Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Ni Na Fi Kowane Marubuci Samun Nasara A Harkar Rubutu – Barista
Muhammad Lawal Barista na ɗaya daga cikin manya kuma fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ya rubuta littattafai sama da 50. Taskar Gizago ta tattauna da shi, inda ya bayyana cewa shi ya fi kowane marubuci na zamaninsa samun nasarori a harkar rubutu.
TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa a wanann zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
Barista: Sunana Muhammad Lawal Isa, amma a harkar rubutu da Muhammad Lawal Barista aka san ni. An haife ni a garin Gama da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano. Na yi makarantar firamare Brigade Special Primary School, Kano. Daga nan na tafi makarantar sakandare ta Government Secondary Commercial School, Airport Road, Kano. Daga nan na samu tafiya Kano State Polytechnic (School of Management Studies), inda na samu National Diploma a Ilimin Ƙididdiga (Accounting). Sai kuma na tafi Federal College of Education na ɗora da Higher National Diploma a Ilimin Ƙididdiga da Binciken Kuɗi (Account and Audit).
Saboda sha’awa da na samu ta karanta harkokin Shari’a sai na tafi Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, inda na karanta kwas ɗin Diploma in Civil Law. Sai kuma na wuce Jami’ar Bayero da nufin in ɗora a karatuna na ‘Accounting’, amma Allah da ikonSa, sai na samu sauyin shawara. Maimakon Accounting sai na karanci Harshen Hausa, a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, kasancewa ta marubuci a harshen. Yanzu haka, ina daf da kammala Digirina na biyu (Masters) a harshen Hausa.
TG: Tun yaushe ka fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?
Barista: Na fara rubutu tun ina aji biyu a Sakandire, amma ban samu damar fitar da littafina na farko ba, sai a shekarar 1999.
Babban abin da ya ja hankalina na fara rubutu, bai wuce hangen wasu matsaloli ba, waɗanda nake ganin zan iya bayar da gudummuwa da baiwar da Allah Ya yi mini wajen warware su.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?
Barista: Zuwa yanzu ina da littattafai kusan guda 55 waɗanda na rubuta, amma guda 27 ne na buga zuwa yanzu.
A internet kuwa ban taɓa wallafa cikakken littafi ba, sai dai gajerun labarai. Amma akan samu wasu daga cikin masoya su ɗauki littafina su kwafe shi gaba ɗaya, su ɗora shi a internet ɗin.
TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?
Barista: Har zuwa yanzu dai ban ci karo da wata gagarumar matsala a harkar rubutu ba. Sai dai matsalar da marubuta suka fi kuka da ita a baya can, matsalar ‘yan kasuwa ce. A yanzu kuma matsalar rashin wadatattun makarantan da suke iya ɗaukar bugaggen littafi su karanta ake fama da ita, saboda kusan komai ya koma kan intanet.
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?
Barista: A gaskiya na samu nasarorin da ba zan iya ƙididdige su ba. Na sha fada, yanzu ma zan faɗa, a fahimtata babu wani marubuci na Hausa a ƙarnina da ya ci ribar rubutu sama da ni.
Na farko dai, na sauke farali saboda rubutu. Na ziyarci wasu manyan ƙasashe saboda rubutu. Na samu manyan kyaututtukan da za su ba mutum mamaki saboda rubutu. Na aura, na aurar, saboda rubutu. An haifi yara an sanya musu sunana saboda rubutu. An sanya wa wasu yaran (mata) sunan mahaifiyata saboda soyayya ta rubutu. An san ni, na san mutane da yawa saboda rubutu. An yi rubutu a matakin Digiri na ɗaya da na biyu (Masters) da ma na uku (Ph.D) a kan littattafaina. A yanzu haka ina hulɗa da wasu manyan mutane a Kano da Najeriya da ma duniya duk don saboda rubutu. Kuma kwanan nan ma zan tafi ƙasar Turkey don yin wani bincike kuma duk dalilin rubutu. Gaskiya maganar nasarori a rubutu sai dai na ce alhamdu lillah. Har yanzu ban ci karo da akasin nasarar da ya kai na ambace shi ba.
TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?
Barista: Kusan duk wanda Allah Ta’ala Ya ba baiwar rubutu (namiji ko mace) gwani ne a wajena, don na san ba daidai yake da wanda ba shi da baiwar ba. Don haka, ina iya cewa, dukkan marubuta gwanayena ne. A game da salo ko koyi kuma, ban ɗauki salon kowa ba, ni ma ina rubutu ne da irin salon da Allah Ya huwace mini. Sai dai wasu sukan ce, rubutuna yana ɗaukar salo da na marubuci wane ko wane.
TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?
Barista: BAƘIN LITTAFI, shi ne sunan littafin da nake rubutawa yanzu haka, kuma zai fito ne da shafuka 560, sannan zai fito a buge (hard copy), kuma zan wallafa shi a intanet in sha Allahu. Ba na so na ambaci haƙiƙanin lokacin da zai fito saboda ina so na inganta littafin sosai.
TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?
Barista: Ai tuntuni ma na rubuta finafinai da dama. Ni ne marubucin fim ɗin Taƙaddama, wanda aka yi shi tun a shekarar 2007. Ni na rubuta fim ɗin Ƙwarya Ta Bi Ƙwarya da Wasiyya da Manaƙisa da Madubi. Kuma yanzu haka ma, ina nan ina rubuta wani fim mai dogon zango mai suna Ruwan Dare.
TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?
Barista: Kullum burina dai a rubutu shi ne isar da saƙo, na hani ga mummuna da umarni da kyakkyawa. Ba ni da wani buri na sai na zama wane, ko shiga cikin sahun su wane.
TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?
Barista: Farko kira na ga marubuta ne, su riƙa rubutu da ilimi da bincike da ma nazari kafin su rubuta. Kuma idan za su rubuta su sani, akwai ranar da za a tutsiye su don amsa abin da suka rubuta. Su ji tsoron Allah a rubutunsu, su kauce wa duk wani abu da ya saɓa wa addinin Musulunci da shari’a. Ko ba don tambaya ba ma, wata rana za su haifi yaran da za a goranta musu a kan abin da suka rubuta na ba daidai ba, kasancewar duk abin da aka rubuta, yana tabbata, tsawon lokaci.
Su kuma makaranta, su kuma riƙa karatu da buɗaɗɗiyar zuciya don su fahimci saƙon da ake son isar musu.
Gwamnati kuwa zan so ta riƙa taimaka wa marubuta ko da kuwa da sanya gasa ne, daga lokaci zuwa lokaci. Hakan ma zai iya zama wata hanya ta tsaftace rubutun.
Daga ƙarshe, ni ma na gode ƙwarai da gaske. Allah Ta’ala Ya saka da mafificin alheri. Kuma zan yi amfani da wannan dama na yi addu’a ga Auwalu Garba Ɗanborno, Allah Ya ji ƙan shi, Ya sanya aljanna ce makoma.













