Shugaban Majalisar Dattijai ta 10, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana sunayen Sanatocin da za su shugabanci majalisar.
Waɗannan kuwa sun haɗa da shi kansa Sanata Godswill Akpabio, a matsayin Shugaba. Sai Sanata Barau Jibrin, a matsayin Mataimakin shugaban Majalisa. A yayin da shi kuma Sanata Opeyemin Bamidele, a matsayin Shugaban Masu Rinjaye.
Sauran shugabannin su ne Sanata David Umahi, a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye. Sai kuma Sanata Muhammad Ndume, a matsayin Babban Mai Tsawatarwa.













