Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) kuma tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, ya sake bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro take ƙara tsananta a ƙasar nan, inda ya yi gargaɗin cewa Najeriya na iya shiga wani mataki mafi haɗari na ta’addanci da fashi da makami, idan gwamnatocin tarayya da na jihohi ba su ɗauki matakai na gaugawa da tsauri ba a kan lamarin.
A cikin wata sanarwa mai taken “Shawara Ta Gaskiya Kuma Ta Kishin Ƙasa Kan Matsalar Tsaro Da Ke Ƙara Kamari A Najeriya,” Buratai ya bayyana cewa abubuwan da suka faru kwanan nan, musamman rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), aka azabtar da shi sannan aka kashe shi, sun nuna yadda tsarin tsaron ƙasar nan yake ƙara raunana.
A cewarsa, wannan lamari wata babbar alama ce ta canjin yanayin matsalar tsaro, domin hare-haren da a baya suka fi shafar fararen hula, yanzu sun fara kai wa ga manyan jami’an tsaro da shugabannin gwamnati.
Tsohon shugaban sojojin ya tunatar da cewa tun a shekarar 2021 ya yi hasashen cewa ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga za su iya ci gaba har tsawon shekaru 20, idan ba a ɗauki matakai masu tsauri ba. Ya ce abubuwan da ke faruwa a yau suna tabbatar da wannan hasashe. Yana mai jaddada cewa ƙarfin da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suka samu yanzu, yana barazana ga zaman lafiyar ƙasa.
Janar Buratai, wanda ke riƙe da sarautun gargajiya na Betaran Biu kuma Garkuwan Keffi, ya yi gargadin cewa: “Idan aka ci gaba da sakaci, manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da ministoci, sanatoci da gwamnoni suna iya zama sabbin waɗanda za a riƙa kai wa hare-hare.”

Janar ɗin ya bayyana cewa, dabarun da ake amfani da su a halin yanzu wajen magance matsalar tsaro sun gama yayi kuma suna buƙatar a sake duba su gaba ɗaya. Ya lura cewa yawancin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya, yanzu suna da ingantattun hanyoyin tattara bayanan sirri, makamai masu ƙarfi da kuma ƙarfin gwiwar gudanar da hare-hare irin na rundunonin yaƙi. Saboda haka ya buƙaci a kawo ƙarshen biyan kuɗin fansa da tattaunawa da masu aikata laifuka, tare da ƙaddamar da wani gagarumin farmakin haɗin gwiwa na soja da hukumomin leƙen asiri; domin rusa sansanonin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a sassa daban-daban na Najeriya.
Da yake tuna nasarorin da aka samu a ayyukan tsaro tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019 da kuma tsarin haɗin gwiwar da aka yi amfani da shi wajen yaƙi da annobar COVID-19, Buratai ya ba da shawarar kafa wani tsari na musamman da zai haɗa dukkan hukumomin tsaro, ƙarƙashin jagoranci guda.
Ya ba da shawarar a kafa Hukumar Ba da Agajin Gaugawa Ta Ƙasa Kan Tsaro (National Emergency Command), wadda za ta jagoranci ayyukan tsaro a jihohin da ke fuskantar barazana. “Hukumar za ta riƙa kai rahoto kai tsaye ga Shugaban Ƙasa, tare da samun wa’adin lokaci da cikakken iko na murƙushe sansanonin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga,” in ji shi.
Betaran na Biu, ya kuma jaddada muhimmancin a daƙile hanyoyin da ‘yan ta’adda ke samun kuɗi, tare da toshe hanyoyin da masu tallafa wa ayyukan ta’addanci suke bi wajen bunƙasa matsalar.
Ya ce “yan bindiga ba sa dogara da bindigogi kaɗai, domin suna dogaro ne da masu ɗaukar nauyinsu da masu safarar kuɗaɗe da masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da masu shiga tsakani wajen biyan kuɗin fansa da kuma masu ba su bayanai daga cikin al’umma.”
Saboda haka ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganowa, kamawa da gurfanar da duk wanda ke taimaka wa ‘yan ta’adda. Yana mai cewa ya zama dole a tanadar da tsananin hukunci ga duk wanda aka samu da hannu wajen tallafa wa ta’addanci.
Dangane da rawar da gwamnatocin jihohi ya kamata su taka, Garkuwan Keffi ya ce lokaci ya yi da gwamnoni za su ɗauki cikakken nauyin tsaro a yankunansu. Ya yi kira da a ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri daga al’umma, a haɗa ƙungiyoyin sintiri na sa-kai da aka tantance yadda ya kamata cikin tsarin tsaro, sannan a ƙarfafa shirye-shiryen ‘yan sandan jihohi, domin su taimaka wa hukumomin tsaro na tarayya.
Kodayake Buratai ya bayyana fatan cewa shugabannin siyasa ba za su zama abin kai wa hari kai tsaye daga ‘yan ta’adda ba, ya buƙaci a ƙara tsaurara matakan tsaro ga manyan jami’an gwamnati. “A ƙara ba da horo ga jami’ai, kan yadda za su riƙa kare kansu daga kwanton ɓauna, yadda za a inganta musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro da kuma ɗaukar matakan kariya kafin aukuwar hare-hare,” in ji shi.
Ya jaddada cewa mafita ta dindindin ba wai kare mutane kaɗai ba ce, illa a rusa gaba ɗaya tsarin da ke bai wa ‘yan ta’adda damar ci gaba da munanan ayyukansu.
Da yake bayyana kansa a matsayin ɗan kishin ƙasa, wanda ba shi da wata manufar siyasa, Buratai ya ce abin da ya sa ya yi wannan kira shi ne, saboda nuna damuwarsa kan makomar Najeriya. Ya yi gargaɗin cewa idan ba a sauya dabarun yaƙi da matsalar tsaro cikin gaggawa ba, abubuwan da za su faru nan gaba, suna iya zama mafi muni fiye da waɗanda ake gani a yau.
Ya ce: “Sace ministoci ko gwamnoni ba abu ne da dole sai ya faru ba amma zai iya faruwa, idan muka ci gaba da tafiyar da al’amura sasakai, kamar yadda aka saba.”
Daga ƙarshe, tsohon Babban Hafsan Sojan na Najeriya ya yi kira ga shugabannin siyasa, hukumomin tsaro da kuma ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su ɗauki mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar a matsayin babban gargaɗi, cewa a zage damtse a yi aiki. Ya jaddada cewa ƙasar nan ba za ta iya ci gaba da rasa rayuka ta hanyar da za a iya kauce wa ba a yaƙinta da matsalar tsaro.
Janar Tukur Buratai ya kasance Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2021 kuma har yanzu yana daga cikin fitattun masu bayyana ra’ayoyi kan harkokin tsaro da tsare-tsaren kariyar ƙasa.
_________












