Daga Abbas Ɗalibi
Maimakon Gwamnan Jihar Kano, Abba Gida Gida ya kwashi masu First Class ya ɗebe miliyoyin daloli ya biya masu karatu a jami’o’in ƙasashen waje, gara ya kwashi masu First Class ɗin ya ba su ayyukan yi a Jihar Kano.
Yayin da suka fara aiki, za su sami ƙwarewa da gogewar aiki. Kkuɗaɗen da za a biya su albashi za su amfane su, su kuma amfani al’ummar Jihar Kano. Aikinsu ma zai amfane su, ya amfani al’ummar Kano, sannan da kansu za su sami damar biya wa kansu karatu na gaba idan suna da buƙata.
Lokacin da Kwankwaso ya yi irin wanna, Dala tana daidai da Naira 250 ne kacal amma yanzu Dalar ta ninninkan farashin Naira, ta kai sama da ₦750.
A yanzu halin da ake ciki, ɓarna ce Gwamna ya kwashi kuɗin al’umma ya narka su a ƙasashen ƙetare. Kamata ya yi duk kuɗin da za a narka a narka su a Jihar Kano, domin al’ummar Kano su anfana.
Sannan ‘yan sakandaren da za a biya wa karatu a jami’o’in ƙasashen waje, to kamata ya yi a ɗauki nauyinsu zuwa jami’o’i masu zaman kansu na Jihar Kano, domin yanzu akwai su da yawa. Ko ba komai, gara a kashe kuɗin a jami’o’in cikin gida, domin suna da ma’aikata ‘yan Kano, tun daga masu koyarwa har zuwa masu shara da masu gadi, kuma suna biyan haraji a Kano.
Ya kamata gwamnatocinmu idanunsu su buɗe, domin da arziki a garin wasu gara a garinku.
~~~~~~~
Abbas, ɗan jarida ne kuma ɗan asalin Jihar Kano.
~~~~~~~













