• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Ambaliya: Gwamnan Jigawa Ya Nemi Tallafin Bankin Duniya

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 8, 2023
in Labarai
0
An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Gwamnan Jihar Jigawa

18
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Ambaliya: Gwamnan Jigawa Ya Nemi Tallafin Bankin Duniya

Related posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya buƙaci tallafi daga Bankin Duniya domin magance matsalolin ambaliya da ke addabar jihar da kuma tallafi na musamman domin bunƙasa rayuwar matasa a jihar.

Kamar yadda wata takarda da ta fito daga Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan, Malam Hamisu Gumel ta bayyana, Gwamnan ya nemi tallafin ne a ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da ya kai ziyara ta musamman Ofishin Bankin Duniya da ke Abuja, inda Darakta mai kula da al’amaran bankin a Najeriya, Mista Shubham Chaudhury da ayarinsa suka amshe shi.

Kamar yadda Gumel ya bayyana, Gwamnan ya kai ziyarar ce musamman domin tattaunawa da Bankin na Duniya, ta yadda za a samu shawo kan manyan matsalolin da ke fuskantar al’ummar jihar.

A yayin ganawar, Mista Chaudhury ya yi wa Gwamna Namadi bayani dalla-dalla game da ayyukan bankin da hanyoyin da suke taimakawa, wajen bunƙasa rayuwar al’umma.

A nasa ɓangaren, Gwamnan na Jigawa ya zayyana wa hukumomin bankin irin matsalolin da ke addabar jiharsa ta Jigawa, wanda ya zama tilas su nemi tallafi daga waje. “Jihar Jigawa na fuskantar matsalolin da suka shafi ambaliyar ruwa, wanda a can baya ya lalata hanyoyi, gadoji. Haka kuma ambaliyar ta mamaye gonaki masu murabba’in sama da eka dubu 400. Ga shi a bana, kamar yadda Hukumar Agajin Gaugawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi hasashe, ambaliyar za ta ta’azzara. Bisa ga haka, ya zama wajibi mu nemi tallafi daga Bankin Duniya, domin kiyayewa,” in ji Gwamna Namadi.

Gwamnan ya buƙaci bankin na duniya ya taimaka wa jihar a fannonin noma, kiwon lafiya, bunƙasa tattalin arziki da kuma ɓangaren magance ambaliya da kwararowar hamada. Haka kuma ya nemi yadda za a tallafa wa manoma da famfunan ban ruwa masu aiki da hasken rana da hikimomin zamani na bunƙasa noman rani da sauransu.

Da yake maida jawabi, Mista Chaudhury ya ce za su yi nazari na tsanaki game da buƙatun Gwamnan, inda za su duba yadda bankin zai yi haɗin gwiwa da gwamnatin jihar, domin tallafawa yadda ya kamata, domin samun bunƙasa al’umma.

Previous Post

Batun Jami’a A Malumfashi: Ƙarin Bayani Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta

Next Post

Ni Na Fi Kowane Marubuci Samun Nasara A Harkar Rubutu – Barista

Related Posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Next Post
Ni Na Fi Kowane Marubuci Samun Nasara A Harkar Rubutu – Barista

Ni Na Fi Kowane Marubuci Samun Nasara A Harkar Rubutu - Barista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sojoji Sun Cafke Manyan Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

Sojoji Sun Cafke Manyan Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

July 19, 2023
TSOKACINMU NA YAU (13)

TSOKACINMU NA YAU (13)

March 13, 2025
RAMADAN KARIM: 25-1447

RAMADAN KARIM: 25-1447

March 14, 2026
Nigeria 2027: How Viable is Obi/Kwankwaso ADC Ticket?

Nigeria 2027: How Viable is Obi/Kwankwaso ADC Ticket?

March 25, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.