmu da ƙalubalen da ke damun ƙasarmu,” in ji shi.
Da ya juya ga ‘yan ƙungiyar tasu ta AANI kuwa, Shugaba MD. Abubakar ya ja hankalinsu da cewa, a matsayinsu na shugabannin al’umma, ya kamata su riƙa nuna shugabanci na adalci bisa misali na ƙwarai. Kuma su riƙa ɗabbaka halayen ƙwarai na tafiya tare da al’umma cikin amana da gaskiya. “Muna ƙarfafa gwiwa ga duk wani tsari na ci gaban al’umma, wanda zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa,” in ji shi.
Da ya juya kan jami’an tsaro kuwa, Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban yaba masu ya yi, musamman saboda namijin ƙoƙarin da suke yi wajen kare al’ummar ƙasa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’umma. Don haka ya buƙaci ɗaukacin al’ummar ƙasa da su so juna, su haɗa kai domin gina ƙasa ba tare da nuna wariya da bambancin yare, ƙabila, yanki ko addini ba.
Ya ƙarƙare da addu’a ga Najeriya da al’ummarta baki ɗaya. “Ya Allah Ka sanya mana soyayyar juna, Ka ba mu haɗin kai da zaman lafiya. Ka yi mana jagora bisa hanyar ci
gaba, Ka haskaka mana al’amura yadda gabanmu za ta yi kyau fiye da baya. Allah sa wannan dimokuraɗiyya ta zame mana alheri da ƙarfafa gwiwar ‘yan ƙasa domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.”














Ma Sha Allah. Allah ta’ala ya Kara haskaka jaridar GIZAGO
Amin Amin Ya Allah. Muna godiya ainun.
Amin, Bahaɗejen.