ALHAMDU LILLAH!

__________
A gare ka ya Allah,
Ƙara godiya nake,
Alhamdu lillah.
A gare ka ya Rahman,
Ƙara shukura nake,
Shukuru lillah.
A gare ka ya Rahim,
Ƙara roƙo nake,
Lafiya ƙaro Allah.
A gare ka Ya Raziƙu,
Ƙara buƙata nake,
Arziƙi ƙaro Jallah.
A gare ka ya Maliku,
Ƙara fata nake,
Walwala ƙaro Allah.
___________
© Bashir Yahuza Malumfashi,
Juma’a, 27-11-1447
15-05-2026.













