IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Gwamna Radda
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya taya tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), murnar cika shekaru 85 da haihuwa, yana bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa kuma ɗan siyasa mai tarihi, wanda gudummawarsa ta bar tarihi mai ɗorewa a harkokin siyasa da gudanar da mulkin Najeriya.
Gwamna Radda, a cikin saƙon taya murnar da ya fitar a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026, ya yi tsokaci na musamman kan rawar da Janar Babangida ya taka wajen ƙirƙirar Jihar Katsina a ranar 23 ga Satumba, 1987, tare da Jihar Akwa Ibom.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙirƙirar Jihar Katsina wani muhimmin mataki ne a tarihin al’ummar jihar, domin ya ba su damar samun keɓaɓɓen mutunci a siyasance da kuma damar tsara harkokin ci gabansu bisa abubuwan da suka fi dacewa da buƙatunsu da burinsu.
A cewar Gwamna Radda, al’ummar Jihar Katsina za su ci gaba da tunawa da Janar Babangida saboda matakin da ya ɗauka na ƙirƙirar jihar. Ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin lamari da ya buɗe sabon babi na ci gaba da bunƙasa ga al’ummar jihar.
“Al’ummar Jihar Katsina za su kasance suna tunawa da Janar Ibrahim Badamasi Babangida saboda ya sama wa jiharmu matsayi na musamman, tare da samar wa al’ummarmu damar tsara tafarkin ci gabansu da kansu,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa matakin ƙirƙirar Jihar Katsina “yana daga cikin muhimman abubuwan da suka bayyana a tarihinmu,” yana mai jaddada muhimmancin da gwamnatin tsohon shugaban mulkin sojan ke da shi a tarihin jihar.

Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa Janar Babangida ya ci gaba da kasancewa fitaccen ɗan kishin ƙasa, wanda hidimarsa da jagorancinsa suke taka muhimmiyar rawa a tarihin siyasar Najeriya. Ya yaba da gudummawar da tsohon Shugaban Mulkin Sojan ya bayar ga ƙasa, tare da shiga cikin iyalansa, abokansa da miliyoyin ’yan Najeriya wajen taya shi murnar wannan babban matsayi na shekaru.
“Yayin da kake bikin cika shekara 85 da haihuwa, muna taya kai da iyalinka da abokanka da miliyoyin ’yan Najeriya wajen gode wa Allah Maɗaukaki bisa ba ka rayuwar hidima ga ƙasarmu,” in ji Gwamna Radda.
Gwamnan ya kuma roƙi Allah ya ci gaba da ba Janar Babangida lafiya, kwanciyar hankali da tsawon rai, tare da neman Allah ya ƙara masa shekaru masu albarka, cike da rahama da ni’imominSa.
A madadin Gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar baki ɗaya, Gwamna Radda ya sake taya tsohon Shugaban Mulkin Sojan murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yi masa fatan samun lafiya da walwala a sauran rayuwarsa.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya jagoranci Najeriya a matsayin Shugaban Mulkin Soja daga shekarar 1985 zuwa 1993. Gwamnatinsa ta yi fice wajen wasu muhimman sauye-sauyen siyasa da tsarin gudanar da mulki a ƙasar, ciki har da ƙirƙirar Jihar Katsina a shekarar 1987.
Ibrahim Kaula Mohammed, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina ne ya sanya hannu kan saƙon taya murnar, wanda aka fitar a ranar 17 ga Agusta, 2026.
__________













