• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 19, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

WATAN SALLAH

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 18, 2026
in Addini
0
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Yau 1 ga Dhul-Hijjah, 1447 (Nijeriya)

3
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Yau 1 ga Dhul-Hijjah, 1447 (Nijeriya)

__________

Related posts

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026

A yau mun shiga kwanaki masu albarka na watan Dhul-Hijjah 1447 (Hijiriyya), kwanaki goma waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki ya fifita a kan sauran kwanakin duniya saboda girman ibada da lada da suke tattare da su.

Wannan wata dama ce ga kowane Musulmi, domin ya kusanci Ubangijinsa ta hanyar ibada, tuba, kyautatawa da yawaita ayyukan alheri.

Allah ya rantse da waɗannan kwanaki a cikin Alƙur’ani mai girma. Wannan yake nuna girman matsayinsu. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: “Ina rantsuwa da alfijir da kuma kwanaki goma.” (Suratul Fajr-89:1-2). Malamai da dama sun bayyana cewa waɗannan kwanaki goma su ne kwanakin farko na Dhul Hijjah.

Manzon Allah (saw) ya bayyana falalar waɗannan kwanaki, a cikin wani hadisi mashahuri da Imam Bukhari ya ruwaito, inda ya ce: “Babu wasu kwanaki da aikin ƙwarai ya fi soyuwa ga Allah a cikinsu sama da waɗannan kwanaki goma.” Sahabbai suka tambaya: “Ko da jihadi a tafarkin Allah?” Sai ya ce: “Ko da jihadi, sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.”

Wannan hadisi yana nuna cewa ibada a waɗannan kwanaki tana da matsayi mai girma ƙwarai a wajen Allah.

Daga cikin abubuwan da ake so Musulmi su yawaita yi, akwai sallar nafila, azumi, karatun Alƙur’ani, zikiri, istigfari da sada zumunta. Haka kuma, musamman akwai azumin ranar Arafah ga wanda ba ya aikin Hajji, domin Manzon Allah (saw) ya ce yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da kuma mai zuwa.

Haka kuma ana son a yawaita faɗin: Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd. Wannan zikiri yana daga cikin manyan ayyukan da ake raya waɗannan kwanaki da su.

Waɗannan kwanaki kuma lokaci ne na tuba ta gaskiya. Mutum ya duba rayuwarsa, ya nemi gafarar Allah daga kurakuransa, ya nisanci zalunci, hassada, gulma da duk wani saɓon da zai iya hana rahamar Allah sauka a gare shi. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: “Ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai, domin ku sami rabauta.”  (Suratun Nur – 24:31). Tuba a irin waɗannan kwanaki tana da girman lada da karɓuwa idan aka yi ta da ikhlasi.

Haka kuma ana ƙarfafa kyautatawa ga iyaye, taimakon marasa ƙarfi, ciyar da mabuƙata da sadaka. Musulunci addini ne na rahama da tausayi kuma Allah yana son bayinsa masu taimakon juna. Duk wanda ya taimaki wani cikin waɗannan kwanaki, yana iya samun lada mai yawa fiye da yadda yake zato. Bai kamata Musulmi ya taƙaita ibadarsa ga kansa kawai ba. Ya kamata ya zama mai amfani ga al’umma.

Ga masu niyyar yin layya, Manzon Allah (saw) ya yi umarni cewa, idan an ga jinjirin Dhul-Hijjah, kada mutum ya rage gashi ko farce har sai ya yi layyarsa. Wannan yana daga cikin sunnonin da suke nuna girmama wannan ibada mai albarka. Layya tana tunatar da Musulmi sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS) da biyayyarsa ga umarnin Allah. Saboda haka, ya dace Musulmi ya yi layya cikin tsoron Allah da kyakkyawar niyya.

Babu shakka, kwanaki goma na Dhul-Hijjah wata babbar dama ce da ba kowa yake riskarta ba. Masu hikima su ne waɗanda suke anfani da ita wajen tara ayyukan alheri kafin rayuwa ta ƙare. Mu yawaita addu’a, domin Allah ya gafarta mana zunubanmu, ya gyara al’amuranmu, ya kawo zaman lafiya da albarka a ƙasarmu da al’ummarmu.

Allah ya sa mu kasance cikin bayinsa nagari, masu anfani da waɗannan kwanaki masu albarka. Amin-Summa-Amin.

__________

Previous Post

ALHAMDU LILLAH

Next Post

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Related Posts

Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)
Addini

MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

April 13, 2026
Next Post
Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

Ɗan Iyan Galadima Ya Zama Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewa

June 19, 2025
PROMOTION GALORE: PSC Promotes 5718 Senior Police Officers

PROMOTION GALORE: PSC Promotes 5718 Senior Police Officers

October 12, 2023
Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

June 29, 2023
GWAMNA MALAM DIKKO YA YI RASHIN MAHAIFIYA

GWAMNA MALAM DIKKO YA YI RASHIN MAHAIFIYA

March 23, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.