Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
A gobe Litinin, Shugaban kamfanin gine-gine na MUNTASRAB Global Concept, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi zai ƙaddamar da manyan ayyukan raya al’umma, na miliyoyin kuɗi a cikin garin Malumfashi da kewaye.
A yayin ƙaddamar da manyan ayyukan, waɗanda Injiniya Muntari ya gina da kuɗinsa a matsayin sadaƙatul jariya, mai girma Gwamna Jihar Katsina Malam Dr. Dikko Umaru Radda ne zai shugabanci bikin.
Manyan gine-ginen guda biyar sun haɗa sabon asibiti a garin Ɗanjanku da ɗakin tiyata na zamani a Asibitin Tsamiya na garin Malumfashi da sabuwar hanya, tare da magudanun ruwa a Unguwar Bayan Sambo Primary School.
Sauran ayyukan sun haɗa da sababbin ajujuwa guda uku a Makarantar Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Malumfashi (School of Midwifery) da kuma sabuwar motar jigilar ɗalibai da ya saya wa Makarantar Sakandaren Mata ta GGSSS Malumfashi.
Da yake nuna godiya da jin daɗin wannan babban aiki na Injiniya Muntari, ɗaya daga cikin aminansa, Malam Isma’il Sanda, addu’a ya yi masa, yana mai cewa:
“Injiniya Muntari Sagir Malumfashi, muna roƙon Allah ya kai lada mizani. Allah ya ƙara ɗaukaka mana kai. Ya ƙara ayyuka a Kamfanin MUNTASRAB Global Concept, amin.”
______________













