Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa
Daga Mohammed Umar Midala

__________
Barka da Ranar Harshen Uwa.
Gudunmawar da Dokta Bukar Usman ya bayar ta zama ginshiƙi a fafutukar da Najeriya take yi wajen yaƙi da ɓacewar harsunan gida, inda ya jagoranci wani yunƙuri na ƙasa baki ɗaya wajen tattarawa da farfaɗo da al’adu da harsunan gida da suke fuskantar barazanar shuɗewa.
Tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, ya jagoranci bincike na ƙasa baki ɗaya, inda ya tattara tatsuniyoyi da almara sama da 4,000 daga dukkan shiyyoyin Najeriya. Ya yi haka ne ta hanyar tattaunawa da dattawa, aka naɗi muryoyinsu da na’ura, inda suka bayyana tatsuniyoyin da ke akwai na asali a shiyyoyinsu.

Wannan aiki muhimmi ne, domin kuwa ya taskance al’adun gargajiya daban-daban na ƙabilun Najeriya cikin harsunansu na asali, kafin su ɓace.
Daga baya an fassara waɗannan tatsuniyoyi da almara da harsunan Hausa, Igbo, Yoruba da Turanci kuma aka wallafa su a manyan littattafai. Haka ke nuna cewa Dokta Usman ya samar da babban rumbu na “Taskar Tatsuniyoyin Najeriya” wanda a yau yake zama ma’adanar ilimi mai gudana ga masana, makarantu da kafafen yaɗa labarai.
Wannan babban aiki da Dokta Usman ya samar, bai tsaya kan adana kalmomi kaɗai ba; ya ƙarfafa muhimmanci da bambancin al’adu ta hanyar nuna yadda harshe, tatsuniya da rayuwar yau da kullum suke haɗuwa wuri guda. A matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Nazari da Bunkasa Al’adu ta Najeriya (Nigerian Folklore Society), ya mayar da waɗannan tarin littattafai, shirye-shiryen rediyo da kayan koyarwa a azuzuwa – yana bai wa matasan Najeriya damar samun tatsuniyoyi da almarorin da a da tsofaffi ke bayyana wa yara, a yayin hirar dare (cikin farin wata).
Wannan muhimmin aiki nasa, ya yi daidai da dabarun Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) na raya harsunan da suke fuskantar barazana. Aikin nasa, wanda ya haɗa da tattarawa, farfaɗowa da koyar da harshen uwa a makarantu; ya zama misali na ɗabbaƙa Shirin Raya Harsunan Gida na Asali na Majalisar Ɗinkin Duniya na Shekaru Goma (2022–2032).
Baya ga Najeriya, wallafe-wallafen Dokta Usman sun isa ƙasashen Afrika maƙwabta da al’ummomin da ke zaune ƙasashen duniya masu nisa. Lamarin da ya haifar da irin wannan ƙoƙari na tattarawa a yankunan Hausawa na Nijar da Chadi da sauransu. Masana daga ƙasar Sin, alal misali, sun yi ishara da aikinsa a matsayin abin koyi wajen kare gadon al’adun baƙar fata na Afirka a fagen ilimi na ƙasa da ƙasa.
Ta hanyar sarrafa tatsuniyoyi da almara daga waɗanda ake bayyanawa a zaman hira da dare, waɗanda ake ganin kamar sun ɓace, zuwa rubuce-rubuce a littattafai da intanet, Dokta Usman ya taimaka wajen ci gaba da bunƙasa tarin harsunan Najeriya, tare da gabatar da wata hanya mai sauƙin koyi ga sauran ƙasashen da ke fuskantar barazanar ɓacewar harsunansu na gida.
BARKA DA RANAR HARSHEN UWA
__________
Mohammed Umar Midala shi ne Mataimakin Sakataren Ilimi na Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Biu, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya.













